AMFANIN MAKEWAYI GA LAFIYA

Public ToiletDuk shekara 19 ga wannan wata ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya da hadin gwiwar wasu kungiyoyin lafiya na duniya suka ware domin nanata amfanin makewayi ko wuraren ba-haya ga lafiyar al’umma.  Taken wannan rana a bana shine ‘baza mu jira ba’, wanda ke nuni da yadda ma’aikatan lafiya ke hakilon ganin wadanda abin ya shafa sun yi hobbasar da ta dace wajen ganin an shawo kan matsalar rashin makewayi a cikin al’umma. Girman matsalar ta kai ga cewa a kasashen da wannan matsala ta rashin bandaki ta yi wa katutu, kusan rabin mazaunan kasashen basa amfani da makewayi.

Amfanin makewayi ga lafiyarmu ba boyayye bane tunda an sha fada ko da a wannan shafi cewa rashin makewayi da kin yin amfani da su, in akwai, ta hanyar yin ba-haya a wurare barkatai a bainar jama’a, na daya daga cikin abubuwan da ke ci wa lafiyarmu tuwo-a-kwarya. Tun daga cuttuka masu saurin kisa irinsu amai da gudawa a kananan yara, zuwa annobar kwalara da zazzabin tafot, zuwa masu nakasa mutane irinsu shan-inna, da masu hana yara girma irinsu cutukan macijin ciki ko tsutsar ciki, duk rashin yin bayan-gida a wuraren da suka dace ne suke janyo su. Don haka kenan idan dai har ba a tashi tsaye ba an yi maganin wannan batu a kasashe irin namu, to tabbas har abada ba za a rabu da wadannan cututtuka ba.

Abubuwan da ke kawo matsalar rashin amfani da bandaki sune karancin ilmin zamani da kuma talauci. Wadannan abubuwa biyu sai sun hadu a lokaci guda suke haifar da matsalar. Wato idan babu daya daga ciki da wuya a samu matsalar. Wadanda suke da abin hannu ko basu da ilmi sukan yi amfani da makewayi, haka ma wadanda suke da ilmin zamani ko da basu da abin hannu sosai suma sukan yi amfani da makewayi. Kazalika, a kasashen da basu da arziki sosai amma ilmin zamani ya wadace su, kamar kasashen gabashin Turai, ba a samun matsalar, haka nan kasashen da ilmin zamani bai ishe su ba, amma suna da dimbin arziki, kamar kasashen Gabas ta Tsakiya masu arzikin man fetur sosai, nan ma ba a samun matsalar. Sai a kasashe inda ake da talauci da rashin ilmin duka a wuri daya kuma a lokaci daya, irinsu Indiya da Bangladesh da Pakistan da kasashen da ke kudu da Sahara irinsu Najeriya da Togo da Ghana sauransu, ake samun matsalar.

A bana ana so a wannan rana a nunawa mutane ne alakar da ke akwai tsakanin rashin makewayi da rashin walwalar yara kanana ta fannin lafiya. Alakar kuwa ita ce, a duk lokacin da yaro ci abinci ko ya sha ruwa mai kwayoyin cuta, wadanda su kuma daga bayan gidan wani ruwa ke wankowa, ko quda ke yadawa, zai kamu ko dai da ciwon gudawa ko na tsutsar ciki. Gudawa nan da nan take karar da ruwan jiki da albarkatu na ma’adinai da sinadarai da yaro ya dan tara a jikinsa, wadanda yake bukata domin dawwama cikin koshin lafiya, ita kuma tsutsar ciki a sannu a sannu take shanyewa yara jini ta jikin hanji, wanda shima jinin ke dauke da duk albarkatun abinci masu gina jiki da yaron ya ci. A haka idan ana samun yawan wannan sai a rika ganin yara ba sa saurin girma, suna kuma yawan laulayi ba koshin lafiya.

To ta yaya za a shawo kan wannan matsala da ta ki ci, ta ki cinyewa? Duba da yadda al’amura suke dada kazancewa musamman idan an yi la’akari da dimbin jama’ar da a yanzu a wani yanki na kasar nan suke sansanonin gudun hijira inda babu isassun wuraren kewayawa, dole a daidaikunmu mu kara zage damtse wajen karin taimako ga sansanonin ‘yan gudun hijira, domin karin abinci da wuraren kewayawa masu inganci. Sa’annan kuma dole ma’aikatan lafiya mu ci gaba da fadakar da jama’a alfanun yin bayan gida da zubar da shi a wuraren da suka dace, (ga masu aikin yasar masai kenan) da muhimmancin wanke hannaye da sabulu bayan an yi bayan-gida.

Bayan wannan, dole ne kuma hukumomi musamman na karamar hukuma da ‘yan majalisu wadanda akan warewa wani kaso domin aiyukan ci-gaba a mazabunsu, su san cewa an daina maganar samar da ruwan sha kawai ta hanyar gina rijiyoyin burtsatse, a yanzu maganar da ake ita ce ta samar da shi ruwan hade da wuraren ba-haya, da wuraren sarrafa shara. Wato dole ne a yanzu a dora wadannan a kan samar da tsabtataccen ruwan sha, domin da ruwa da wadannan bukatu a tare suke tafiya a bangaren ci-gaba. Ana bukatar karin gina wuraren ba-haya a makarantun gwamnati, da kasuwanni, da tashoshin mota da gefen manyan hanyoyin sufuri. Don haka jama’a masu yin zabe ya kamata suma su qara da wadannan a cikin abubuwan more rayuwa da ya kamata wakilansu su yi musu. Kwamishinonin lafiya su kuma su hada kai da masu ruwa-da-tsaki a qananan hukumomi domin ganin an farfado da wani shiri da zai rika bibiyar irin wadannan aiyuka da ganin ana bin ka’idojin amfani da su, ko da kuwa ta dawo da aikin duba-gari na Mallaman tsabta da ake da su a da, wadanda bayan tafiyar turawan mulkin mallaka suma suka bace.

Sai kuma shawo kan su manyan abubuwan da kan jawo matsalar, wato rashin ilmin zamani da talauci. Dole ne a yanzu kowa ya san cewa ilmin zaman duniya a wannan zamani ya zama wajibi, musamman ga yaran da ake turo su karatun AlQur’ani kawai, wadanda sune suka fi kowa rashin matsuguni a al’umma, don haka su suka fi kowa yin ba-haya a bainar jama’a, kuma su suka fi kowa shiga hadarin kamuwa da cututtukan da kan kama jama’a su rika kuma yada su cututtukan. Bayan ilmantarwa akan amfanin makewayi, sai kuma magance talauci. Wannan kusan ya zo kan gaba, inda gwamnatin tarayya take tattara bayanai na wadanda suka cancanta su rika karvar tallafi domin magance talauci. To tabbas idan aka aiwatar da wannan shiri da gaske, ba da wasa ba, za a ga cewa ba a talauci kawai aka sa hannun jari ba, an saka hannun jari a harkar lafiya da ilmi, da sufuri da sauransu, domin dama rashi ne ke sa wasu kin neman lafiya da ilmin.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s