ILLOLIN MAKAMAN KARE DANGI

Su dai makamai masu guba kamar yadda sunansu ya nuna guba ce da su. Ban da kiransu da ake makamai masu guba, ana iya kuma kiransu da suna makaman kare dangi, saboda irin barnar da suke yi ga lafiyar al’umma.

Kasashen da ake ganin sun mallaki makaman kare dangi sune Amurka da Birtaniya, Sin, Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa, Faransa da Israila. Akwai kuma Indiya da Pakistan, da Sudan da Syria, sai kasar Iran. Sauran sune Masar da Afirka ta Kudu.

Ba kamar sauran makaman yaki irinsu bindiga mai harshashi da nakiyoyi da bama-bamai ba, su wadannan makamai ko ba a saita mutum da su ba idan aka harba su a sararin sama to duk wanda yake yankin da abin ya faru suna iya yin illa ga lafiyarsa, domin ana harba su, akwai masu bin iska, da masu shiga ruwa, sa’annan akwai kuma masu shiga kasa. Wato kenan nau’i nau’i suke zuwa: Akwai mai kamar gas, wato mai bin iska; akwai mai kamar ruwa, wato wanda zai saje da ruwa, akwai kuma za su fadi kawai a rairayi wadanda sai an tava suke illa, ko kuma su gurbata abinda aka shuka a kasar. Haka kuma dangane da yadda ake kera su, akwai wakanda ake kerawa da kananan kwayoyin halittu wato kwayoyin cuta irinsu bacteria da virus da fungus, akwai kuma wadanda ake kera su da ma’adinan karkashin kasa irinsu uranium. Akwai kuma wanda ake shiga dakin bincike a kirkiresu da sinadaran kyamikal irinsu plutonium, da sauransu.

Wasu ana harba su ne kamar yadda ake harba nakiya ko bam ta cikin bututun mizayil (wato linzamin makamin), don haka akwai mai cin karamin zango, akwai kuma mai cin nisan zango dangane da karfin linzamin da aka yi amfani wajen harba makamin. Duka-duka dai yawanci ba sa haura nisan zangon mil 2000, nisan daga Najeriya zuwa Libya misali. A lokacin yakin Tekun Fasha na shekarar 1990 tsakanin kasashen Iraqi da Kuwati, (wanda kasar Amurka ta shigarwa Kuwaiti) an yi ta yada jita-jita a nan gida Najeriya cewa an sako iska mai guba daga kasar Iraqi wadda idan muka shaka zamu iya mutuwa. A hakikanin gaskiya mun yi nisa da Iraqi ta yadda da wuya iska ta tunkudo mana gubar. Ana ganin kafin ta zo yankinmu iska ta sirka ta. Sai dai dama idan saita nahiyarmu akai, abin ya zo kasashen da suke makwabtaka da mu.

Misalan irin wadannan makamai masu bin iska sune gubar barkonon tsohuwa wato tiya-gas da gas din Sarin. Wadannan tunda shakarsu ake ta huhu suke shiga jiki su kawo lahani. Yawanci tiyagas na sa tari, mura, da zubar ruwan ido sosai, ko ma makanta. Shi kuma hayakin Sarin idan ya shiga jiki daga huhu sai ya je ya kama jijiyoyin laka ya rike, mutum ya kasa motsi, a haka har numfashi ma sai ya kasa saboda shima numfashi aikin motsi ne. Nau’insa ne ake sawa dan kadan a cikin maganin sauro na feshi.

Misalin makamin da sai an taba yake illa shine makamin hodar kwayar cutar bacteria ta anthrax irin wadda aka yi ta aikawa jama’a a kasar Amurka ta akwatin gidan waya a ‘yan shekarun baya, wadda da mutum ya bude ya taba hodar sai rashin lafiya wadda za ta iya kai shi ga halaka. An kiyasta mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun yi jinya sosai. Haka kuma za a iya zuba wannan kwayar cuta a gidan ruwa ta yadda idan aka tunkuda shi famfuna mutane suka sha za su iya mutuwa. Gubar da dwayar cutar Anthrax ke fitarwa idan ta taba jiki tana kona fata, wurin yayi rudu-rudu wanda ya fi karfin kunar wuta. Idan aka shaki kwayar kuma takan sa tari da mura mai tsanani. Idan kuma aka sha ko aka ci a abinci akwai ciwon ciki da amai mai tsanani. Duka dai kafin ka ce kwabo ta galabaitar da mutum.

Babu babban misalin makami mai guba da aka taba amfani da shi a duniya wanda ya girgiza ita kanta wadda ta harba kamar makamin nukiliya (wanda ake yi da makamashin uranium) da Amurka ta harba a garuruwa biyu na kasar Japan a shekarar 1945 wato garuruwan Hiroshima da Nagasaki. Makaman a tsakiyar gari kawai aka jefa shi a filin Allah, amma kan gari ya waye an ce mutane fiye da dubu dari ne suka mutum har lahira a garuruwan biyu, wasu dubu darin kuma cikin makonni da yin abin. Wannan ta faru ne saboda karfin girgizar garin da bam din ya sa, da karfin wani tiririn maganadiso mai kona jiki tun daga fata har cikin bargo da ake kira gamma radiation. Idan bai kashe mutum a lokaci guda ba, zai iya janyo rikidewar kwayoyin halitta na jiki ko su jawo ciwon daji. Wannan nakasu ta kwayoyin halittu har ‘ya’ya da jikokin mutanen da gubar ba ta kashe ba a wannan lokaci, sun gaje ta. Wasu haka kawai za su ga sumarsu na zubewa, wasu kuma fatarsu ce za ta qi lafiya. Da yake bargo ne gidan jini da yawa sun samu ciwon daji na jini, da wasu irin cutuka na jini da sai a lokacin aka fara ganinsu.

Haka ma an ce makaman kyamikal masu guba samfurin dioxine da Amurka ta rika yadawa ta jirgi mai saukar angulu a yakinta da Bietnam a shekarun tsakanin 1961 zuwa 1971, wanda ya shiga iska da ruwa, da kayan amfanin gona ya hallaka miliyoyin ‘yan kasar, kuma ya sa mata wakanda suka shaki gubar haifar jarirai masu tauyayyar halitta. Wato dai a duk duniya ba wanda ya kai kasar Amurka barna ta bangaren makaman kare dangi.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s