RAWAR DA ZAMU IYA TAKAWA A FANNIN KIWON LAFIYA

Ita dai harkar lafiya kamar harkar ilmi tana da matakai uku. Mataki na farko da na biyu da kuma na uku (wato Primary, Secondary, Tertiary health). Matakin sama wato na ukun za a iya cewa gwamnatin tarayya ke da alhakin samarwa kamar yadda muke gani a a asibitocin koyarwa da kuma na Federal Medical Center. Sai kuma na tsakiya wanda alhakin a kan jihohi ne na samar da wurare masu kama da General Hospital ko Specialist Hospital. Sai kuma mataki na farko primary healthcare wanda kacokan ya rataya a wuyan al’umma da masu unguwanni da  karamar hukuma.

Mene ne matakin kiwon lafiya na farko? Matakin lafiya na farko kamar yadda sunan ya nuna shine ginshikin kiwon lafiya a cikin al’umma. Idan babu shi babu kiwon lafiya. Rashin wannan shine babban abinda ke ciwa harkar samar da lafiyarmu tuwo a kwarya. Kuma shine ummul-aba’isin cinkoso da muke samu a manyan asibitocinmu.Wannan mataki na primary health bai tsaya ga gina asibitocin kawai ba, a’a har da abubuwa irinsu tsabtar muhalli (ta gida ko ta kasuwa) don kiyaye yaduwar cututtuka, a daidaikunmu ko ta aiyukan gaiya wadanda aka sanmu da su a zamanin da, wanda a lokacin idan ba’a kiyaye dokokin tsabtar gari ba hukumomi kansa duba gari su kulle kasuwa ko suci tarar mai gidan da yaki tsabta.

Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya take fada, matakin lafiya na farko dole ya zama tamkar dimokradiyya wato na jama’a, domin jama’a, kuma daidai karfin jama’a. Don haka wannan mataki ba zai inganta ba sai mu jama’a mun shigo ciki dungum don ba aikin gwamnati ne ita kadai ba. A matakin aikin gaiya ne na kwashe shara da kwatami, ko a samar da motoci da kwandunan kwashe shara ne, ko a kiyaye zubar da ita sharar a inda bai dace ba, duk ba wanda zai mana sai mu da kanmu. Kananan asibitocinmu mu hada gwiwa da karamar hukuma misali ta dau nauyin sa kayan aiki da magunguna mu kuma mu dau nauyin biyan albashin likita da mai aikin jiyya duk wata. Ka ga idan kananan cutuka suka tashi ba sai an garzaya da maras lafiya babban asibiti ba.

Duk duniya an yi amanna cewa harkar lafiya tsada gareta, don haka ne ma babu kasar da ta samarwa da al’ummarta cikakken kiwon lafiya daga aljihun gwamnati kawai, komi kudin kasar kuwa. Kasashe irinsu Jamus da Sweden da Birtaniya da harkar lafiyarsu ta fi ta kowa a duniya, matakin lafiya na farko suka inganta, shi yasa sauran matakan biyu na sama (secondary da tertiary) suka yi karfi nesa ba kusa, saboda an rage musu nauyi. Muma da zamu ragewa manyan asibitocinmu nauyi dole su inganta sosai sufi na yanzu karfi. A wadannan kasashe da na lissafa, a cikin kashi 100 na kudin da ya kamata ya tafi bangaren kiwon lafiya, kashi 30 cikin dari kawai gwamnati ke samarwa, sauran kashi 70 al’umma ne ke fitarwa ta hanyar haraji, don haka harajin da ‘yan kasa kan fitar yake da yawa a can.

To tunda mu kudaden harajin da ake samu a kasashenmu bai taka-kara-ya-karya ba, ba a ce za a barwa gwamnati komai ba, ko don saboda rashin dorewar aiyukanta. An san al’ummarmu da yunkurin tara kudi a kungiyance ko a unguwanni don ginawa da tafiyar da manyan-manyan wuraren ibada, da makabartu da makarantu masu zaman kansu da ma sauran harkokin tafi da rayuwa, amma ba a sanmu da yin hobbasa wajen samar da wuraren samun lafiya ba. An barwa gwamnati da likitoci masu zaman kansu, a wuraren da ma aka samu kenan.

To wannan hobbasa don ganin matakin farko na lafiya ya samu a kowanne lungu da sako shi muka rasa. A mafi yawan lokuta sai an dauki maras lafiya nisan duniya zuwa babban asibiti wanda shima da wuya a duba mutane a kyauta. Mun bar asibitocinmu na kusa damu da ake kira asibitin sha-ka-tafi wato dispensary (suma idan akwai kenan) sun zama ba magunguna ba likita. Wasu lungunan kuma sai kyamis-kyamis da masu saida magunguna a titi wadanda mafi yawancinsu basu iya rike biro ba ballantana allura. A kasashen da na lissafa a sama irin wadannan kananan asibitocin sha-ka-tafi sune daidai da manyan asibitocinmu. Su kuma manyan asibitocinsu abin ba a cewa komai.

Alal misali a kasashen Yarabawa na ga manya-manyan asibitoci da jama’ar gari ke samarwa kuma su tafiyar dasu da kansu ba tare da sa hannun gwamnati ba. Masu hannu da shuninsu su suka fi taimakawa. Sa’annan ga kungiyoyin kasashen waje nan masu taimakawa da abubuwa dabam dabam saboda ganin yunkurinsu.

3 thoughts on “RAWAR DA ZAMU IYA TAKAWA A FANNIN KIWON LAFIYA

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s