MATSALAR TSAMIN JIKI 2

Shafa man kanshiBari mu duba daya ma’anar ta tsamin jiki, wato irin dan qari-qari ko bashi-bashin da hanci kan ji, wanda jikin kowane dan Adam kan fitar a yau da kullum. Jikin kowace irin halitta na sakin sinadarai a qarqashin fata masu qamshi ko wari, dangane da yadda hancinmu ya sarrafa abin. Don haka dan Adam ma ba a bar shi a baya ba. Wasu ma sukan yi kuskuren kiran mutane wadanda tasu matsalar tayi yawa da sunan masu warin qashi. A’a wannan matsala daga cikin fata ne ba a qashi ba.

A tsakanin ‘yan Adam din ma kowane irin jinsi na mutanen duniya akwai irin tashin da jikinsu kan yi wanda hanci zai ji a matsayin qamshi ko wari, dangane da sabon da ya yiwa shi qamshin ko warin. Na baqaqen mutane dabam, na Turawa dabam, na Larabawa dabam, na ‘Yan Asiya ma dabam, dangane da bambancin sinadaran halittu na gado, da yanayi na yau da kullum kamar sanyi ko zafi, da bambancin abinci. A ‘yan kwanakin nan ne muke karantawa a jaridu cewa wai wasu ‘yan qasar Malesiya suna toshe hancinsu idan suka ga baqaqen mutane, kamar daliban qasar nan da ke karatu a can, wai don kada su ji warinsu. Basu san suma da nasu irin warin jikin ba, wataqil kawai suna danneshi ne, ko kuma ana musu kara ba a toshe hanci.

Banda wannan tsami na yau da kullum kuma akwai warin jiki iri-iri da kan yi nuni da cutuka daban-daban ko nuni da irin abincin da mutum ke ci ko sha. Misali, mai ciwon suga wanda suga yayi yawa a jikinsa sosai jikinsa yana fitar da wani dan qamshi kamar na alewa, mai ciwon qoda ma nasa dabam, mai ciwon hanta ma haka, mai gyambo nasa dabam, mai ciwon daji ma nasa qarin dabam. Kai kusan ma a aikin likita akan iya hasashen ciwon da mutum ke dauke da shi ta hanyar qamshin jikinsa. Amma dai ya kamata a san cewa ba kowane ciwone na jikin dan Adam ke fitar da sinadarai masu tashi ba.

Haka nan a bangaren abinci da sha, mutane masu yawan cin irinsu tafarnuwa ko masu yawan shan barasa ko zuqar sigari da masu shan magunguna barkatai wato ‘yan qwaya duk basa buya a cikin taro.

A qarqashin kowace irin fata akwai halittu masu samar da gumi ko zufa. Wadannan halittu banda sarrafa gumi suna kuma fitar da wasu sinadarai na acid wadanda jiki yake fitarwa ta kafar fata (tunda banda kafar hanci da baki da mafitsara da ta bayan gida, jiki kan fitar da abinda baya buqata kuma ta kafar fatar jiki). Wadannan sinadarai ana kiransu fatty acids, kuma iri-iri ne. Sa’annan kuma a jikin fatar kowane dan Adam akwai qwayoyin bacteria da suka maida fata wurin zamansu amma basa sa wata cuta (normal flora). Wadannan qwayoyi suna iya amfani da wadannan sinadaran acid na cikin zufa, su sarrafa shi ya zama wari. Yawan wadannan qwayoyi da zufa, yawan warin jiki. Sinadaran sukan kuma maqale a tufafi ma, tufafi su riqa bashi. Kusan warin jiki na nuni da tsabtar mutum. Yawan tsabtarsa yawan qamshinsa, yawan qazantarsa yawan warinsa. Zafin rana da yanayin wurin aiki ko sana’a suna iya ta’azzara matsalar, domin a qasashe da ake sanyi sosai, inda mutane basu cika zufa sosai ba, abin da dan sauqi. Ga irin mutanen da ko sun tsabtace jikinsu kuma ta hanyar wanka da sabulu mai qamshi haxe da shafa mai mai qamshi basa daina tsami, akwai ‘yan dabaru da akan yi don rage haka.

Banda yawan aske wuraren da suma take saurin taruwa, akwai turare iri-iri na fesawa da na shafawa a fatar jiki (deodorant) don rage irin wannan matsala. Ya kamata mu san cewa turaren fata daban yake da turaren fesawa a tufafinmu, wanda shi Mallam Bahaushe ya fi sani. Su turare irin wadannan an sarrafasu ne don kada su kawowa fata wata illa. Sune aka zuba a irinsu body spray, da roll-on da cikin hoda. Qwarai kuwa har da hoda. Hoda itace ma tafi sauqin kudi a cikinsu, wadda kowa zai iya saya ya riqa shafawa a kullum. Ga masu yawan zufa a qafa ma ko a tafin hannu, duk hoda takan iya tsaneshi cikin sauqi. idan a qafa ne safa takan tsane gumin ta hana warin takalmi.

Su wadannan kayan shafe-shafe kenan an fi shafasu a inda jiki ya fi saurin gumi kamar hammata da matse-matsin cinyoyi da sauransu. Shi kuma turaren perfume shine na fesawa a tufafi. Banda wadannan na zamani, mun san akwai turarruka da dama na gida masu dadin qamshi kuma masu rahusa da mutum zai iya amfani da su a kullum.

Bayan wadannan kuma, yawan sa kayan marmari na itatuwa da ganyaye cikin abinci a kullum yana rage yadda fata takan feso wadannan sinadarai na acid, kuma ko da ma an sarrafa an fitar da sinadaran, wadannan kayan abinci suna da sinadarai wadanda sukan taimaka wajen tsane duk abinda aka feso qarqashin fatar.

Idan kuma mutum duk ya bi irin wadannan dabaru amma ba a daina cewa yana tsami ba, ko bai daina jin warin jikinsa ba, to ya kamata ya samu ya je a binciki lafiyarsa tunda mun ce akwai cutukan da kan nuna alamu ta haka.

 

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s