Matsalolin yanayin damina

Kowane yanayi yana da nasa alfanun da kuma rashin alfanu ga lafiyarmu. Wani yanayin alfanunsa ya fi na wani, amma a mafi yawan lokaci ba yanayin ne ke da matsala ba, halayyarmu ce ke kawo matsala. Misali, barin ciyawa ta taru a kofar gidajenmu saboda danshin damina, wanda shi kuma kan jawo sauro; ko kuma ta yin ba-haya ko jibge shi a gefen magudanan ruwa (ka bi duk hanyoyin manyan garuruwanmu masu rafi ko tabki ko kogi, ka bi gefen inda mutane suke wanka ka ga yadda ake ba-haya!)
Ga cututtukan da aka fi samu da damina a takaice:

1-Cututtukan kwalara da atini da taifot: Duk wadannan cututtuka jirgi daya ne ya kwaso su, domin duk kusan a gurbataccen ruwa ake samunsu. Lokacin damina, lokaci ne da ruwa kan wanko bayan-gidan jama’a daga ko’ina zuwa ruwa ta hanyar kwatoci, tabki, kuddufai, koramu da sauransu, daga nan su shiga koramu da sauran manyan dam-dam na garuruwa, inda ruwan sha da ruwan da ake ban ruwa na noma ke taruwa.
Ciwon kwalara ko amai da gudawa, kwayoyin cutar bacteria da ake kira bibrio cholerae, su ke kawo shi. Atini ma ciwo ne da ke zuwa da gudawa mai jini ko majina, ko duk biyun, wanda kwayoyin cuta iri biyu ke kawowa. Wadannan kwayoyi su ne na bacteria da ake kira Shigella da na parasite da ake kira Entamoeba. Zazzabin taifot, kwayoyin cuta na bacteria da ake kira Salmonella typhi ke kawo su.
Duk wadannan kwayoyi a ba-haya da ruwan da ya gurbata da ba-haya suke rayuwa yawanci kuma dalilin kashi da muke yi barkatai a gefen magudanun ruwa. kwayoyin na yaduwa ne ta hanyoyi hudu: In aka sha gurbataccen ruwa, ko aka ci abincin da aka dafa da wannan ruwa, ko aka ci abincin mai dauke da wadannan kwayar cutar (wadda ba ta wanke hannu da sabulu bayan ta yi bayan-gida), ko kuma kuda ko kyankyaso masu shiga bayan-gida su kwaso cutar su zo su yada kan abinci suka kwaso kwayoyin suka sa a abinci. kwayoyin sukan shiga ciki su makale a ’ya’yan hanji, su kawo ciwon ciki (taifot) ko atini, ko amai da gudawa.
Alamomin Cututtukan:
Da kwayoyin sun shiga hanjinmu, nan da nan cikin ’yan awoyi sai zawo ko ciwon ciki. Wasu sukan yi amai. Amma atini ba ya zuwa da amai – abin da ya bambanta shi da ciwon amai da gudawa. Kafin gari ya waye mutum ya fada, ba kuzari, ruwan jikinsa ya kare. Idan ba a dauki mataki ba rai zai iya yin halinsa; Idan babba ne akan dau lokaci kafin ya galabaita. Yara ’yan shekara 1 zuwa 5 da haihuwa da tsofaffi su suka fi mutuwa. Manya sukan iya kamuwa da kwayar cutar ba tare da sun yi amai ko zawo ba ma.
Cututtukan na yaduwa ne kamar wutar daji ta hanyoyi uku: kuda ko kyankyaso yakan dauko kwayoyin cutar a amai ko zawon da mai cutar ya yi, ya taba abinci ko ruwa. Hanya ta biyu kuma ita ce mutum ya taba amai ko zawon mai cutar ya ci abinci bai wanke hannu ba. Hanya ta uku kuma idan mai dauke da kwayar cutar ya yi ba-haya ko zawo kusa da ruwan da jama’a ke amfani da su ko da rijiya ce kuwa.
Hanyoyin Kariya Daga Wadannan Cututtuka:
Ruwan famfo wanda hukumar gidan ruwa ta tace ta sa magani da kuma irin na kwalba da kan bulbulo daga karkashin dutse da ruwan sama da aka tara kai tsaye da ruwan rijiya mai zurfin gaske, kamar ta burtsate ko tuka-tuka, su ne za a iya cewa da wuya a samu wadannan kwayoyin cuta a ciki. Duk wani ruwa da bai shiga cikin wannan lissafi ba to ka kiyaye shi.
Sauran hanyoyin su ne:
1-A guji bayan-gida barkatai a hanya da gefen magudanan ruwa ko rijiya ko kogi kamar dabbobi. A koyi hali irin na kyanwa wadda takan tabbatar ta bizne ba-hayanta.
2-Kada a gina rijiya dab da bayan-gida, a ba da tazarar akalla kafa 50.
3-Gina gidajen ba-haya na zamani a wuraren zaman jama’a kamar kasuwanni zai rage yawan ba haya barkatai, da kusa da magudanan ruwa.
4-Saka dokar-ta-baci ga duk wanda aka samu yana bayan-gida a bainar jama’a ko yana zub da ba-haya irin na gidaje a magudanan ruwa.
5-A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha. Ruwan famfo yana da sinadarin chlorine da kan kashe kwayoyin cutar. Amma wasu lokuta bututun ruwa sukan fashe su sake gurbata da ruwan kwatami ta yadda sinadarin ma ba zai yi tasiri ba.
6-Hukumomin gidan ruwa su tabbata an tace kuma an saka sinadarin chlorine yadda ya kamata kafin a sako ruwa.
7-A guji shan kankara da ba a tabbatar daga ruwan da aka hada ta ba. Idan ya zama dole, a ribanya ledar jikin kankarar kafin a sa a ruwa mai tsabta don ya yi sanyi.
8-A tabbata an wanke hannaye da sabulu bayan an yi bayan-gida ko kuma an yi wa yara tsarki da kuma kafin cin abinci. Yawan wanke hannu da sabulu yana hana kamuwa da wadannan cututtuka kwarai da gaske. Kuma a tabbata an fara yin amfani da wani mayani kamar kara ko toilet paper bayan an yi bayan-gida, daga bisani kuma a sa ruwa.
9-Masu sayar da abinci su guji taba abin sayarwar da hannu, sai da babban cokali ko marar zuba abinci.
10-Duk matar da ba a yarda da tsabtarta ba a kiyayi abincinta.
11-A kiyaye tsabtar muhalli da ta bayan gida don kada kuda da kyankyaso su samu wurin zama.
12-A rufe duk wani abinci da abin sha da aka ci, don kada kuda ko kyankyaso ya hau.
13-Kada a ci kayan lambu irin su latas da karas da ba dafa su ake yi ba, har sai an wanke su a ruwa mai gishiri, an kuma dauraye. Ruwan gishiri yana aiki a nan kamar sabulu.
14-Da zarar an ga alamun gudawa, a samo ruwan gishiri da sukari na sachet wato ORS a hada a fara ba mara lafiya kafin a garzaya asibiti mafi kusa. Idan ba a samu ORS ba a samu gishiri rabin karamin cokali da sukari cikin karamin cokali biyar a hada a ruwa mai tsafta kwatankwacin babban kofi, a bayar a hankali har a kai asibiti.
15-Dole a tafi asibiti domin a duba maras lafiya sosai a ba shi magani ko karin ruwa saboda mara lafiya zai iya amai ya dawo da ruwan gishirin da aka ba shi. Sinadarin ORS ba shi zai tsayar da gudawa ba.

2- Zazzabin cizon sauro:
Bayan cututtukan da kan sa gudawa, an yi amanna cewa zazzabin cizon sauro shin e na biyu wajen halaka yara kanana kuma ya fi yawa a lokacin damina saboda yawan ciyayi inda sauro ke kyankyasa. Wannan ciwo kuma har ila yau bai bar manya ba. Ta macen sauro ce ke daukar wannan kwayar cuta ta saka wa mutane yayin da ta zo shan jini da dare.
Alamomin Wannan Ciwo:
1-Akwai zazzabi mai zafi. 2-Ciwon kai. 3-Wani lokaci akwai amai ko kumallo. 4-Sai ciwon gabobi. 5-A yara zai iya kawo suma idan jiki ya yi zafi sosai.
Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo:
1-Yawan sare ciyayin da ke kewaye da gidajenmu na rage kwanciyar sauro.
2-A rika tabbatarwa magudanan ruwa suna gudana sosai, ta hanyar daina zuba shara a cikinsu ko kuma rufe su ma baki daya.
3-A rika kwashe shara a kai-a kai.
4-Saka kaya masu rufe ko’ina a jiki idan dare ya yi, kamar riga mai dogon hannu da safa a kafa.
5-Yin amfani da gidan sauro irin na taga da kofa don rage shigar sauro dakunan kwanciya.
6-Yin amfani da gidan sauro yayin kwanciya.
7-Za a iya sa maganin feshi a daki amma a tabbatar ba kowa a ciki tukun, in ya sarara a bude tagogi.

3-Mura:
Sai ciwon mura. Akan samu wasu kwayoyin cuta musamman na birus masu son danshi su kawo matsala a irin wannan yanayi na damuna. An yada ta ta iska, ta hanyar atishawa, sai dai ba kamar lokacin bazara ba lokacin da gari ba danshi sai busasshiyar iska.
Hanyoyin Kariya:
1-Yawan cin kayan marmari na itatuwa masu cike da sinadaran bitaman na rukunin C, yana kiyaye wannan ciwo, ta yadda ko mutum ya sami matsalar ba zai nuna alamu ba ma a mafi yawan lokuta, tunda sindarin bitaman C yana sa garkuwar jini kaifi, wanda su kuma sukan kashe kwayar cutar.

4-Borin jini:
Bayan mura sai borin jini. Akwai mutane da yawa da kan samu kurajen borin jini a farkon damina kawai, ta yadda da zarar damina ta kankama, sai su bace. Wannan ba wata matsala ba ce tun da ba ta da wani hadari ga rayuwa, sai dai dan kaikayi. Ko a kyamis za a iya ba mutum maganin borin jini da kaikayin jiki (irinsu piriton). Mun rubuta a makon da ya shude cewa wani mai karatu ma Aduwa kawai yake ci sai su bace.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s