Hanyoyin Kariya Daga Saran Maciji

MacijiyaA Najeriyarmu ta arewa an fi samun macizai a jihohin Arewa maso gabas irin su Bauchi da Gombe da Taraba da Pilato, musamman a garuruwan Billiri, da Kaltungo da Alkaleri da Langtan da makwabtansu. Akan samu ma a Borno da Adamawa da kauyukansu. Ko a bana ma a wadannan yankuna an samu karuwar wadannan macizai wadanda aka yi hasashen cewa daga Kasar Kamaru suka shigo sakamakon ambaliyar ruwa da ya biyo dasu nan.

An fi samun wannan matsala ta sarar maciji a tsakanin Manama da makiyaya da mafarauta da masu wasa da maciji.

Macizai masu sara da dafi ba su kai marasa dafi yawa ba, domin da yawa za su iya yin sara ba tare da sun harba dafi ba. Haka nan ma akwai irinsu mesa wadda ba ta sara sai dai ta kama mutum ta nannade a jikinsa ta matseshi ta yadda zai kasa numfashi, har ya ce ga garinku.

 

Alamomin sarar maciji

Yawanci duk wadanda maciji ke sara maza ne ba mata ba, kuma an fi samun wannan matsala a daji ko a gona. Mutumin da maciji mai dafi ya harbeshi za a ga ‘yar kafa ko tsaga a fatarsa ta inda dafin ya shiga, akan ga jini a wurin saboda yawanci dafin macijin kan tsinka jini, jini ya yi ta zuba ta kafafe da dama ya qi tsayawa. Za a ga jinin har ta baka, a wasu lokuta. Sauran alamun sun haxa da firgita da dimaucewa saboda ba tsammani yawanci abin ke faruwa. Mutum kan iya kasa motsi idan dafin ya shiga jijiyoyin laka, a wasu lokuta ma numfashi gagara yake.

A yawancin lokuta wurin da akai saran ba ya wani zogi, sai dai idan a ido aka fesawa mutum dafin nan da nan zai ji radadi ya fara gani dusu-dusu, idan ba a dau mataki da wuri ba ma har makanta dafi a ido kan sa.

Yana da kyau idan an ga macijin a kashe shi a tafi da shi asibiti domin a ba da maganin karya dafin wannan macijin. Idan kuma ba a ga macijin ba za a iya ba mutum maganin dafin kowane irin maciji a asibiti. Wato a asibiti akwai maganin dafi iri-iri, akwai na duka macizai, akwai kuma na macizai daban-dabam. Kusan dukan wadanda akan kai asibiti aka basu allurar da wuri suna rayuwa.

 

Hanyoyin Kariya

 1. Manoma su rika sa takalma masu tsayi da kauri (sau ciki) kamar takalmin ruwa kenan idan za a gona, musamman ma idan a wancan yanki na kasar nan wannan gona take, ko kuma idan fadama ce inda ruwa ke kwanciya
 2. Idan aka ga maciji musamman idan mai dafi ne bai kamata a tanka masa ba, canza hanya ake a kyale shi ya wuce. Yawanci tsokana ce ko takura kan sa macizai harbi.
 3. Kada a rika sa hannu a cikin ramuka haka kawai
 4. A rika yawo da fitila a hannu da dare musamman ga mutanen karkara masu ratsa ciyayi cikin duhu
 5. A kula da tsabtar muhalli musamman yanke ciyayi da gyara juji a mazauninmu na cikin gari.
 6. Macizai kan ziyarci wuraren da akan samu beraye da kwadi ko da a harabar gidajenmu ne domin wadannan qananan dabbobi sukan iya zama abincinsu.
 7.  Ya kamata hukumomi su rika sa alamu na tunatarwa a wuraren da aka san ana samun macizai, a rubuta varo-varo kamar haka “HANKALI DA MACIZAI”.
 8. Da zarar maciji ya sari mutum a yi sauri a kai shi asibiti domin ba shi allurar da ta dace
 9. Kada a sa kashin dabbobi wato irin takin nan na kashin dabbobi a wurin ciwon kamar yadda wasu suke yi, don hakan zai iya sa kwayoyin cuta musamman kwayar cutar tatanas mai sa ciwon sarke hakora. Za dai a iya sa ruwa da sabulu a wanke wurin kan a isa asibiti.
 10. Kada kuma a daure saman wurin da abin ya faru don gudun kada dafin ya bi jini. Yin hakan kan iya sa wannan bangare na jikin ya mutu saboda rashin gudanar jini.
 11. Kada kuma a ce za a tsaga wurin da aska ko a ce za a zuko dafin da baki.
 12. A yanzu haka hukumomin lafiya na kasa-da-kasa kan kai alluran dafin macizai asibitocin yankunan da suke da yawan macizai, saboda a yi saurin ba wa maras lafiyar. A yankunan da ba a fiya samun sarar maciji ba sai an je babban asibiti.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s