HANYOYIN KARIYA DAGA ZAZZABIN LASSA

Zazzabin Lassa wani ciwo ne da kwayoyin cutar virus ke kawowa. Su kuma wadannan kwayoyi beraye ne ke yada su. Bayanai sun nuna cewa, an fara samun bullar cutar zazzabin Lassa ne a kauyen Lassa dake jihar Barno, a arewacin Najeriya, shekaru fiye da hamsin da suka gabata.

A cikin wadannan shekaru, cutar ta samu bulla wasu kasashen a yammacin Afirka, wato kasashe irinsu Guinea da Saliyo da kuma tsakiyar Afirka. Alkaluma dai suna nuna cewa, mutane fiye da dubu 300 ne kan kamu da zazzabin Lassar a kowace shekara a duniya.

Bincike ya nuna cewa, an gano bullar cutar ne, yayin da wata malamar asibitin koyarwa na jami’ar Fatakwal ta kamu da zazzabin, wanda kuma ya zama ajalinta.

Daga bisani kuma an gano wasu mutanen da suka kamu da cutar .

A yanzu haka kuma ana samun bullar cutar a garuruwa irinsu Taraba da.

 

Ta yaya ake kamuwa da ciwon?

Beraye sukan yi yawo a gidajenmu su je neman abinci musamman da dare. Wasunsu a irin wannan lokaci sukan kwaso wadannan kwayoyi na virus. Wasu sukan hauro ta katanga, wasu sukan shigo ta rariya, wasu kuma ma suna da ramuka cikin gidajenmu. Idan suka taba abincin da yake a bude, sukan iya sa mana wadannan kwayoyi abinci, mu kuma mu dauka in mun ci. Wasu lokuta ba sai sun taba mana abinci ba, kashinsu da fitsarinsu kan iya yada kwayoyin cutar ta hanyoyin numfashi idan muka shaki warin.

Ana kuma iya daukar ciwon ta hanyar taba jikin mai ciwon, musamman a ma’aikatan asibiti.

 

Alamomin ciwon

Akwai zazzabi, sai ciwon ciki da amai da gudawa, wadanda za a iya ganin jini a ciki. Babu inda ciwon bai iya tabawa, domin za a iya jin kasala, ciwon kai, tari, mura da dai sauransu. Don haka babu dai takamaimai wata alama guda daya da za a danganta ciwon da shi.

 

Hanyoyin Kariya

1. Kada a rika bari beraye suna samun sukuni a cikin gidajenmu; a nemi ramukansu a tottoshe musamman a dakunan da ake ajiyar abinci wato store; a kuma kawo mage cikin gidan.

2. A daina barin abinci a bude ko da yaushe ya zama a rufe, kada wani abu ya shiga

3. A daina barin kwanukan abinci suna kwana ba wanki. Mun san yawancin gidajenmu akan bar wanke-wanken kwanuka zuwa da safe, wanda hakan kan iya jawo beraye su hau kwanukanmu cikin dare. Ko da an yi wanke-wankenma, a dauraye su sosai kafin a zuba abinci

4. Idan an yi wanke-wanke a share guntattakin abinci sosai, kada a bari su shiga rariya, don gudun kada ya jawo beraye.

5. Idan an ga fitsari da kashin beraye kada a share sai an sa kyalle an rufe hanci tukuna

6. Idan an ji zazzabi da ya wuce kwana biyu, ko ya ki jin magani, a garzaya asibiti

7. Idan ana da maras lafiya wanda ake tunanin yana da wannan ciwo, kada a rika taba shi sosai ko amansa, a sa leda a hannu kafin a yi aikin amai.

4 thoughts on “HANYOYIN KARIYA DAGA ZAZZABIN LASSA

  1. Slam! Dama lassa sunan garine ba cutaba kuma mene gaskiyar cutar mufa min fi shekara 30 muna hurda da beraye bamu taba samun matsala ba! Amma duk da haka zamu dauki mataki. Mun gode Allah yasaka da alheri!

    Like

  2. salam docter dan allah inaso aimin bayani akan ciwom jijjiga ga wanda yasamu ta sanadin”typhoid” kuma meye banbancinsa dana masu haihuwa.

    Like

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s