HANYOYIN KARIYA DAGA CIWON SANKARAU

HANYOYIN KARIYA DAGA CIWON SANKARAU

A watan nan da ya wuce an bada labarin bullar ciwon Sankarau a makociyarmu kasar Ghana inda aka tabbatar akalla mutane 140 sun kamu da wannan ciwo. Kwatsam sai kuma aka ji hukumomi ma a Najeriya na bada bayanin bullar wannan ciwo.

A irin wannan yanayi mai shigowa na zafi wanda kuma ya zo lokacin da aka samu ‘yan gudun hijira na fadace-fadace, sankarau kan yi barna idan ba a dauki matakan kariya ba. Don haka yana da kyau mu dan kara yin bita ga daidaikunmu akan hanyoyin da zamu bi wajen kare kai daga wannan ciwo.

Ciwon sankarau wani nau’in ciwo ne da kwayoyin cuta ke mamaye mayafin da ke lullube kwakwalwa da lakar wuya da gadon baya watomeninges a turance. Akwai nau’o’in ciwon sankarau daban-daban wanda kwayoyin cuta iri-iri ke kawowa. Kwayoyin cutar bacteria ne da ake kira Neisseria meningitidis ke kawo nau’in sankarau din da muka fi sani.

Su wadannan kwayoyin cuta suna nan a cikin iskar da muke shaka mai zafi. Hasali ma kashi daya cikin biyar a cikinmu masu lafiya na dauke da wadannan kwayoyin a hancinmu da makogwaronmu bamu sani ba. Ta haka ake yadasu in anyi kaki an tofar ko kuma ta iska a wuri mai cinkoso. Kwayoyin cutar mutuwa suke da sun ji sanyi. Don haka da wuya ayi sankarau lokacin sanyi.

Idan aka shakesu ta hanci kwayoyin na samun shiga jiki har jini ya kwashesu ya kai mayafin kwakwalwa. Nan da nan alamomin cutar zasu bayyana.


Alamomin Ciwon

Ciwon sankarau yafi kama yara ‘yan shekara 5-10, amma a lokaci na annoba zai iya kama kowa. Alamomin ciwon sankarau suna da yawa. Da farko dai akan ji

 1. Ciwon kai mai tsanani
 2. Zazzabi, sai
 3. Sankarewar wuya

Da zarar an ji wadannan alamomi na farko sai ayi maza a garzaya asibiti mafi kusa. Idan an dade ba je asibiti ba, za a ga mutum ya fara

 1. Amai
 2. Rashin son ganin rana ko haske
 3. Wasu kuma sukan suma
 4. Daukewar numfashi akai-akai wanda yakan sa a rasa mutum

Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo?

1.      A irin wannan lokaci, ayi nesa da jama’a musamman wajen taron suna ko biki ko daurin aure ko kallon kwallo, ko kuma a yi taron a waje

2.      A rika kwanan waje a gidan yawa ko wurare irin su makarantun kwana, ko wuraren samun mafaka na ‘yan gudun hijira irinsu bariki, da ma sauran wurin kwanciya na mutane da yawa kamar gidajen kaso.

3.      A tabbatar dakin barci na da tagogi bude a kalla biyu masu kallon juna. Idan taga daya ce abar kofa bude musamman idan mutane fiye da biyu ne a dakin

4.      A je cibiyoyin alluran riga kafi domin a karbi allurar riga kafin ciwon sankarau

5.      A face majina inda ya dace ba a cikin mutane ba

6.      Idan wani na kusa a gida ko wurin aiki ya kamu da ciwon to duk mutanen wurin ko da basu yi ciwon ba, su je su karbi magani a asibiti.

7.      A yi saurin kai wanda ya kamu da wannan ciwon asibiti don gudun yada cutar ko ya galabaita.

8.      Cin abinci mai gina jiki da shan kayan itatuwa na marmari masu tsabta musamman ga yara don kara karfin garkuwar jiki masu iya kashe kwayoyin cutar tun kafin su isa kwakwalwa.

AMSOSHIN TAMBAYOYI


Ina fama da fitsarin jini, na sha magunguna amma Allah baisa ya tafi ba

-A. S. Mukhtar.

Idan da kaje asibiti da tuni an gano abin da ya kawo hakan watakil kuma da tuni an fara magani. Bari in kara nanata maka abubuwan da kan kawo fitsarin jini, wadanda duk sai an dan yi binciken jini da fitsarin kafin a ce daya daga cikinsu ne;

1.     1. Wankan  rafi na kuruciya wanda kan jawo ciwon tsargiya, ciwonda wasu tsutsotsi kan rika kartar fatar mararka har tayi jini ka rika gani a fitsari

2.      2. Wanda idan aka sha maganin praziquantel bai tafi ba, to  yakan iya zama kari ko tsuro a cikin mafitsarar wanda kan sa ka rika ganin jini

3.      3. Idan kuma ka taba yin ciwon sanyi, wasu kwayoyin cutar kan makale a bangon mararka suna karta har wurin yai jini ka rika ganinsa a fitsari

4.      4. Sai kuma ciwukan koda ko shan magunguna barkatai masu sawa koda illa, wanda kansa koda ta rika jini yana kwaranyowa a fitsari

5.      5. Kumburi ko ciwon daji na wata ‘yar halitta a karkashin marar maza da ake kira prostate gland musamman idan ka ba shekaru hamsin baya ko kuma fitar fitsarin sai an yunkura sosai.

Da dai ciwuka iri-iri da sai anyi bincike marasa tsada kafin a dau mataki walau na magani ko na tiyata.


Ni kuma na taba yin ciwon sanyi ne na syphilis an ba ni magani a asibiti na sha na warke amma har yanzu akwai wani tabon ciwon kan kaciyata duk da dai ba ya ciwo. Ina son Karin bayani.

-Y.M. Dambatta da D.L.M

To wannan tabo in dai likitanka ya tabbatar kana da syphilis shi a likitance muke kira gumma kuma alama ce ta cewa ciwon ya shiga mataki na uku wato da alama bai tafi ba, domin mai wannan ciwon ana so bayan anyi masa magani da allurai, ya koma bayan wata shida da bayan shekara daya da bayan shekara biyu a sake wannan gwajin na farko da ake kira VDRL a tabbatar kwayoyin sun mutu.  In ba su mutu ba sai an sake allurai. Sannan kar ka manta idan kana da iyali ka tafi da matarka itama ayi mata gwajin VDRL.

5 thoughts on “HANYOYIN KARIYA DAGA CIWON SANKARAU

  • Wannan wani nau’in ciwon ciki ne mai wuyar sha’ani. Yawanci wannan ciwo ba wani abu za a iya nunawa guda daya a ce ga abinda ya samu ‘ya’yan hanjin mutum ba. Abindaa ake magani shine alamun da mutum ya zo da su, don rage kaifin ciwon. Wadannan alamu sun hada da yawan gudawa (ba tare da an ga wasu kwayoyin cuta a bayan gida ba), wani lokaci da jini a bayan gidan, sai yawan ciwon ciki, ko yawan cushewar ciki, wanda kan yi sauki idan mutum yayi bayan gida. Wani lokaci kuma mutum kan yi fama da duka wadannan. idan mutum ya ga yana da wata matsala irin wannan ya kamata ya ga likita.

   Like

 1. Ina ganin wani abu kamar jini bayan nagama fitsari kuma idan na tashi da safe inxan fitsari sai inga banga komai ba kuma in na sake jin fitsari sai inga wani abu karshen fitsarina. Kuma nayi kwana 2 banga komai ba kuma yau abin ya dawo don Allah minene yake son kamani kuma miye magani da xan kubuta dashi. Inajiran amsa ta.!

  Like

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s