‘AN KAWAR DA CUTAR KURKUNU A WANNAN KASA’

Ciwon KurkunuHukumomin lafiya na kasa da ma na duniya a karshen shekarar da ta gabata sun yi iqirarin cewa a yanzu an kawar da wannan ciwon gaba-daya daga kasar nan. Hukumomin suka kara da cewa yau shekaru uku kenan ba a kawo musu rahoton wannan ciwo ba, kuma suma basu ga mai wannan ciwo ba a tsawon wannan lokaci. Don haka suke dakon manyan jami’ai na kasa da qasa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) domin su ba wa kasar nan takardar shaidar cewa an kawar da wannan cuta baki daya daga cikinta.

Tun cikin shekarar 2005 aka sa cewa Najeriya da sauran kasashe 5 (Sudan ta Kudu, Mali, Ghana, Ethiopia, da Chadi) wadanda suke da annobar wannan ciwo za su ga karshen wannan ciwo amma abu ya faskara. Domin a halin da ake ciki har yanzu akwai labarin wannan ciwo a Sudan ta Kudu da Chadi.

An fara yaki da wannan ciwo ne tun kimanin shekaru ashirin da suka wuce da kudin da kungiyar tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter ta samar. A lokacin kasashen Indiya da Pakistan, da Yemen duk suma suna fama da wannan annoba, amma a cikin ‘yan shekaru kadan su suka ga bayan ciwon. A wannan kasa a wancan lokaci babu inda ba a samu bullar ciwon ba, Kudu da Arewa.

A yanzu haka hukumar da ke da alhakin kawar da wannan ciwo a kasar nan wato Carter Foundation da ke da hedikwata a Jos ta saka ladan kudi na kimanin Naira dubu ashirin da biyar (N25,000) ga duk wanda ya kawo rahoton ganin mai wannan ciwo. Bari mu zayyana alamun ciwon ko da zaka dace da wannan lada:

Cutar kurkunu ciwo ne da wasu qwayoyin cuta suke kawowa. A gurbataccen ruwa mai dauke da kwayayen kwayar cutar ake daukar ciwon. Don haka za a fi ganin ciwon a karkara, kuma yawanci a garuruwan da suke da rafi a kusa da su.

Idan kwayayen suka shiga ciki, sai su zama macijin ciki. Daga nan ne tsutsar take saukowa kafa ta huda wajen agara ko idon sawu ta fara fitowa (za a ganta fara kuma doguwa a idon sawu), wurin kuma ya zama gyambo. Idan ta fara fitowa sai tayi kwanaki kan ta gama fitowa. Don haka a samu tsinke a nannade ta a jiki a rika janyo ta a hankali ba a lokaci daya ba kar ta tsinke, don in ta tsinke sai anyi tiyata an ciro ta. Kafar takan kumbura fiye da ‘yar uwarta ta yi ta ciwo.

HANYOYIN KARIYA

  1. A tace, kuma a bar ruwan rafi ko na rijiya mara zurfi ya kwanta, sannan in da hali a dafa kafin a sha.
  2. A rika wanke hannu da sabulu bayan an yi bahaya saboda kwayayen kan zauna a hannaye
  3. A rika kula da yara sosai kar suci kasa, a kuma rika yawan wanke musu hannuwa da sabulu duk lokacin da suka je wasa suka dawo
  4. Akai mai ciwon kurkunu asibiti mafi kusa ko a sanar da hukuma mafi kusa don daukar mataki
  5. A guji ba haya a kusa da magudanan ruwa ko gonaki ko fadamu saboda gudun yada kwayayen
  6. Dole hukumomi musamman na qananan hukumomi su ci gaba da samar da ruwa mai tsabta kamar rijiyoyin burtsatse ga jama’arsu

2 thoughts on “‘AN KAWAR DA CUTAR KURKUNU A WANNAN KASA’

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s