MATSALAR TSAMIN JIKI 1

A bi a sannu...gajiya tana kisa

Tsamin jiki (tsami na ciwo da gajiya, ba na wari ba), abinda muke kira lactic acidosis wata matsala ce ta yau da kullum da ya kamata mu duba. Idan mutum ya motsa jiki da ya wuce kima ko yayi aikin qarfin da ya wuce misali, naman jikinsa zai shanye duk wata iskar oxygen da dan abincin da aka tara a cikin naman. To idan ya kwanta barci namomin cikin jikin nasa sukan saki wasu sinadarai na lactic acid, masu kawo tsamin jiki. Banda wannan akwai rashin lafiyar ma da zata iya sa mutum ya riqa jin irin wannan, kamar qarancin jini misali, akwai kuma qwayoyi da za su iya sa hakan har ila yau.

 

Wannan na faruwa ne saboda su gavovin basu samu isasshiyar iskar oxygen da abinci ba a yayin da suke aikin qarfin. An fi yawan samun irin wannan a wurin ‘yan wasa kamar na qwallo ko na gudu, abinda suke kira fatigue ko a wurin ‘yan dako wato masu sana’ar daukar kayan nauyi. A wasu lokuta wanda aka wa dukan kawo-wuqa kan samu irin wannan, gami da taruwar jini a namomin da aka daka.

 

Idan mutum yana yawan samun irin wannan yana nufin baya cin isasshe ko lafiyayyen abincin da ya kamata kafin yayi irin wannan aikin qarfin. A likitance an ce a riqa motsa jiki a qalla na mintuna ashirin zuwa talatin a rana, to amma da zarar wannan motsa jiki ya fara wuce awa daya ba tare da an huta ba, to fa irin wannan ce zata riqa faruwa, don jiki ba inji bane. Shi ya sa a qa’ida babu wasan da yake kaiwa awa guda ba tare da an samu an huta na dan wani tsawon lokaci ba. Wannan ce kuma kan sa wasu samari shan kayan maye da sunan wai qarin kuzari. Duk abinda aka sha in dai ba sinadarin suga bane a ciki to vata lokaci kawai aka yi.

 

A lokuta da dama akan samu masu irin wannan motsa jiki da ya wuce misali a ga haka kawai sun yanke jiki sun fadi saboda qarewar kuzari. A da dai mun san a filin wasanni musamman a makarantu malaman koyar da motsa jiki sukan qunshe sinadaran magunguna da dama a jakunkunan kar-ta-kwana wato first-aid kit. Akan qunshe kamar sinadarin Glucose-D wato bulkodi da liniment da maganin wanke ciwo da plaster da auduga da sauransu, amma bamu sani ba ko har yanzu ana ajiye irin wadannan a filayen wasanni. Haka nan a yanzu mutum zai ga samari wadanda basu da cikakkiyar qoshi a ido sun zage suna ta qwallo fiye da awa ba hutawa, masu qosasshiyar lafiya kuma sun taru a gefe suna kallonsu! Wato dai kusan ba waxanda ya kamata su motsa jikin ne ma suke motsawa ba.

 

Sai dai ita wannan matsala ta tsamin jiki bata buqatar wani magani illa dan hutun kwana daya zuwa biyu. Wato ba wani magani da aka sani da zai narkar da wannan acid idan ya riga ya taru sai dai kawai mutum ya xan huta na kwana biyu kuma ya riqa wanka da ruwan dimi mai dan zafi sosai da sawa a danna masa wurin, wato tausa, har abin ya baje. Idan mutum yana irin wadannan wasanni na wuce misali ko yana aikin dako, zai iya sayen kayan qara kuzari kamar bulkodi ko lukuzed ko xan wani lemon kwalba (don dukansu dai suga ne cikinsu mai saurin bin jiki) ya dan sha kadan tsakanin hutun rabin lokaci don kiyaye aukuwar tsamin jiki.

 

 

 

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s