CUTUKAN FARCE

Yadda fungus ke cin farceAkwai cutuka da dan dama da suke kashe farce, wadansu farcen kawai sukan kama, wasu kuma duk jiki ciwon kan shafa har da faratan, kuma irin wadannan akan ganosu idan aka kalli farcen mutum.

Da farko dai akwai cutukan farce su kansu kamar a irin wadanda su farcensu baya fitowa yayi tsawo waje, sai dai ya fito ya kuma lanqwasa ya shiga fatar qarqashin farcen yayi ta girma a ciki, wanda ake kira ingrowing toenail, wanda hakan kan kawo zafi da radadi da lalacewar farcen.

Sa’annan akwai qwayoyin cuta ba tsutsa ba, da kan iya shiga qarqashin farce su kashe farcen. Irin wadannan akwai na bacteria masu kawo ciwon kakkare, wanda saboda tsananin radadi nan da nan mutum zai nemi magani, akwai kuma na fungus masu kawo nannadewa da bushewar farcen shima ya mutu gaba daya. Da yake irin wannan na biyun ba wani zafi ne dashi ba, har qwayoyin su lahanta farcen mutum ba zai damu ba, wasu ma ba sa sani sai abu ya ci ya cinye, tsawon shekaru. Duka wadannan da zarar an ba da maganin kashe qwayoyin sun mutu, farcen ke ficewa wani sabo ya fito.

Akwai kuma buguwa ta yau da kullum a jikin qofa misali ko da guduma a wurin sana’a wadda kan sa datse jinin shi farcen. Shima saboda zafi nan da nan mutum ke neman magani, amma saboda zubar jini qarqashin farcen dole dai sai farcen yayi baqi kuma ya mutu, kafin daga bisani wani ya tsuro bayan ‘yan watanni.

Akwai kuma cutukan cikin jiki gaba daya wadanda kan taba lafiyar farce. Rashin isasshen jini a jiki wanda muke kira anaemia da rashin wasu sinadaran bitaman kan iya sa farce ya loba ciki, yayi kamar cokali; Cutukan huhu kamar na tarin fuka da na dajin huhu da na zuciya su kuma kumbura farcen suke, da ma qarshen yatsu gaba-daya. Cutukan borin jini masu qarfi su kuma sukan tsatsaga farcen ne; Sigari kuma kan farcen duhu kamar yadda takan sa fatar wasu duhu.

Wasu nau’in magunguna kamar na kashe ciwon daji sukan lahanta farata. Wasu kayan shafe-shafe da ado kamar lalle da jan farce su kuma sukan ba farcen kala ne kawai ba tare da wani lahani ba. Idan mace na yawan sa irin wadannan dole ta fadawa likita abinda ta shafa idan an zo duba lafiyarta.

Koma dai mene ne ya sa farcen ka lalacewa, da ka je wajen likitan fata ya gani ya san ko mene ne sanadi, kuma zai taimaka da yardar Allah.

Yawan tsabtar faratan kamar yankesu akan lokaci da wankesu, da hana yara yawo ba takalmi, da cin abinci lafiyayyu sukan taimaka wajen rage cutukan farce.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s