RUWAN GISHIRI DA SUKARI

Ina neman bayani kan alakar ruwan gishiri da sikari da kuma wanda ake karawa mutum a asibiti ta hanyar jijiya. Mene ne kuma amfaninsu?

-Abdul Warakat, Ayagi.

Tun lokacin da aka kirkiro sinadarin ruwan gishiri da sikari wajen shekaru talatin da suka wuce, har yau ba a ga sinadari mai ceto rayuka ba kamarshi. An kirkiroshi ne bayan an fahimci ire-iren sinadaran gishiri da ruwan jikinmu ke dauke da shi.

Shi ruwan gishiri iri-iri ne, akwai irin wanda ake hadawa a gida akwai kuma na hukumar lafiya ta duniya da ke zuwa a sacet mai suna ORS, akwai kuma na asibiti da ake sawa ta jijiya. Dukkansu ana bawa mai gudawa wanda ruwan jikinsa ya fara karewa, musamman yara wadanda gudawa ko zawo yafi galabaitarwa. Ana gane cewa ruwan jikin yaro mai gudawa ya fara karewa ta alamomi a jikinsa kamar haka;

1.      Yaushin fata,

2.      Kuka ba hawaye,

3.      Bushewar lebe,

4.      Rashin kuzari,

5.      Ko a ga idanuwa sun fada

6.      Ko a ga fitsari dan diris ko wanda kalarsa tayi duhu (ruwan dorawa) sosai.

A irin kasashenmu bayan zazzabin cizon sauro zawo shine ke saurin salwantar da rayukan yara kanana.

Da zarar an ga wadannan alamu ko da a babban mutum ne mai zawo, ba jira sai a fara bashi ruwan gishiri da sikari wanda ake hadawa a gida kafin a rankaya asibiti. Ana hada irin wannan ruwa ne idan aka zuba gishiri kwatankwacin karamin cokali daya da sikari kwatankwacin karamin cokali gomaa cikin kofi daya na ruwa. Ko kuma a sayo na hukumar lafiya dan sacet a zuba a kofi daya na ruwa. Sai a gauraya a rika bayarwa a hankali ba tashi guda ba. Duk a wannan hali ana ba maras lafiyar abinci yaci kamar yadda ya saba koda gudawa bata tsaya ba, idan yaro ne ba a yaye shi ba shima a ci gaba da bashi nono.

Ba lallai sai irin wannan ruwan gishiri da sikari na hadi ba, akan iya bada ruwan da aka fara dafa shinkafa da shi, wato ruwan da ke bararraka shinkafa idan ta dauko dahuwa, don shima ruwan yana da gishiri da sikari sanadiyar gishirin da aka barbada, shi kuma sitacin shinkafar sikari ne. Haka ma farfesu maras yaji ko romo, shima ana so a ba mai gudawa don ya maida ruwan jikinsa. Su wadannan ruwan shinkafa da na romo bincike ya nuna bayan karin ruwa da sinadaran jini a jiki, har sukan taimaka zawo ya tsaya. Wadannan sune ruwan gishiri da sikari na gida.

Idan aka je asibiti likita ya ga mai gudawar na bukatar karin ruwa cikin gaggawa ko kuma amai ko kumallo ya hana bayarwa ta baki, sai ya sa masa na roba wato na jijiya. Shi na robar shima iri-iri ne, akwai mai gishiri kawai, akwai mai gishiri da sikari akwai kuma mai sikari kawai, akwai kuma mai dukkan sinadaran da jini da ruwan jiki ke dauke dasu. Dukkaninsu ana iya bayarwa gwargwadon abinda mutum ke bukata a wannan lokaci.

Wane irin abinci ya kamata a ba yaro dan wata shida?

-Habibu, Gusau.

Daga wata shida bayan ruwan nono, akan iya fara ba yaro ruwa mai tsabta (tunda da munce ba a ba jariri ruwa har tsawon wata biyar ko shida sai ruwan nono kacal). Wannan ne zai kare shi daga kamuwa da kwayoyin cuta masu sa zawo. A wannan wata ne kuma ake so a fara sabawa yara da abinci mai dan ruwa-ruwa, wato kamu mai madara da ayaba, ko kunun gyada, ko cerelac, ko frisocrem daidai karfin mutum. Haka har wata tara inda za a kara da irinsu dafaffen kwai, indomie, taliya, da sauran abinci maras nauyi kamar ‘ya’yan itatuwa.

Ina tambaya ne akan lemon tsami, don an ce yana da illa. Kuma idan ba illa ana iya sha a shayi? Kuma da gaske yana da sinadaran rage kitse?

Khadija, Hotoro.

A dan binciken da na gudanar ban gano inda aka fadi illar lemon tsami ba indai shansa za a yi ba sawa a wani wuri ba. Wurin da aka ce yana wa illa kawai shine hakora saboda sinadarin acid din citric acid. Wato idan ana yawan shansa zalla ba a abinci ba na tsawon shekaru, zai iya kashe hakora.Amma amfaninsa yafi illar yawa.  Don haka idan aka sashi a abinci ko shayi kamar yadda kika fada, zai iya rage karfin acid din. Bayan acid akwai sinadarai da dama irinsu vitamin kala-kala a cikinsa masu kara lafiya, da sinadaran anti-oxidants masu kona kitsen jiki.

Idan mace ta samu ciki a mara yake zama koda yaushe? Kuma wane wata yake fara motsi?

-Safiya, Samarun Zariya

Mahaifa dai a mara take. Kashi 98 cikin dari na ciki na zama a mahaifa. A ragowar kashi 2 ciki zai iya zama ko ina a wajen mahaifa ko a mara, bayan mahaifar ko a gefe, ko kuma a ciki kusa da hanji. Shekaru biyu da suka wuce a kasar Birtaniya da kuma Australia an yi wa wasu mata tiyata a ciki an fidda ‘ya’ya ‘yan watanni tara da suka rayu a ciki kusa da hanji ba a mahaifa ba. A mafi yawan lokuta dai, wannan ciki kan zama hadari ga lafiyar uwar. Akan iya kiyaye irin wannan idan ana zuwa awo.

Jariri a mahaifa kan iya fara motsi lokacin da aka busa masa rai tun daga misalin wata na hudu ko kwanaki 120.

One thought on “RUWAN GISHIRI DA SUKARI

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s