Magungunan Da Ke Karya Azumi

medical ampoules and syringe
Kwalbar Allura  

Mallamai na addini da na kimiyya kamar likitoci da masu hada magunguna, sun sha zama akan wannan batu a kasashen musulmai irinsu Saudiya da Masar da sauransu, domin samun mafita a game da amfani da magunguna lokacin azumi. Ban sani ba ko a kasashen musulmai Hausawa ana irin wannan zama.

Ga abubuwan da na binciko daga wadancan Mallamai game da wannan batu: Wadanda suka hadu suka fitar da hukunci akan wannan batu suka ce, magunguna a lokacin azumi idan ya zama dole a yi amfani da su, hukuncinsu yana kasuwa kashi biyu ne, da masu shiga ciki kai tsaye da masu aiki a wasu wurare ba sai sun shiga ciki ba.

Su magungunan da ake hadiya kai tsaye su shiga ciki wadannan kowa ya san za su karya azumi, sai dai a ajiye azumi a sha su, musamman idan ciwo na cin mutum, ko kuma su a ajiyesu a ci gaba da azumi, musamman idan ba su wuce sha sau biyu a rana ba. Wato idan ciwon mai sauki ne, kuma shan maganin bai wuce sau biyu a rana ba, ka ga a kaikaice za a iya sha lokacin shan ruwa da lokacin sahur kenan.

Su kuma magunguna masu aiki a wasu wurare ba sai sun shiga cikin uwar hanji ba su ne:

  1. Magungunan da ake shaka masu bin hanyar iska: Suka ce mutum zai iya amfani da maganin shaka kamar inhaler ta asma ko a shaki oxygen ko wani abin shaka dai na wani ciwo, wadanda ke bin hanyar iska, tunda huhu suke shiga kai tsaye kamar yadda iska da muke shaka ke shigarsa, ba ciki suke tafiya ba. Amma suka ce a lura akwai magungunan shaka masu sa maye wadanda ke tafiya kwakwalwa, wadannan za su karya azumi saboda za su gusar da tunani
  2. Magungunan da ake digawa a ido: Suka ce wadannan ma ba laifi idan aka diga magani a ido idan ana azumi. Wato hakan ba zai karya azumi ba tunda ido ba kafa ce ta cin abinci ko abin sha ba.
  3. Magungunan da ake digawa a kunne: Wannan ma ba zai kai ga karya azumi tunda a cewarsu, da wuya maganin kunne ya gangara ya shiga ciki
  4. Magungunan da ake digawa a hanci: Suka ce wadannan in dai a sigar ruwa maganin ya zo, to kuwa idan aka digashi zai iya kwaranya makoshi daga nan hanci ya tafi makogaro ko ciki, ko an ji shigarsa ko ba a ji ba, don haka zai iya karya azumi
  5. Magungunan da ake shafawa: Su kuma suka ce ba za su iya karya azumi ba tunda akan shafa sabulu da man shafawa ko na goge baki lokacin azumi, kuma duk yawanci iyakacinsu wajen jiki.
  6. Magungunan yin dauke wato wadanda ake tusawa ta dubura: Irin magungunan da ake cewa suppository, kamar masu rage zogi da rage zazzabi ko rage kumburin basur, su ma sun ce ba za su karya azumi ba
  7. Magungunan da ake sa wa a karkashin harshe har su narke su bi jijiyoyin jini ba tare da an hadiye ba (sublingual), kamar magungunan hawan jini da na ciwon zuciya, irinsu Nifedifine da Glycerine Trinitrate suka ce ba sa karya azumi. Amma idan hadiyesu aka yi za su karya tunda ana iya hadiyesu
  8. Allurai wadanda ba sa iya kara kuzari, kuma ba da wani abin karin kuzari aka yi su ba, (wato babu sinadarin glucose ko makamancinsu a ciki) irinsu alluran karkashin fata kamar ta masu ciwon suga – duk da dai masana ciwon suga suna ganin mai amfani da allurar insulin ba magunguna ba, ya fi kyau ya ajiye azumi – ko allura ta cikin tsoka kamar ta mai zazzabin maleriya, duk ba sa karya azumi. Wato masanan sun raja’a akan allura ta tsoka ko ta karkashin fata ba ta karya azumi
  9. Allurai wadanda ake yi a cikin jijiyar jini kai tsaye (arteries and veins) ko jijiyar laka ta gadon baya (epidural) idan na ruwan magani ne kawai babu sinadaran abinci a cikinsu kamar allurar hydrocortisone, suka ce ba sa karya azumi. Amma allurai na karin sinadaran jiki kamar allura mai sodium (irinsu diclofenac sodium) da mai sinadaran calcium (calcium gluconate) ko potassium (potassium chloride) komi kankantarsu, za su iya karya azumi, yawanci an fi so in za a yi su  ko idan an yi su a hakura da azumi, domin za su iya karya shi
  10. Karin ruwa ta jijiya wannan kai tsaye zai karya azumi. Ruwa na glucose ko na normal saline ko na dextrose saline ko na ringers lactate duka, saboda duk ruwa da abinci ne. Kai har ma wadanda ba sinadarin abinci a cikinsu amma ruwa ne ya fi yawa kamar su mannitol za su iya karya azumi

Domin karin bayani za ku iya tuntubar malamai na addini da ke kusa ko kuma a binciki littattafan Mallaman musulunci wadanda suka yi rubutu kan wannan maudu’i, kamar Sheikh Saleh Ibn Uthaymeen. Yana daya daga cikin Mallamai wadanda suka yi dogon bayani da rubutu akan azumi da magunguna, kamar a Fataawaa ‘Ulamaa’ al-Balad al-Haram ko kuma a duba https://www.islamicboard.com/worship-in-islam/134321255-ruling-taking-inhaler-fast.html.

One thought on “Magungunan Da Ke Karya Azumi

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s