MAKARANTUN FIRAMARE: TUBALIN GINA LAFIYAR YARA

SHPA da akan dauki lafiyar yara a kananan makarantunmu, musamman ma na gwamanatoci da muhimmanci sosai. Amma a yanzu saboda tabarbarewar al’amura ’yan makarantun hukuma idan aka gan su ko sha’awarsu ba a yi, ta wajen tsabtar jiki da ta kayan sa wa, balle a zo ga maganar makarantun allo. Wannan na nuni da irin yadda shi kansa ilmin ya tabarbare, domin a ka’ida an gina kananan makarantun firamare ba don ilmi kawai ba har da kulawa da mu’amala da tsabtar dalibai.

A yau mun lalubo manyan tubalai na kiwon lafiyar ’yan makarantar firamare domin tunatar da mu da malamai da hukumomin da abin ya shafa. A cikin tubalan abu daya ne ko biyu kawai muke jin labarin ana samarwa yara ’yan makaranta, shi ma don dawowar siyasa. Wannan kuwa shi ne ciyarwa lokacin ‘tara.’ Makarantu da dama a yanzu a wasu manya birane na Arewacin kasar nan an dawo da ciyar da dalibai abinci. Abin da dai kawai ba mu sani ba shi ne ko masu tsabta da gina jiki sosai ake bayarwa.

Tubalin gini na biyu shi ne samar da ilmi a kan kiwon lafiya, wanda wannan ma akwai shi. Sai kuma samar da wuraren motsa jikin. Wauraren motsa jiki a makarantunmu filaye ne kawai ba kayan wasa. Wato fili ne kawai aka ware kato guda, ba a raba an zana taswirar bangaren kowane irin wasa ba. Sai tubalin bin diddingin tsabtar kowane dan makaranta ta jiki da ta kayan sa wa, wanda da ake yi duk sati akalla sau daya a makarantun firamare. Wannan ya hada da duba tsaftar farce ko kumba, duba baki, duba tsabtar tufafi da takalma. A da duk yaron da bai cika tsabtar jikinsa ba kora shi gida ake kada ya yada wa yara cututtuka. Har yanzu a wasu kasashe sai an nuna shaidar allurar riga-kafi ma kafin ba a yara gurbin karatu, don gudun irin haka, amma a kasar nan an daina.
Wani tubali da za a ce kusan yanzu babu shi kwata-kwata a makarantun firamare shi ne dakin shan magani na sha-ka-tafi, wanda ake ajiye wa ma’aikacin lafiya sukutum. Ba makarantun firamare ba, kai har sakandare a yanzu da wuya a samu wannan.
Mun san akan samu bandakunan zagayawa, amma sam mun sani a yanzu da su gara babu su. Tun a hanyar shigar su mutane suke kicibis da kazanta.

Duk binciken da masana ke gudanarwa a kan harkar lafiyar ’yan makaranta a ’yan shekarun nan a kasar nan ba su yi nuni da ci gaba mai kyau ba a harkar kiwon lafiyar makarantu. Binciken ya hada kuma har da makarantu na kudi, inda sai dai a ce gara su da na gwamnati, amma duk tafiyar daya ce. Da fatan masu ruwa-da-tsaki za su gyara lamarin.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s