TSABTAR HAKORA

TSABTAR HAKORA

Yawancinmu bamu fiya damuwa da tsabtar haqori ba, har da ma bakin gaba daya. Tsabtar haqora tana da muhimmancin gaske domin komai yawan tsabtar bakin mutum da ya ci abinci, ya dan bar bakin tsawon awa guda bai wanke ba, to fa qwayoyin cuta ne zasu taru a ciki, su ci karensu ba babbaka (wato su cinye guntun abincin ciki idan sun gama kuma su fara cin haqora). Kamar misalin yadda idan mutum ya ci abinci da dare bai wanke hannu ba, idan akwai kyankyasai ko wasu qwari a makwancinsa, zai ga suna dumfaro hannun da aka ci abincin da shi. Kai har labarin beran da ya gwagwuyi hannun da ba a wanke ba cikin dare ana samu. To haka ke faruwa a baki.

Sa’annan kuma wannan ruwan dorawa-dorawa da haqora kan yi dattin da qwayoyin cutar kan bari ne. Shima kuma yana sa saurin hujewar haqora da mutuwarsu. Yana kuma iya sa warin baki. A wasu mutanen kuma ba a rasa dan ragowar man ja ko miya a jikin haqoran ba, wasu kuma dama kowa ya sansu da cin goro, wanda shima yakan dafar da haqora idan ba a kula da su sosai. Idan da za a dan kankari dan yalo-yalon dattin kadan a sa a kan madubin gwaji na duba qwayoyin cuta, qwayoyin cutar da za a gani sai sun firgita mutum.

To ya za a shawo kan wannan matsala?
Komai tsabtar mutum, dole ne qwayoyin cuta su taru a bakinsa a kullum, don haka ba yadda zamu rage su sai dole ta hanyar wanke baki yadda ya dace. E, qwarai kuwa rage yawansu kawai zamu iya yi bamu isa mu kawar da su duka ba.

Manya daga cikin kayan goge baki sune burushi da makilin. Mutane da dama sun fi amfani da irin wadannan ababen goge baki na zamani. Sai aswaki. Aswaki yana daya daga cikin kayan goge baki masu amfani, idan an yi amfani da shi yadda ya kamata. Ana lakata man makilin akan burushi ko sa asuwaki a goga a haqora. Banda qwayoyin cuta, shi aswaki yakan iya fitar da dattin nan mai kalar ruwan dorawa da kan taru akan haqora wanda da wuya burushin zamani ya fitar da shi. Likitocin haqori kan iya kankareshi da wani tsinke idan an je wanke baki wurinsu. Na san haka ne saboda ana kankare min duk shekara. Kenan yana da kyau mutum ya riqa ziyartar wadannan ma’aikatan lafiya, da shi da iyalansa, a qalla sau daya a shekara. Sa’annan a sauran ranakun shekara mutum ya rika kula da goge hakora yadda ya kamata.

To ya ake goge hakoran. Wasu da dama ba sa bin ka’idar goge haqoran. Kamata yayi a fara daga gaba a wanko sama zuwa kasa, ba a yi gefe da gefe ba, sai a shiga lungunan baki na dama da hagu a gogo kan haqora shima sama da qasa. Wato na sama a gogo zuwa qasa, na qasa kuma a gogosu zuwa sama. Yin burushi gefe da gefe kan iya cinye dasashi. Bayan an gama da wajen haqori sai a shiga ciki wato bayan haqoran. Daga nan sai a je turamen ciki sama da kasa. Daga qarshe sai harshe. Shima wasu mutane suna goge baki amma sam ba sa dirje harshe, wanda shima matattara ce ta abinci da datti. Idan da safe ne a kurkure baki da ruwa, amma idan da dare ne kada a kurkure, a tofar da kumfar kawai a je a kwanta. Wannan dan ragowar makilin da aka bari a baki, magani ne (saboda sinadarin sodium fluoride) dake hana qwayoyin cuta taba lafiyar hakorin mu idan mun yi barci. A gwada yin haka a gani, washegari idan an tashi za a ji baki wasai.

Mutane da dama kuma suna zaton wanke baki sai an tashi daga barci ne kawai, tunda a lokacin ne ake jin bakin ba dadi. To hasali ma wanke baki da dare kafin kwanciya ya fi amfani fiye da wankewa da safe. Ana kuma so duk bayan cin abinci ko da yaushe ne, a yi sakace, ko a sa igiyar floss a tsakanin haqora a fidda abinci, sannan a wanke bakin ko da ba sa burushi da makilin ba. Za a iya kuma amfani da ruwan kurkure baki na chlorhexidine ko listerine don rage  abinda aka bari a bakin na abinci don kada a samu warin baki.

Banda goro, yawan shan suga da abu mai zaqi yakan sa suga ya maqale a tsakanin haqora, wanda hakan kan jawo qwayoyin cuta. Don haka rage shan zaqi shima zai taimaka qwarai da gaske wajen tsabtar baki.

Ga wadanda ba su da halin amfani da man makilin a kullum, yana da kyau su rika amfani da asiwaki ko garin gawayi wanda aka sa wa dan gishiri wajen goge bakin nasu. Idan duk aka bi wadannan qa’idoji in Allah ya yarda haqora zasu riqa sheqi.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s