HANYOYIN KARIYA DAGA ILLOLIN CIWON SUGA GA MASU MATSALAR

Diabetic FootA wannan shafi tuni mun riga mun ga hanyoyin da ake bi wajen kare kai daga kamuwa da ciwon suga, wanda muka ce kiba ce ta fi kawo shi fiye da gado. Ga wadanda kuma aka jarrabesu da wannan matsala, bayan addu’o’i neman sauki da shan magunguna, ba haka kawai kuma za a zauna ba, akwai ‘yan dabaru a likitance da ake yi wajen rage illar da ciwon ke sawa a jiki.

Da yake mu a likitance ciwon suga in dai ya kama mutum sai an yi da gaske kafin ya bar shi, (in dai ba irin na mace mai juna biyu ba) dole ne sai ana hadawa da wadannan dabaru idan ba a so matsalar ta yi wa jiki lahani. Mun san cewa ciwon suga na iya yi wa kananan magudanan jini na wasu sassan jiki kamar na idanu, na zuciya, na qoda, na kwakwalwa, na fata da na kafafu illa saboda taruwar suga a cikinsu. Haka nan yakan iya yi wa wasu jijiyoyi na laka ma illa kamar na hanji, na dubura da na kafa.

Mun kuma san cewa shi dai ciwon suga yana faruwa ne yayin da jiki ya kasa samar da sinadarin insulin wanda kan sa jiki ya tsotse sikari ko kuma kiba ta sa wuraren da ake tsotse suga a jiki su ki aiki. Don haka idan babu wannan sinadari ko wurin tsotsewar na da matsala, suga kan taru a jini har ya kawo illa ga wadancan sassa na jiki da aka ambata. Idan suga yayi yawa a jini har buge mutum yake ya suma, haka ma idan yayi kadan, musamman a masu wannan matsala. Wato dole ne kenan sai an saisaita suga tsaka-tsaki. Duk wanda yake da iyaye ko kakanni masu ciwon suga, shima yana da kyau a riqa gwada nasa yawan sugan a kalla sau daya a shekara.

Ga masu ciwon kuma wadanda aka xora kan shawarwari ko magunguna, dole ne su bi waannan ka’idoji, kuma su riqa shan magani kamar yadda aka zayyana, domin ba makawa idan aka bi waxannan ka’idojin, za a iya rayuwa kusan kamar kowane mai lafiya.

 

Hanyoyin Kariya Daga Wadannan Illoli Sune:

  1. Bin Ka’idar Cin Abinci: Kowane mai ciwon suga dai ya riga ya san dole ya kiyayi abincin da aka sa suga na kasuwa, wato suga na gari, amma zai iya cin abincin wadanda da sugansu aka halicce su kamar kayan marmari. Wasu akan hana su cin wasu abubuwa masu sitaci irinsu doya, amma wasu ba a hana su, wannan ya danganta ne da irin yanayin jikin mutum da irin yadda magani ya karve shi. Akan bukaci su yawaita cin wake da acca da kayan ganye, da burodin alkama da sauransu, saboda su ba su da yawan suga. Duk dai abincin da aka dora mutum akai dole ya kiyaye. Hasali ma masu ciwon da yawa akan fara basu wannan ka’ida a karon farko kafin a je maganar magani. Idan suka kiyaye wannan yawanci ba sai an je ga shan magani ba.
  2. Yana da kyau mai ciwon suga ya sayi na’urar gwada sukari ta ‘glucometer’ wadda za a iya samu a manyan kyamis, sa’annan ya je a koya masa yadda ake amfani da ita, ya rika auna sugan da kansa a gida a kalla sau daya a sati idan mai amfani da magani ne. Idan kuma shi mai amfani da allurar insuli ne kusan yana wajaba a riqa aunawa a kalla sau daya a rana. Amfanin wannan shine bibiyar sugan jini domin kare duk sassan jiki daga illa, da kuma kiyaye aukuwar irin yawan suman da wasu masu ciwon suga kan yi a gida, walau idan suga yayi yawa a jini, ko kuma idan yayi qasa sosai
  1. Ga lafiyar koda, akwai wata na’ura ma har ila yau ta auna sugan da ke cikin fitsari urine dipstick wadda ita tsinke ne kawai ake dangwalawa a cikin fitsari a ga yadda zai canza kala. Suma akwai ire-irensu masu sauqi a manyan kyamis hade da robar fitsarin (tunda sai dole a roba mai tsabta ake zuba fitsarin, kuma sai zubar fitsari ta tsakiya ake tara a robar, ba na farko ba, ba na karshe ba). Amfanin wannan itace kare koda daga illar suga. Da yake mun ce koda na daya daga cikin manyan sassan jiki da ba sa son suga, da mutum ya ga alamun suga a fitsari ta hanyar wannan tsinke, sai ya garzaya asibiti a saisaita masa maganinsa, domin kuwa alama ce ta cewa suga ya fara zama a qoda. Banda wannan na gida a asibiti ma akan auna sinadarai da kan iya nuna lafiyar koda duk lokacin da mutum ya je sabunta magani
  2. Ga kiyaye lafiyar ido kuma, kamata yayi a kalla duk shekara a auna lafiyar idanun mai ciwon suga a asibiti ko da sau daya ne. Shi wannan ba wata na’ura mutum zai saya ba, a’a ko yana jin alamun matsalar gani dusu-dusu ko bashi da ita, ya kamata a ce a asibitin da mutum ke zuwa akwai vangaren ido, domin likitan sugan ya aika shi a auna idon a kalla sau daya a shekara. Idan kuma babu to dole sai ya nemi asibitin ido. Wannan zai yi matuqar kare ido daga illar yanar ido ta sukari (cataract) da kuma illar da sugan kan yi a can bayan kwayar idon (retinopathy). Idan aka ga alamar matsala da wuri an fi iya maganceta fiye da idan aka gano a kurarren lokaci, wanda hakan kan iya jawo makanta.
  3. Game da lafiyar kafa kuma, dole ne mai ciwon suga ya riqa duba kafarsa kusan duk safiya lokacin wanka, ya duba kumburi, ko canjin kala, ko wani kwarzane ko faso, ya latsa ya ji ko akwai inda ba ya jin tavi, ko akwai wuri mai zogi, domin da yawan abubuwan da ke fara shafar lafiyar qafar mai ciwon ba zafi ne ko raxaxi ake ji ba. A wasu lokutan dai akan ji raxaxin kamar na qunar wuta a tafin qafa, ko na tafiyar kiyashi, waxannan alamu ne na farko-farko ga mai ciwon suga cewa suga fa yana tava jijiyoyin laka na qafa. Idan wannan ya daina suga bai sauka yadda ya kamata ba, to sauran duk abubuwan da zasu fari ga qafar da wuya mutum ya ji alamun ciwo. A qasashen da suka ci gaba a asibitoci akwai sashen duba lafiyar kafa na musamman (podiatry), wanda har yanzu bai zo qasashenmu ba tukuna. Duk dai wata alama da mai ciwon suga ya ji a qafarsa ya kamata ya sanar da likitansa cikin gaggawa kada a je lokacin da za a ce sai an yanke yatsu ko qafa
  4. Hanyoyin kare magudanan jini na zuciya da na qwaqwalwa daga illar suga duk xaya ne da hanyoyin kare su daga maiqo waxanda muka sha zayyanawa a wannan shafi.

 

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s