HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR KANJAMAU


Ina son cikakken bayani a game da cutar kanjamau (HIV/AIDS). Shin za a iya daukar ciwon bayan an sadu da mai dauke dashi sau daya kawai? Za a iya dauka idan wani ruwan jikin mai cutar ya taba mutum? Mene ne alamun ciwon? Kwanaki nawa kwayar cutar ke dauka kafin ta bayyana a awon jinin mutum don idan mutum yayi gwajin akan ce ya sake dawowa bayan watanni a sake.

-Sani Musa da Basira Azare

Cutar kanjamau ciwo ne da kwayoyin cuta na virus ke kawowa. Wadannan kwayoyin cuta ba kamar na bacteria ba, suna da wuyar sha’ani, domin suna hayayyafa fiye da yadda wani magani zai yi musu tasiri. Wato ana hayayyafarsu suma ‘ya’yan suke kara hayayyafa kamar kiftawar ido. Wannan itace kwayar cutar HIV. Kwayoyin kan mamaye kwayoyin garkuwar jiki ko sojojin jiki. Ciwon da suke sawa kuma shine AIDS wato mutuwar wadannan sojoji na jiki.

Yadda ake daukar kwayar cutar:

Hanyoyi hudu da aka tabbatar ana daukar ciwon sune;

 1. Saduwa da mai ciwon,
 2. Karin jini mai dauke da kwayar cutar
 3. Daga uwa zuwa jaririnta.
 4. Daga kayan kaifi

Saduwa da mai ciwon ko da sau daya ne da mu’amala ruwan jikin mai ciwon kamar miyau zai iya sa wanda bai da ciwon ya kamu, musamman idan akwai ciwo ko miki a daidai wurin saduwar ko kuma a inda ruwan jikin mai ciwon ya taba. Za a iya kamuwa bayan saduwa ko da kuwa an sa kariya domin kwayoyin cutar sukan iya bi ta kananan kofofin robar, don sun fi kofofin duk wata kariya kankanta. Idan da kariya, to akan iya rage hadarin kamuwa daga kashi 100 zuwa kashi 90. Shi yasa ake so ayi gwajin jini kafin auratayya. Mai dauke da cutar ba zai auri maras cutar ba, sai dai dan uwansa mai cutar.

Sai kuma karin jini da ake wa wasu ba tare da an gwada jinin ba. Akwai masu dauke da wannan ciwo da dama da suka kamu da wannan ciwo saboda irin wannan kuskure. To wani ya ce sauro da ke zukar jinin mutane ya dura wa wasu me ya sa baya sawa mutane? To bincike ya nuna kwayar cutar mutuwa take a cikin sauro ba kamar ta maleriya ba.

Ita kuma hanya ta uku, wato daga uwa zuwa jaririnta, na iya faruwa tun jariri na ciki, ko kuma yayin haihuwa ko kuma ya dauka yayin shayarwa.

Hanya ta hudu, wato ta kayan kaifi, na faruwa ne yayin da aka yi amfani da reza, aska, kaho ko allura wadda mai kwayar cutar yayi amfani dasu.

Ba a iya dauka don kawai an zauna da mai ciwon ko an taba jikinsa ta mu’amala ta yau da kullum kamar gaisuwa ta musabiha da sauransu.

Alamun Ciwon:

Shigar kwayar cutar jikin mutum ba lallai ne yazo da wata alama ba, don sai mutum yakai shekaru goma ma yana dauke da kwayar cutar amma bata kawo masa ciwon kanajamau ba. Wadannan sune masu yawan sojojin jiki. A wasu mutane kuma marasa karfin garkuwar jiki da kananan yara, watanni ne kawai kwayar zata yi a jikinsu su fara nuna alamu.

Alamun sune a ga mutum yana rama wata da watanni kuma yana cin abinci kamar kowa, ko gudawa wato zawo wanda yaki jin magani tsawon satuttuka, ko a ga yana tarin da yaki jin magani shima na tsawon satuttuka sakamakon cutar TB wadda tafi kamasu. Hakanan duk da cewa tarin TB shine babbar alamar ciwon kanjamau a irin kasashenmu, ba lallai bane kuma mai tarin TB ya kasance yana da ciwon. Wadannan sune manyan alamu amma akwai kuma sauran alamu da dama. Wato duk wani ciwo da yaki ci yaki cinyewa, zai iya kasancewa sanadiyarsa shine ciwon kanjamau.

Gwajin jini:

Akwai cibiyoyi na gwajin jini kyauta a wurare da dama don sanin ko mutum na dauke da wannan ciwon ko a’a. Yana da kyau kowa ya san ko yana dauke da wannan ciwo ko kuma akasin haka. Amma wadannan rukunin mutane da zan lissafo dole ne suje a yi musu; idan mutum na shirin sabon aure, ko kuma mai auri-saki ne, ko wanda aka taba yi masa karin jini ko lafiyayyen mutum wanda yaje kai gudunmowar jini asibiti aka ki daukar nasa, ko wanda ake yawan yi masa amfani da kayan kaifin da ba a tsabtace su ba, ko kuma yaron da iyayensa ke da ciwon. Amfanin gwajin kafin cutar ta bayyana yafi yawa nesa ba kusa ba fiye da idan cutar ta bayyana.

Idan alamun cutar basu bayyana ba aka yi gwajin jini aka ga kwayar cutar, to sai an yi masa wani gwajin a mataki na biyu a ga ko yana bukatar magungunan da zasu rage yawan kwayar cutar a jikinsa ko kuma shawarwari kawai yake bukata na yadda zai yi rayuwa kamar kowa. Idan kuma akayi gwajin jini ba a ga cutar ba, a wasu lokuta akan ce mutum ya dawo bayan wata shida a sake gwadawa don dai a tabbatar. To duk wanda akayi masa wannan gwajin sau biyu aka babu, to kusan a iya cewa baya dauke da kwayar cutar. Gwajin cutar na ELISA wani gwaji ne da ba a yinsa kyauta saboda tsadarsa kuma ana yina sau daya kawai zai nuna mutum na da ciwon ko babu. A wasu lokuta a asibiti idan mutum yaje ba da gudunmowar jini aka dau nasa bayan anyi wani gwaji to kusan bai da ciwon kenan don gwajin kwayar cutar kanjamau (HIV) da na hanta (hepatitis) akeyi dama.

Hanyoyin kariya:

 1. Kamewa har sai anyi aure
 2. Tabbatar an yi gwajin cutar ga wanda za ka/ki aura kuma a nuna takardar shaida kafin a daura auren
 3. Tabbatarwa cewa jinin da za a karawa mutum an gwada shi a asibiti
 4. Awon mata masu juna biyu
 5. Ka tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko an kona su da wutar lighter ko an wanke su da sinadarin bleach kafin ayi maka amfani dasu
 6. Zuwa cibiyoyin gwaji don sanin matsayin mutum na taimakawa rage yada ciwon

32 thoughts on “HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR KANJAMAU

 1. Menene mafuta, ina famada matsanaycin ciwon kai na tsayon shekara guda, naje asubiti anyimun kwaje-kwaje ciki harda RVS, Nakan koma asibutin kowace wata ana sakeyimun kwajin RVS harna tsawon shekara guda, akan cemun babu amma haryanxu ciwom kai yakiyin sauki. Naji kace duk ciwonda taki jin magani tana iya zamowa kanjamau, ina mafita?

  Like

  • Idan nagane tambayar ka,kana nufin ana iya kamuwa da cutar wajen kiss? Tabbas ana kamuwa sai dae yadda xa’a kamu ta wanan hanya ne bai da yawa, idan mai dauke da ciwon yana da open sores a harshen sa ko a baki, wajen xchanging miyau xaka iya kamuwa da wannar cuta inhar ka karbi miyau dake hade da jinin mai dauke da wannan cuta.

   Liked by 1 person

 2. assalamu alikum yan uwa zanyi amfani da wannan dama akan baiwa yan uwa shawara akan sukiyaye kansu da kamuwa da wannan cuta maikarya garkuwar jiki.kuma ita wannan cuta tana da hanyoyi dayawa nakamuwa da ita wannan cuta maikarya garkuwar jiki.Akarshe duk masu wannan cuta Allah ya basu lafiya,wadanda kuma basu da ita Allah ya karesu Ameen.

  Like

 3. Idan mutun yake ta gudawa hartsawon wata 3 batatsayaba kuma anyitayin gwaje_gwaje hartsawo wata 4 ba’agakomaiba hakan yananufin yanadauke da cutar?

  Like

 4. IDAN MUTUM YAYI AMFANI DA KWARORON ROBA KUMA SAI KA GAMA BAI YAGEBA. AN CIRE SAI MANIYI YA DIGA A WURIN GASHIN GABAN MUTUM KAYI DA GASKE NAN TAKE KA GOGE AKWAI YIWUWAR KAMUWA?

  Like

Leave a Reply to Saifullahi Ado Cancel reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s