TAMBAYOYI

Mene ne muhimmancin motsa jiki? Kuma wane lokaci ya dace ayi shi?

-N.I, Ringim.

Ba shakka motsa jiki akai-akai na daya daga cikin hanyoyin samun koshin lafiya. Bincike dabam-dabam ya nuna cewa motsa jiki kan hana cututtuka irin na zuciya da na mutuwar barin jiki aukuwa, ta hanyar kona man cholesterol, da rage hawan jini, da rage siga a jiki ga masu ciwon siga da ma wadanda basu da ciwon. Wato dai a hannu daya motsa jiki riga-kafi ne babba daga ciwon siga, ciwon zuciya, ciwon hawan jini, ciwon mutuwar barin jiki, wasu ciwukan na daji wato kansa, ciwon baya, ciwon jiki, ciwon damuwa na depression, ko na kasala da ma wasu da dama. A daya hannun kuma motsa jiki kan yi maganin duk wadannan ciwuka idan basu yi nisa sosai ba.

Binciken suka kuma ci gaba da nuna cewa mai motsa jiki akai-akai bayan annashuwa da zai rika ji a ransa, da kuma jin karfin jiki ta hanyar kara kwarin kasha, ana sa ran kuma zai samu karin shekaru a duniya.

A mafi yawan lokuta mutane sun fi jin dadin motsa jiki da safe, amma masana sun tabbatar da cewa ko da wane lokaci ma ana iya yi don za a iya samun duk fa’idojin da ake samu da safen. Ba wai kawai ka zage da tikar gudu a fili shine kawai motsa jiki ba, a’a idan ka yi tafiyar minti 45 a kowacce rana ko da mintina 15 sau uku (wato ya dai tashi minti 45) indai za ka yi a kullum, to kana daya daga cikin mutane masu motsa jiki.


An gwada siga na a asibiti ya nuna 8.8 aka ce ina da ciwon siga aka bani magunguna da wasu ka’idojin cin abinci. Da na gama na ‘yan kwanaki sai na koma aka gwada aka ga ya dawo 5.5. A wancan lokaci bana cin wasu kalar abinci amma yanzu ina cin komi kuma sigan baya wuce 5.0 don ya nuna hakan fiyen da sau goma. To shin ya abin yake ne don ance ba a warkewa.

-Musa.

Cewa ko kana da ciwon siga ko baka dashi ya danganta da lokacin da aka dau jinin, wato da safe kafin kaci abinci ne ko kuwa? Kuma idan da safe ne sau daya kawai aka gwada ko sau da dama? Wato wani gwaji mai suna OGTT da za a dau siganka a gwada duk bayan awa biyu biyu shine zai tabbatar kana da ciwon siga ko a’a, kuma idan ba a dau fitsarinka an gwada ko yana dauke da siga ba, ba za a iya tabbatarwa ko kawai siganka ne yayi sama a wannan lokaci ba.

Amma da yake ciwon siga iri-iri ne, watakil naka irin wanda wani abu ke jawo shi ne kamar kiba da wasu cutukan (wanda ake kira secondary diabetes) wanda shi yakan warke gaba daya. Amma idan har kana da gadon ciwon siga wato idan akwai mai irinsa a gidanku tunda kace ku uku ne kuke da irin ciwon, to shi baya warkewa sai dai ya lafa. Kuma idan ya lafa ka kan iya rayuwarka kamar maras ciwon in dai ka bi ka’idojin da likitan ya baka.

Shawara dai itace idan akwai mai ciwon a dangi, ka gayawa likitanka ayi gwajin OGTT da na fitsari a tabbatar.


Nine mai syphilis kuma na je an min gwajin VDRL an ce non-reactive. Shin kana ga har yanzu da sauran wannan ciwo?

-Y.M, Dambatta.

A’a tunda gwaji ya tabbatar babu ciwon kuma ba ka da wasu alamu sai na wannan tabo to ciwo ya tafi kenan kuma shima tabon a hankali da sannu zai baje.


Duk lokacin zafi tafin hannuna da na kafata sai sun bambare (sai sun yi saba). Me yake kawo hakan?

-Bakari, Maiduguri


To saba iri-iri ce itama akwai ta gado akwai kuma ta canjin yanayi. Yawanci duka gado ake don haka da wuya kenan ciwon ya tafi baki daya, sai dai a rika shafa mai mai karawa fata taushi da lafiya wato irin man na mai dauke da sinadaran vitamin na rukunin A da E.


Mene ne amfanin tsarki da toilet paper kafin ayi da ruwa?

-Shafi’u.


To shidai bayan gida kashi 90 cikin dari duk kwayoyin cuta ne wadanda nan da nan za a iya sawa a abinci ba tare da an sani ba. Don haka idan aka yi amfani da wani makari kamar toilet paper aka share sarai za a iya kiyaye kwasar kwayoyin cuta da dama a hannun, musamman a cikin farce ko kumba. Daga nan a sa ruwa da sabulu a wanke ragowar. Shima hannun shi yasa ake sa sabulu ko toka a wankesu sarai.

Kaga da zamu rike wannan dabara kadai musamman ga masu abincin sayarwa da ‘yan aiki masu abinci a gidajenmu,  da za mu rage ciwon tafot kwarai da gaske tunda da hannun da ya taba bayan gida wanda ke dauke da kwayar cutar ake yada shi wannan ciwo

20 thoughts on “TAMBAYOYI

 1. shin ana warkewa daga ciwon jijjiga wanda akasamu ta hanyar “typhoid”sabo da hawan da jini yayi zuwa kwakwalwa.by maraqisiyya abdulkareem

  Like

 2. Aslm, mallam wane agani zan dunga amfani dashi ne,don idan ina zuwa gudu sai inji jikina namin ciwo kuma tana haddasa mun yawan bacci. Nagode

  Like

  • Qwarai kuwa zogin ciki da ciwon olsa ke kawowa yana hana barci domin a lokuta da dama ya ma fi tashi da dare. Amma da ka je asibiti an duba an tabbatar olsar ce aka ba ka magunguna ka fara sha, a daren za ka fara jin canji.

   Like

  • : Qwarai kuwa akwai olsar iri biyu, akwai ta bangon ciki akwai ta farkon hanji. Ta farkon hanjin masana sun ce it ace ta fi tashi da dare ta hana barci, har sai an ci ko an xan sha wani abu kafin ta yi sauqi. Amma dai kullum muna nanatawa akwai maganin warkewa. Kawai dai sai aljihu ya motsa sosai ne shi ne matsala domin magungunan masu qarfi ne da tsada, ga kuxin gwaje-gwaje. A mafi yawan lokuta magungunan lafar da ciwon kawai akan bayar, amma idan maras lafiya ya nuna wa likita buqatar yana so a yi komai da komai har ta warke za a masa.

   Like

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s