KIRKIRE-KIRKIREN ZAMANI A FANNIN KIWON LAFIYA

Daga  science photos library
Daga Taskar Science Photos

Mutane masu matsalolin rashin lafiya da dama irinsu ciwon suga da hawan jini da asma da sikila da sauran ire-irensu waxanda kusan a likitance mukan ce musu mutu-ka-raba, zuwa yanzu ya kamata su san cewa bibiyar matsalolinsu da da aka fi yi a asibitoci, za a zo lokacin da suma da kansu zasu rika bibiyar kansu-da-kansu a gida. A irin wannan zamani na yanzu wanda kayan kere-kere da sabbin kirkire-kirkire basu bar kowane bangare na rayuwa ba, tuni yanzu mai ciwon suga ya san a qalla na’urar auna sugan jini, ko ma yana da tasa a gida; mai ciwon asma a kalla ya san na’urar auna karfin numfashi, ko ma shima yana da ita a gida; shima mai ciwon hawan jini ya san na’urar auna hawan jini ta tafi-da-gidanka, ko ma a ce shima yana da ita, da sauran dai ire-iren masu wadannan matsaloli.

Dole ne kowane mai matsala ta rashin lafiya mai bukatar yawan bibiya a asibiti ya tambayi likitansa ko majinyaciyarsa irin na’urorin da ya kamata ya nema domin bibiyar lafiyarsa a gida kafin ranar komawa asibiti ta yi. Bayan an fada masa ya same su, dole ne kuma ya nemi a yi masa bayani yadda ake amfani da su. Wannan ba karamar ragewa maras lafiya matsalar zarya zuwa asibiti zata yi ba, da matsalar zulumin halin lafiya da mai matsalar lafiya ke shiga idan dan wani abu kadan ya faru ga lafiyarsa kafin ranar komawa ganin likita ta zagayo. Haka nan irin wadannan dabaru za su iya rage cinkoso sosai a asibitocinmu.

Haka nan a bangaren mu masu ba da kula da marasa lafiya tuni mun san sababbin kirkire-kirkire irin na zamani da zasu sawwaka mana aiki wadanda kasashe masu arziki tuni suka fara amfani da su. Wannan ba wai ana maganar ma kayan aiki irin na gwaje-gwaje ba, wanda har yanzu suke sa wasu cikinmu tura marasa lafiya kasashen waje, ana maganar na’urori waxanda za su ajiye bayanai akan duk wasu masu zuwa asibiti akai-akai ba tare da fargabar batan fayil ba. Banda matsalar batan fayil, irin wadannan na’urori kan taimakawa ma’aikatan lafiya sanin ranakun zuwan wane da wance domin su basu takamaiman lokacin ganin likita a wannan ranar, ba sai mutum ya zo da asubahin fari ya yini a asibiti ba, wasu ma don kawai a sabunta masa magani. Akan sa ire-iren waxannan manhajoji a na’urar kwafuta wadanda kan tattara bayanan mutanen da zasu ga likita a wannan rana ta hanyar saqonni akan shafin farko da an kunna na’urar.

To ire-iren waxannan abubuwan qirqire-qirqire alfanunsu kenan ba kawai ga maras lafiya bane, har ma da masu jinyarsu. Duk da tafiyar hawainiya da harkar lafiyar kasashenmu ke fama da su, za a zo nan gaba waxannan manhajoji na zamani su kasance sune kawai abin amfani ko an ki ko an so, kamar yadda wayoyin tafi-da-gidanka suka zama wajibi a aljihun kowane mutum a yanzu.

Wadannan misalai da muka yi bayaninsu a sama kusan tsoffin kirkire-kirkire ne ma a wasu qasashe domin suna amfani da su fiye da shekaru goma da suka wuce. Bari mu duba wasu sabbin kirkire-kirkire da wasunsu ma ba su ma shigo gari ba tukuna:

Ga daidaikun mutane yawanci manhajojin kiwon lafiya a yanzu a manyan wayoyin tafi-da-gidanka ake sa su. A yanzu akwai manhajoji da mutum zai iya lodawa wayarsa wadda zai iya amfani da ita wajen motsa jiki, ta gaya masa tsawon kilo nawa ya ci yana tafiya ko sassarfa ko gudu (irinsu manhajar runstactic pro); akwai manhajojin da za su iya auna bugun zuciya (irinsu manhajar instant heart rate), akwai waxanda za su iya auna hawan jini idan mutum ya sayo kuma ya daura robar da ake jonawa wayar salula; akwai masu auna nauyin jiki; akwai masu auna xumin jiki; akwai masu auna bugun zuciyar jarirai na ciki idan mai juna biyu ta kara su a ciki; akwai mai kintatar ranar haihuwar mai juna biyun, da dai sauran ire-irensu da dama wadanda idan mutum ya samu ya bincika wayarsa in dai mai manhajar android ko ios ko blackberry os ce, ba zai rasa na zaba ba na kyauta, sa’annan akwai kuma na kudi.

Akwai kuma wadansu na’urori wadanda ba a waya suke ba sai an saya, wadanda suka dade kamar irin biron da ake amfani da shi wajen allurar insulin, insulin pen a maimakon allura maimakon allura mai zafi a masu ciwon suga . Har ila yau a bangaren allura a sabbin kirkira ana nan ana kirkiro yadda magungunan riga-kafi ba dole sai ta allura za a iya shigar da su jiki ba, wasu da yawa za kera na digon baki kamar na shan inna. Sauran na’urorin da aka kirkiro sun hada da irin karafunan da suke aika saqonni zuwa qwaqwalwa domin bawa gurgu da maras hannu ikon motsa sabbin hannayen da aka sa musu. Kai a kwana-kwana nan ma har tubarau mai sa wasu nau’in makafi gani aka kaddamar.

Ga masu aikin lafiya kuma misalan sabbin kirkire-kirkire da aka yi dominmu na lodawa a waya sune na duba bayan ido irinsu iExaminer, da cikin kunne irinsu cellscope oto waxanda ba a samu a wasu asibitocin, ko kuma ga masu son duba maras lafiya a gida ko daji inda ba kayan aiki.

Ga asibitoci ana nan ana kirkiro wata na’ura kuma ga dakunan binciken jini wadanda za su iya gwada sinadarai da dama a jikin mutum da digon jini daya kawai, ba sai an ta zukar jini a kwalabe biyu ko uku ba, abinda wasu marasa lafiya basu cika so ba. Har ila yau a bangaren binciken cututtuka, a yanzu za a iya gane masu dauke da cutukan daji ta hanyar amfani da wasu karnuka da aka horas, ta hanyar sansana jikin mutum kawai, kamar yadda akan horas da karnuka su sansano miyagun kwayoyin magunguna a filayen jirgin sama.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s