HANYOYIN KARIYA DAGA YOYON FITSARI


Muna so mu san me ke kawo yoyon fitsari? Kuma ya za a kiyaye shi?

-Shu’aibu Ubale Freedom

Abubuwan da kan kawo yoyon fitsari guda uku ne, doguwar nakuda, da yiwa mata kaciya da kuma yiwa mata yanka ko kari yayin haihuwa. Doguwar nakuda takan faru sanadin abu biyu; imma dai kugun uwar matsattse ne, ko kuma kan jariri kato ne. Idan kugun uwa matsattse ne ko dan karami kuma kan jariri daidai yake, to kugun zai rike kan jariri ya kasa fitowa. Hakama idan kugun uwa daidai yake wato wadatacce ne amma kan jariri kato ne, to kan jariri zai makale ya kasa wucewa. Idan dayan biyun ya faru, maimakon mace tai nakuda cikin ‘yan awoyi, sai ta yini ta kwana, wato nakuda ta zama doguwa kenan. To wannan yakan sa kan jariri ya rika gogar fatar da ta raba mafitsara da wurin haihuwar ta koke, fitsari ya fara yoyo, kuma a mafi yawan lokuta akan rasa jaririn saboda wannan matsi.

Ana iya kare aukuwar haka tun daga fara zuwa awon ciki inda za a iya sanin girman jariri har zuwa haihuwa a asibiti. Idan mace bata son haihuwa a asibiti to yana da kyau ta kira kwararriyar ungozoma wadda aka ba horo na zamani. Ita wannan ungozoma ta san lokacin da yakamata nakuda ta kare, ta kuma san lokacin da dole sai an rankaya asibiti don yin tiyata a cire jariri kafin ya rasu ko kuma kafin yoyon fitsari ya auku. Har ila yau ita wannan mata ta san daidai inda akewa mata kari ta yadda ba zata yanks mafitsara ba.

Hanya ta uku ta samun yoyon fitsari itace ta yiwa mata kaciya ko yankan gishiri ko angurya da wasu wanzamai ke yi, inda cikin kuskure suke taba mafitsara da aska hart a huje fitsari ya fara yoyo. Ana iya kare aukuwar haka idan aka daina yankan gishiri kwata-kwata.

Duka dai a yanzu ana iya gyara ciwon yoyon fitsari kusan a kyauta, amma dai an ce riga-kafi yafi magani.

Wane wata ne mai ciki ya kamata ta fara zuwa awo? Kuma me ke kawo ciwon ciki mai tsanani a watannin ciki na farko?

-H. Umar

Da zarar mace tayi batan wata ake fara zuwa awo. A nan ne za a tabbatar ko ciki ne ko ba ciki bane ta hanyar gwajin fitsari. Bayan kamar wata biyu kuma ana sake komawa don ayi hoton ciki, musamman ma idan akwai ciwon ciki mai tsanani domin a gani cikin a mahaifa yake ko a wajen mahaifa.

Ina da ciki wata bakwai amma ciwon kafa da rikewar jijiyoyin kafa da ciwon kugu da na mara sun dameni me kawo haka?

-Safiya A, Samaru da wata baiwar Allah

Wadannan alamu ne na cewa cikin da yayi nisa, kamar yadda kika fada wata bakwai zuwa haihuwa saboda girman jariri da motsinsa. Wadannan alamu sun fi tsanani a cikin fari, wato idan ciki na biyu ya zo zasu zo da sauki, haka ma sauki zai karu a na uku har ki saba. A cikin farko kusan ba makawa sai kin sha wannan ‘yar wahalar kuma wani zubin paracetamol da sauran magungunan ciwon baya basa magani. Abinda yafi magani shine tausa. Wato mai gidanki ya rika yi miki tausa a kafa da baya da kugun wani lokaci da ruwan dumi wani lokaci da hannu.

Me yasa wasu mutane ke yin tika bayan sun ci abinci kamar yadda dabbobi suke yi?

-Bashir Ibrahim Fatakwal da Abdurrashid Yakubu da Abdullahi Tenten Amaco Foam

Idan dabba taci abinci takan koma gefe ta kwanta ta rika fito dashi kadan-kadan tana taunawa a hankali har yawu ya narkar dashi kafin ya bi uwar hanji, saboda cikinsu bashi da karfin sinadarai na asid masu narkar da abinci.

Tabbas akwai wasu daidaikun mutane da suke yin tika kamar dabbobi, wato bayan sun ci abinci sai kadan daga ciki ya rika dawowa wuya zuwa baki kafin daga baya su kara taunawa sannan su hadiye ko su tofar (rumination syndrome). Ana ganin kamar irin tunbudi (ba amai ba) wanda jarirai keyi shi ke bin mutum idan ya manyanta. A wannan yanayi babu yunkurin amai ko ciwon ciki, sai dai ‘yar rama idan mutum ya fiya yi. Don haka ba a cika bad a wasu magunguna don magance wannan matsala ba, domin magungunan nasara basa iya hana wannan yanati aukuwa. Shawarar da aka fi ba masu yi itace ta yin numfashi da ciki maimakon da kirji duk bayan cin abinci don abincin yayi saurin wucewa kada ya dawo wuya.

Tunanina ya kasa fahimtar abinda taba sigari ke karawa jiki. Ko za ka yi min bayani akan amfaninta da illarta da kuma maganinta?

Ashir, Richifa

Duk da cewa masu shanta suna jin dadinta sosai ita taba sigari bata karawa jiki lafiya. Amma tabbas tana karawa jiki lahani. Abinda yasa ba’a rabuwa da ita duk da rashin karawa jiki wani abu da take yi shine saboda sinadarinta a kwakwalwa yafi aiki. Wannan sinadari shine nicotin, wanda banda kwakwalwa yakan iya yiwa zuciya illa da magudanan jini da fatar jiki lahani. Akan iya ganin taruwar wannan sinadari a fatar mai shan sigari ta yadda za a ga fatar tayi baki. To hakama duk sauran sassan jiki da ba a iya gani ke kasancewa, wanda zai sa a hankali su mutu.

Daya illar kuma ta taba sigari itace ta hayakin. An yi amanna cewa wannan hayakin ne kawo ciwon daji na huhu. Illar hayakin bata tsaya kan mai sha kawai ba a’a har wanda yake wurin idan ana sha. Misali idan mai gida na shan taba a cikin gida to duk mutanen gidan wadanda suka ji warin tabar kamar sun sha ne. Wasu likitoci suna ganin kamar hayakin bayawa mai sha illa kamar yadda yakewa na kusa dashi tunda hayaki yawo yake. Hakan yafi illa kuma ga kwakwalwar kananan yara dake wurin ko yaron dake ciki idan mace mai juna biyu na wurin da ake busa hayakin.

Da yake tana zama kamar alakakai kadangaren bakin tulu (ka daina ta sa ka ciwo, ka ci gaba shima ciwo) saboda wancan sinadari mai aiki a kwakwalwa, barin shan taba na da wuyar gaske. Mai son ya daina zai iya zuwa ya nemi wani cingam mai dandanon nicotin don ya rika taunawa. Wannan zai sa yaji a ransa kamar nicotin din yake zuka har idan akai sa’a ya manta da sigarin.

Ni an cire min tsakuwa a koda har sau biyu kuma na karanta a hanyoyin kariya daga ciwon koda a wannan mujalla inda naga kace a rage cin jan nama da alaiyahu da kofi. To naman har da na kaza? Ina son karin bayani

-Muhd Baba, Gombe

E yawan cin nama musamman a irinku wadanda aka cirewa tsakuwa ko a koda ko a matsarmama kan sa tsakuwar ta sake taruwa saboda sinadarin uric acid wanda kan dunkule ya zama tsakuwa. Kuma naman har na kaza da kifi. Abinda nace shine a rage yawan ba daina ci dungurungum ba. A irin kasashenmu irin cin nama da muke yi yanka daya ko biyu a cikin abinci ba zai zama hadari ba. Hadarin shine idan kai da aka cirewa tsakuwa kana ci da yawa kamar irin na lokacin laiya da babbar sallah, to zai iya sa tsakuwa sake taruwa, amma ba cin yanka daya ko biyu a rana ba. Idan kaci naman to ka tabbata duk inda ka shiga a wannan ranar sai ka sha ruwa don yayi saurin wanke wancan uric acid a fitsarinka. Alaiyahu da kofi suma suna sa tsakuwa mai sinadarin oxalate taruwa a irinku.

Sauran mutane wadanda ba a taba cire musu tsakuwa ba ko kuma ba wasu a danginsu na kusa da aka taba cirewa za su iya ci ba matsala.

Ni kuma gidana da motata da ofis duk akwai na’urar sanyaya wuri ta AC. Anya babu illa kuwa ga lafiyata, idan akwai kuma ya zan kare kaina?

-Nasir Ibrahim Jagoran Falasdinawa

Idan dai ana yiwa nau’rar sabis akai-akai to ba wani hadari a irin yanayinmu na zafi. Domin bayan sanyaya wuri na’urar AC takan tace kwayoyin cuta dake cikin iska wadanda idan aka shaka kan iya zama lahani. Yin sabis akai-akai don wanke wadannan kwayoyin cuta da nau’rar ta tara daga ciki zai rage yawan mura da takan jawo.

12 thoughts on “HANYOYIN KARIYA DAGA YOYON FITSARI

 1. Salam,likita me ke sa kumburin kafa da hannuwa da ciwon kai ga mai cikin wata shidda zuwa bakwai?,sai tambaya ta biyu shin me kesa idan macce taje awo alhalin tasan watan cikinta don tasan sadda taga al adatarta karshe amma sai acce cikin ya gota hakanan kamar ita tasan yana wata 6 sai acce wata 7 ko 8

  Like

   • Mace ce take da ciki tun Yana wata vakwai take fama da ciwon Mara Idan taje awo sai arubuto Mata plagyl da suproxin da wasu makamansu Amma haryakai wata Tara Bai bariba
    Dan Allah muna bukatar shawarwarinka

    Like

   • Ai kuwa maganin ciproxin bai dace a ba da shi ga yara da mace mai juna biyu ba domin yana iya tava lafiyar qashin yara ko jarirai. Shawara ita ce, ta dakatar da waxannan magunguna na flagyl da ciproxin, ta kuma canza wurin awo ta koma ko da na kudi ne. Yadda ake canza wurin awo shi ne, sai ku karvi takarda daga inda kuke awon na yanzu ku kai musu a sabon wurin da kuke so a ci gaba da awon. Idan sun tambayi dalili ku fada musu qorafinku, watakila su gyara. Idan ta je sabon wurin awo a faxawa likitan wurin abinda ya faru a can, a sake hoton scanning da aune-aunen jini da fitsari don a gano abinda ke kawo ciwon marar sosaiAi kuwa maganin ciproxin bai dace a ba da shi ga yara da mace mai juna biyu ba domin yana iya tava lafiyar qashin yara ko jarirai. Shawara ita ce, ta dakatar da waxannan magunguna na flagyl da ciproxin, ta kuma canza wurin awo ta koma ko da na kudi ne. Yadda ake canza wurin awo shi ne, sai ku karvi takarda daga inda kuke awon na yanzu ku kai musu a sabon wurin da kuke so a ci gaba da awon. Idan sun tambayi dalili ku fada musu qorafinku, watakila su gyara. Idan ta je sabon wurin awo a faxawa likitan wurin abinda ya faru a can, a sake hoton scanning da aune-aunen jini da fitsari don a gano abinda ke kawo ciwon marar sosai

    Like

   • Akan samu kumburi na qafa da hannaye da ma jiki gaba xaya nau’i biyu a mai juna biyu; da na lafiya da wanda ba na lafiya ba. A ido ba za a iya cewa wannan kumburi lafiya lau ba sai an yi awo, an auna hawan jini da fitsari. Hawan jini da taruwar sinadarin protein a fitsari yakan nuni da cewa kumburin ba na lafiya bane. Amma idan ba hawan jini ba kuma wani abu a fitsari, to za a iya cewa ba matsala. Shi nau’i mai matsalar sai an fara shan magungunan rage hawan jinin dole. Don haka duk mai juna biyu wadda ta ga sabon kumburi a qafafuwa sai ta koma awo an sake dubawa an tabbatar ba matsala.

    Like

 2. Aslm likita wai mekesa ciwon kai da maimayi ta gefen dama kusa da ido kuma menene magani daga maman ummi kd

  Like

  • Ciwon kai irin wannan a likitance zai iya zama xayan uku, tunda kin ce yana zuwa har kusa da ido, zai iya zama na migraine ko na matsalar murar sinusitis ko na irin wanda muke kira cluster wanda ya fi kama masu yawan aiki ba gajiya da ‘yan sigari ko masu yawan shan barasa. Dukkansu dai suna shige da juna amma idan kika je likita ya duba ki zai iya tantance ko wane ne ya ba ki magani, domin wasu lokuta ko an sha magungunan kashe raxaxi irinsu parasitamal ba sa dainawa

   Like

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s