Hanyoyin Kariya Daga Illolin Yanayin Sanyi

A bana sai ga shi sanyi ya zo da karfin gaske a garuruwan arewacin kasar nan, ta yadda idan ba a yi tanadi ba, na barguna da kayan sanyi da kayan jin dimi, to zai iya illa. A cikinmu ‘yan Adam akwai mutane da suka fi son yanayi na sanyi, akwai kuma wadanda suka fi son yanayi na zafi, dangane da yadda jiki ke karvar canjin yanayin.  Haka ma a cikin halittu na kwayoyin cuta, akwai wadanda suka fi rayuwa a yanayi na sanyi, akwai kuma wadanda suka fi rayuwa a yanayi na zafi, akwai kuma wadanda suka fi son danshi. Misali, kwayoyin cuta na virus sun fi son yanayi na sanyi, amma na fungus sun fi son yanayin ruwa da danshi. Na bacteria kuma da dama sun fi yawa lokacin zafi.

  1. Ga wasu daga cikin matsalolin da kwayoyin cuta kan kawo lokutan sanyi:

Mura: Kwayoyin cutar da kan sa mura duka na virus ne, wadanda suka fi yawa a wannan yanayi. Suna bin iska ne mu shakesu ta hanyar kafofin numfashi. Wasu masanan kuma sun ce a’a wadannan kwayoyin suna nan a kowane lokaci amma sun fi samun karfi a lokacin sanyi. Saboda kusancin da muke da juna, da kukkule tagogi da muke, hakan kan sa mu rika yadawa juna.

Alamomin murar sun hada da zazzabi da ciwon kai, amma ba sa tsanani irin na maleriya.  Abinda ya fi bambanta su shine yoyon hanci ko cushewar hanci.

Hanyoyin da za’a bi a kare kai daga kamuwa da mura sun hada da yin nesa-nesa da mai mura. Idan kuma ta kama mutum, zai fi kyau ya bar shiga mutane na tsawon kwanaki biyu ko uku. In ya zama dole ya fita, ya rika yawan amfani da hankici ko hannun riga ya rufe fuska yayin atishawa don kada ya yadawa wasu. Sai kuma yawan wanke hannaye da ruwa da sabulu don rage kwayoyin cutar da sukan hau hannayen yayin share hancin. Mai mura ya rika yawan shan ruwa da shan abu mai yaji kamar farfesu, ko shayi mai citta ko shakar robb don kwayoyin cutar kamar basa son yaji, kuma ruwan romon da shayin kan dumama jiki.

A qasashen da suka fi mu sanyi kuma akwai allurar riga-kafin kamuwa da murar kwayar cutar virus nau’in influenza ko flu a takaice, wadda take kashe musu mutane da dama a duk shekara, musamman kananan yara da tsofaffi. Ga wadanda za su je irin wadannan kasashe a cikin irin wannan yanayi yana da kyau komin shekarunsu su karbi wannan allurar riga-kafin kafin su tafi, ko kuma da zarar sun sauka can.

Tari: Kamar mura, lokacin sanyi akan yi tari, musamman na ciwon hakarkari, wato numoniya, idan kwayoyin cuta sun fara gangarawa daga hanci zuwa makoshi da huhu kenan. Wani tari da ya fi kamari a irin wannan lokaci shine na yara ‘yan kasa da shekara biyar, da ake kira croup a likitance, saboda numfashin mai murar kan yi ta ‘kurup-kurup’ kamar na mai asma ko tarin shika,  wasu kuma kana ana hura usur, saboda maqogwaron ya kumbura. Sukan kasa cin abinci sosai. Wani lokaci hakarkari na shigewa ciki idan suna jan numfashin. Idan aka ga irin wannan, dole a kai yaro asibiti domin karbar magani da iskar oxygen, domin a wasu lokuta sai an kai ga saka musu wannan iska da magungunan shaka ta bututun iskar. Yana xaya daga cikin cutukan da ke galabaitar da yara, yayi sanadin rasuwar wasu.

Hanyoyin kariya basu wuce irin na mura ba, a rika sawa yara kayan sanyi masu aminci a kuma rika ajiyesu daki mai dumi, da kuma daina yawo da su tsakar gida lokacin sanyi.

Mura

A. Dangane da yadda jiki ke karbar canjin yanayi kuma, jikin wasu kan samu kansa a yanayi na:

Sabar fata/Bushewar Fata/Kaushi/Faso: Wasu fatarsu ta sama ke fita wata ta fito, kamar dai yadda wasu halittu suke yin saba. Wannan ba ciwo bane, yanayi ne da fata kan bi domin ta gyara kanta. Wasu kuma fatar tasu takan bushe sosai. Wasu kan samu bushewar a fuska wanda ake kira waskane. Bushewar fata ta fi kamari a kafafuwa inda akan samu kaushi da faso, a wasu lokutan ma fason ya zama ciwo. Yawan sa safar qafa mai qwari da takalma sau ciki idan za a fita, da yawan dumama kafafu a ruwan dimi da shafa man basilin sukan taimakawa mai busasshiyar fata wuce sanyi lafiya kalau

Yawan fitsari/Taurin Bayan Gida:  Shima yawan fitsari a irin wannan yanayi hanya ce da jiki ke samu domin fitar da ruwan da baya bukata a wannan lokaci. Wato in dai ba dama can mutum yana da yawan fitsari ba a lokacin zafi, to kusan yawan fitsari lokacin sanyi alama ce ta lafiyar koda. Amma kuma duk da haka ana so mutum ya ci gaba da shan ruwansa daidai wa daida, domin hakan kan taimakawa ciki da hanji narkar da abinci. Domin ba abin mamaki bane mutum ya ji ya fara samun taurin bayan gida a lokacin sanyi, idan baya shan ruwa sosai.

B. A wasu lokutan kuma wasu cutukan sun fi tashi a wannan yanayi, misali:

Asma: A irin wannan yanayi na sanyi aka fi samun mutane masu matsalar asma, kuma a irin wannan yanayi ciwon ya fi tashi ga masu ita, saboda kurar hazo. Mai asma dole ya rika sa kyalle ko takunkumi mai rufe fuska kenan a ranakun da ake hazo, kuma ya rika yawo da maganinsa na rage illar asma kamar inhaler.

Ciwon hakori: A mafi yawan lokaci mataccen hakori baya tashi ciwo sai a lokacin sanyi, ko kuma idan an sha ruwa mai sanyi. Ba sanyin ne ke jawo ciwon hakorin ba, a’a dama can kwayar cutar musaman na bacteria ta ci, ta cinye, har jijiyar karkashin hakorin ta fito. To da sanyi ya tavo wannan jijiya sai fa haqorin ya fara zogi.  A nan zuwa asibitin hakori domin cike ramin, ko ma a cire shi gaba-daya idan an ga bashi da mamora shine kawai mafita.

Bugun zuciya: Masu ciwon zuciya iri dabam-daban sun fi samun matsaloli a irin wannan yanayi domin ciwon kirji na masu ciwon zuciya da kuma bugawar zuciyar ya fi aukuwa. Wannan na faruwa ne musamman a tsofaffi wadanda jikinsu baya samar da dumi sosai, don haka jininsu kan fara daskarewa har zuciya ta tavu. Wato dai dole ne tsofaffi da masu ciwon zuciya su kasance a wuri mai dumi a irin wannan yanayi. Idan ta kama dole a fita kuma dole a yiwa sanyin shiri ta hanyar rufe ko’ina a jiki da kaya masu kauri.

Sai kiyaye irin abubuwan da ake kunnawa na jin dimi a dakuna. Hayakin itace da na makamashin kwal suna dauke da gubar carbon monoxide mai iya kisa cikin dare musamman idan tagogi a rufe suke. Wutar gawayi bata fiya hayaki ba sosai, za a iya amfani da ita. Idan aka hura gawayi a waje ya kama, sai hayakin ya lafa kafin a shigo da shi daki. A kuma kiyaye kada a sa wurin da zai iya kama wuta. Ga masu wutar lantarki, heater itace tafi.

Mu tuna da ‘yan uwa ‘yan gudun hijira wajen taimakawa da tantuna masu kwari da kayan sanyi da barguna da magunguna, a kungiyance don kaiwa sansanoninsu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s