YADDA ZA A SHAWO KAN MATSALAR SHIRIN KAWAR DA SHAN INNA

Digon Bakin PolioA hakikanin gaskiya tun lokacin da mutanen arewacin kasar nan, da ma takwarorinsu na kasashen irinsu Afghanistan da Pakistan, suka ji kishin-kishin wai ana hada allurar riga-kafin polio da maganin kayyade iyali, da dama daga cikinsu suka daina rakiyar shirin, wasu suka karaya, suka hakikance cewa wannan allura ba alkhairi bace ga ‘ya’yansu. Da ma can a irin wadannan kasashe wasu kan yiwa duk wani abu da ya zo daga kasashen yamma muguwar fassara, ballantana a ce an ba da shi kyauta. Duk da haka kuma masu irin wannan zargi, ko suna da gaskiya, ko basu da ita, watakila sun kwana da sanin cewa yawanci magungunan kyauta na asibitocinmu irinsu maganin warkar da tarin TB da na rage kaifin ciwon kanjamau, kai har ma da wasu na warkar da zazzabin cizon sauro da akan bayar kyauta, duk daga kasashen yamman suke, kuma suna daga cikin masu karbarsu idan matsala ta tashi. Tambayar da kan fito a bakin masana itace to su wadannan ya aka yi suka san ba a gurbata su ba?

Wani abin dubawa game da alluran riga-kafi a duniya ma baki daya shine cewa ba a kan irin wadancan kasashe ne kawai aka taba yi wa allurai bore ba. A’a a kasar Ingila alal misali akwai lokacin da iyaye da dama suka hana a yi wa ‘ya’yansu allurar bakon-dauro domin ana zargin a wancan lokacin tana sawa yara nakasa a kwakwalwa. Daga baya aka zo da kyar aka ganar da su. Kai a yanzu haka a kasar Amurka akwai wadanda ba sa ba da yaransu a musu wannan allura ta kariya daga ciwon bakon-dauron wai domin ‘zuciyarsu bata yarda da ita ba’. Wannan bore yana nan yana nema ya jawo annobar ciwon bakon-dauro a wasu garuruwa na kasar Amurkan.

Har yanzu Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO ta kasa shawo kan wannan matsala ta ciwon shan inna a wadannan kasashe uku da aka lissafa a sama. Tuni lokacin da aka ware domin shawo kan ciwon, ko kawar da shi daga doron kasa, ya wuce da wajen shekaru goma. An kiyasta cewa, tun daga lokacin da aka fara wannan yaki shekaru 25 da suka wuce, zuwa yanzu, kusan an shawo kan yaduwar ciwon da kashi 99%. Kashi 1% ne kawai ya rage, wanda kusan a wadannan kasashe uku yake. Sai kuma a ‘yan kwanakin nan da ake dan jin bullar ciwon a kasashen da ba a zaman lafiya, irinsu Syria da Iraqi da Yaman. Kai har ma Kenya da kasar Gini da suke da ‘yar kwanciyar hankali an samu bullar ciwon a wancan wata da ya wuce, duk da dai hukumomi sun sha alwashin hana yaduwarsu daga wadannan yankuna, akasin a kasashen da ake yake-yake. To abinda dai ake so a nuna a nan shine, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, wannan kashi 1% zai iya zama gagara-badau. Tuni hukumomin lafiya da ke wannan aiki suka kara wa’adin cimma wannan buri zuwa shekaru uku masu zuwa.

To ta yaya za a cimma wannan buri? Duk wani mai son duniya da zama lafiya, da kuma son harkar kiwon lafiya, zai yi matukar murna idan aka ce a zamaninsa an cimma wannan babban tarihi na kawar da ciwon shan inna daga doron kasa. Tuni muka ji labarin yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta kawar da ciwon Agana wajen shekaru talatin da doriya da suka shude, ga shi yanzu an ce ana nan saura kiris a kawar da ciwon kurkunu ma. Za mu so mu sake jin irin wannan labari nan gaba kadan akan shan inna, har ma a zo a sake daukar wani ciwon kamar zazzabin maleriya, shima a ga bayansa.

Babbar matsalar da ke ci wa shirin yaki da wannan ciwo tuwo-a-kwarya shine rashin yarda da alluran. Hukumomin lafiya sukan kawo dalilai da cewa ai wadanda basa yarda kansu bai waye bane sosai, ko kuma ai wuraren da ba a iya zuwa yin alluran ba, wuyar shiga ne da su. A nan suna nufin ko dai rashin hanyoyin sufuri ko dai rashin wurin ajiyar allurai masu sanyi a cikin lungunan. Amma mu dai ma’aikatan lafiya mun san babban dalilin dai shine guda daya tilo na rashin yarda da alluran. Mutane da yawa sun riga sun kyamaci abin. Sai an yi wani abu akan wannan kyama.

Anan ne muke ba wa hukumomin lafiya na qasa-da-qasa waxanda ke wannan aiki a irin kasashen namu, shawarar cewa dole fa a canza dabara. A kwana-kwanan nan wani fitaccen attajiri na kasar Saudiya wato Yarima Alwaleed Bin Talal ya sha alwashin sadaukar da duka dukiyarsa ga aikin taimako. Dama can yana yin taimako iri-iri, kkarawa kawai zai yi. A cikin irin taimakon da ya riga yayi, har da bada kudade wuri-na-gugar-wuri dala miliyan 30 ga bangaren Hukumar Lafiya ta Duniya mai yaki da wannan ciwo. Idan mutum ya duba shafin yanar gizon kungiyar da ya kafa, zai ga batun. Wannan ba kananan kudade bane, amma hakan bata sa shi cikin jerin masu bada taimakon kawar da ciwon na gaba-gaba ba. Wadannan na gaba-gaban sune irinsu attajirin nan na kasar Amurka, wato Bill Gates, wanda da kansa har-ila-yau yake ta shi ya rika yawo a wadannan kasashe yana wa shirin kamfe, yana kuma diga ruwan allurar polio ga yara. Sauran na gaba-gaban sune irinsu Bankin Duniya, kungiyar Rotary da ire-irensu.

A can kasashen gabas ta tsakiyar, banda Yarima Alwaleed, Bankin ci-gaban harkokin addinin Musulunci wato IDB, shima an jero shi a cikin masu ba da kudade akan wannan yunkuri. Haka nan an zayyana cewa a yanzu wannan banki ne ke sa ido a wajen sarrafawa ko hada ruwan alluran a kasar Indonesia, inda daga nan alluran suke zuwa mana yanzu. To wadannan bayanai ne da dama mutanenmu da irin na kasashen can da aka lissafa basu sani ba. Yadda kuwa za a canza abin cikin sauki shine cewa a lallabi shi Yarima da Bankin Islamar su shiga gaba-gaba a wannan yakii, itama hukumar lafiyar ta yarda ta saka su a sahun gaba. Abin nufi a nan, ba wai su kara wasu kudi tsaba a asusun kamfe din ba, a’a. Abinda watakil zai ceto shirin shine, su da jami’ansu a kungiyance, su zama limaman shirin tun daga masana’antun hada wadannan ruwan allurai (inda zasu  ci gaba da tabbatarwa ana bin dokokin da suka kamata wajen hada wadannan allurai) har zuwa diga alluran a wadannan kasashe.  A ga jami’ansu a gaba-gaba maimakon a ga turawa a gaba-gaba. Wannan zai yi matukar wanke wani zargi da shakkun da ke tattare da shirin ga mutanenmu, tunda da wuya su juyawa wani taimako daga kungiyoyin da ke kasashen musulmai baya.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s