Gwaje-Gwajen Lafiya Kafin Aure

Ana so a rika yin aune-aune da gwaje-gwajen lafiyar ma’aurata kafin a daura aure. Wannan gwaji a likitance shi muke kira da pre-marital screening, kuma a yanzu a kusan ko’ina a duniya, har qasashen musulmai na Larabawa ya zama doka ta wajibi wadda dole sai an cika kafin a daura aure.

Gwaje-gwajen lafiya kafin aure na daya daga cikin manyan hanyoyin da ake bi wajen kiyaye aukuwar cutuka, musamman a mata da kananan yara. Tunda an ce riga-kafi ya fi magani, idan aka rungumi wannan hanya ta riga-kafi za a iya shawo kan wasu manya-manyan cutuka da mata da yara kan samu wadanda za mu lissafosu a gaba.

Awon jini shi ne ginshiqin wannan gwaji. Ana auna cutuka da dama a ma’auratan, amma su cutukan sun kasu kashi biyu: Cutukan gado na tangardar kwayoyin halittu na gado na DNA wadanda uwa da uba za su iya sa wa dansu, da kuma cutukan da kwayoyin cuta za su iya sa wa, wadanda miji ko mata za su iya sa wa junansu, har ma idan ba a yi sa’a ba su sa wa ‘ya’yansu. A kashi na farko ana duba kwayoyin halittu na cutuka kamar na amosanin jini wato sikila da sauran tangardar kwayoyin halittun gado irinsu ciwon maloho da sauransu. Amma da yake ciwon sikila ya fi yawa, kuma ya fi yi wa yara illa da saurin kisa, an fi ba da karfi da muhimmanci a kansa. Wannan gwaji na sikila sunansa ‘Hb Genetype’, kuma a yanzu wajibi ne ma’aurata sai sun yi shi. A kashi na biyu kuma ana auna cutuka ne wadanda kwayoyin cuta sukan sa, cutuka irinsu kwayar kanjamau kamar yadda ka ce, gwajin da muke kira ‘HIV Screening’ sai awon ciwon

hanta na hepatitis B, wanda muke kira Hepatitis B Screening’ sai na ciwon tunjere ko syphilis, awon da ake kira VDRL. Akwai saura amma wadannan su ne manyan.

Wadannan aune-aune a yanzu sun zama tsari na dindindin a asibitocinmu wadanda ake yi lokutan awo, amma ba su zama tsari na dindindin ba a masallatai da majami’u inda ake daura aure ba. Wannan shi muke so a canza, domin ina amfani a zo awo a ga mace da wadannan cutuka? (Amfanin kawai shi ne, watakila a ceci danta, amma ba ita ba). Amma idan aka yi kafin aure an kiyayeta da ita da ‘ya’yanta. Tunda misali idan aka ga akwai mai ciwon hanta a tsakanin ma’aurata alluran riga-kafi kawai za a yi wa wanda bai da ciwon a cikinsu, shikenan an kare kowa.

ILLOLIN TABA SIGARI

Sigari   Tarihi ya tabbatar da cewa an dade ana zuka ko taunawa ko shakar taba a duniya, domin kusan shekaru dubu hudu kenan da fara amfani da taba. Sai a ‘yan shekarun baya ne, kamar shekaru dari daya da suka shude sa’annan aka fara alakantata da cututtuka irin na zuciya da na huhu da ciwon daji iri-iri.

Duk da cewa a kasarmu da sauran kasashen Afirka matsalar bata yi kamari sosai ba kamar sauran sassan duniya, an yi kiyasin a kalla rabin mazan duniya suna sha ko sun taba shan taba sigari. A mata matsalar bata kai haka ba domin kashi goma ne kawai cikin dari na mata ke sha. Yawanci mutane na fara sha ne tun a kuruciya daga shekaru sha biyar misali zuwa sama, kuma ana koya ne a wurin iyaye ko abokai ko dai na makaranta ko na majalisa. Da yake aikin babban sinadarin cikinta wato nicotine a kwakwalwa yake, nan da nan kwakwalwar takan ji dadi kuma ta nemi kari, ta haka har mutum ya saba. Wasu kalilan wadanda kwakwalwarsu bata jin dadin sinadarin a nan take suke barin shanta, wato ba kowa bane sigari ke wa dadi.

Da an zuki hayakin sinadarin nicotine ke tafiya huhu, a nan sai magudanan jini su tsotse shi su rabawa lakar jiki, da kwakwalwa, nan da sai mutum ya ji nishadi. Bayan sinadarin nicotine sauran guba da ke tattare a cikin hayakin, irinsu benzopyrene, da formaldehyde, da cadmiumda nickelda arsenicda nitrosamines,  su kuma manyan cututtuka irinsu ciwon daji suke kawowa. Amma an tabbatar da cewa taba ta taunawa tunda babu hayaki, ba ta kai mai hayaqi illa ba. Duk da haka ita ma takan iya sa ciwon kansa ko sankara.

Ga cututtukan da aka tabbatar taba sigari kan jawosu

 1. Sankarar baki da makoshi
 2. Sankarar Huhu
 3. Sankarar tantanin fitsari na mara
 4. Bugun zuciya
 5. Kumburin Huhu na COPD
 6. Bugun jini a kwakwalwa mai sa mutuwar barin jiki

Akwai wasu musabbabai ban da sigari da kan jawo wasu daga cikin cutukan da aka lissafa, kamar bugun zuciya da mutuwar barin jiki kiba da hawan jini suka fi kawosu, sa’annan shan sigari. An kiyasta duk shekaru mashaya sigari miliyan bakwai duk shekaru.

Hanyoyi da dabarun rabuwa da taba sigari suna da yawa kuma sukan taimaka wajen kiyaye wadannan cutuka da muka lissafa a sama. Hukumar Lafiya ta duniya ta tabbatar da cewa hukumomi da daidaikun mutane masu sha, duka akwai rawar da zasu iya takawa wajen ganin karshen wannan bala’i wadda kamfanonin sarrafata ne kawai suke moruwa da ita. Wadannan sun hada da:

Bangaren Hukumomi:

 1. Sakawa sigari Haraji mai tsauri: Wannan zai iya sa sigari ta yi tsada. Hakan kan sa mutum ya rika tunanin yawan kudin da yake kashewa a kanta, domin ya rage. Hasali ma wannan tsadar ce ta sa kasashe marasa arziki ba su kai masu arziki shan taba ba.

 

 1. Saka dokar hana shan taba a bainar jama’a: Kasashe da dama sun gwada wannan hanya kuma sun fara ganin moriyarta domin zama ma da madaukin kanwa yana kawo farin kai, wato masu zama inda ake shan sigari da yawa su ma suna cikin hadari kamar na masu sha.

 

 1. Kamfe ta kafofin watsa labarai kamar irin wadannan mujallu, da gidajen radiyo da talabijin, da manyan fastoci a garuruwa da kauyuka a wuraren taruwar jama’a kamar kasuwanni, asibitoci, da sauransu da yaren da mutanen garin ke fahimta, da hana tallanta ta wadannan kafafe

 

A bangaren daidaikun masu sha:

 1. Gudunmowar iyaye: Da yake a kuruciya yawanci mutum kan fara shan sigari, ya kamata iyaye maza da mata mu rika kula da abokan ‘ya’yanmu. Illar itace akwai alaka mai karfin gaske tsakanin shan taba sigari da shaye-shayen sauran muggan kwayoyi a tsakanin samari. Akwai alamu da ake gani a abokai kamar duhun lebba da tafin hannuwa da jan idanu da akan gane mashayanta.

 

 1. Gudunmowar mata: Sanin wasu ne cewa tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama a kwanaki ya sanar da rabuwa da sigari saboda nacin da matarsa ta rika masa a kan ya bari. Wato kenan in dai uwargida ta kafa kahon zuka a kan maigidanta zai iya barin sigari, ba don komai ba don har ita ma idan yana sha a gidanta tana cikin hadari da ita da yaranta

 

 

 1. Gudunmowar ma’aikatan lafiya: Dole mu ma ma’aikatan lafiya mu ci gaba da wayar da kan jama’a akan wannan matsala, kuma mu guji shan sigari idan muna sha, musamman a bainar jama’a domin mun san akwai masu sha kalilan a cikinmu. Illar ita ce ba mu san iya mutanen da suke iya koyi ko nuni da dabi’un ma’aikacin lafiya ba

 

 1. Canjin ra’ayi: Haka kawai mutum zai iya yin ra’ayi barin sigari kuma ya bari nan take ba tare da wata matsala ta faru ba. A lokutan azumi an fi samun damar yin hakan. Wasu idan suka yi irin wannan canjin ra’ayi tashi guda sukan sha wahala saboda sabo da sinadarin nicotine da kwakwalwarsu ta yi.

Wasu kuma ba sa samun wata matsala.

 

 1. Musayar sinadarinNicotine: Ga wadanda suka samu matsala saboda tsaida sinadarin nicotine tashi guda kamar wasu alamu a jiki na rashin lafiya da sa wa kwakwalwa alamun dan tabin hankali na wani lokaci, akan taimaka musu da musayar sinadarin ta hanyar cingam ko alewa ko lika sinadarin a kan fata. Wadannan sinadarai an rage karfinsu ta yadda ba za su cutar ba sosai. Mutum na sa wa yana ragewa a hankali har a zo a tsayar gaba daya. Idan ana amfani da dayan wadannan mutum ba zai ji kwadayin sigari ba sosai. Ana iya samu a manyan kyamis-kyamis

 

 1. Magunguna: Idan wadannan hanyoyi sun gagara kuma mutum yana da ra’ayin daina sha, to akan iya taimaka masa da wasu magunguna masu aiki a kwakwalwa amma sai an je wurin likita ya rubuta.

 

BAYANI AKAN CIWON NUMFASHI NA CORONA

Kwayar Corona

K’wayar Cutar Corona

A ‘yan makonnin nan ne muke ji a labarai cewa wata irin mura sabuwa fil mai zafin gaske kuma mai saurin yad’uwa ta b’ulla a k’asar Sin. K’wayar cutar da kan sa wannan mura sunanta Novel Corona wato sabuwar k’wayar corona wadda a karon farko ne take kama mutane, kuma tana kama da ta SARS domin kuwa dukansu k’wayoyin virus ne wad’anda akan d’auka daga jemagu. Kun san a k’asar Sin ana shan dabgen jemagu. Wato ita wannan k’wayar cuta ta samo asali ne daga jemagu. Daga wad’annan dabbobi ne cutar kan shiga jikin d’an Adam. Ana yad’ata ta iska sai ta shiga hanyar numfashi idan mai ita ya yi tari ko atishawa.

To had’arin da ma shi ne, ita sabuwar k’wayar cuta wadda ta taso daga dabbobi kuma take yad’uwa a cikin mutane tana zuwa ne a matsayin annoba, wato idan ta b’ullo ba mutum d’aya take kamawa ba. To sai aka yi rashin sa’a ita wannan ba ma gari d’aya kawai take kamawa ba, duka duniya ta shiga domin tana yad’uwa ne kamar wutar daji ta hanyar mutane masu shige da fice a k’asashen duniya. Ga shi ba mu da riga-kafinta (ba a ma santa ba ballantana a k’irk’iri allurar riga-kafinta) don haka jama’a da dama yake kwantarwa, wasunsu kuma ba sa kai labari saboda ciwon ba shi da magani.

A wannan kafa mun sha fad’in cewa duk wani ciwo wanda wannan k’waya ta virus kan kawo wuyar magani gareta, irinsu ne ke kawo k’anjamau da bak’on dauro wad’anda har yau ba a gano maganinsu ba.

A yanzu haka dai maganar da ake ta kama mutane kusan sam da 500,000 kuma ta halaka 26,000. Kuma a halin da ake ciki an ce ta shiga kasashe kusan 200 har da k’asashenmu na Afirka.

Abinda mutumin da ya kamu da wannan ciwo zai fara lura da shi shine ciwon mak’ogaro sai ciwon jiki da kasala da zazzab’i mai zafi, sa’annan sai tari, a fara jin hanyoyin numfashi sun rirrik’e. A wasu lokuta ana samun gudawa. Don haka duk wanda ya ga wani da irin wad’annan alamu dole ya taimaka ya sanar da hukumomin lafiya mafi kusa domin a tantance irin ciwon, amma kada ya kusanci mai matsalar. Idan ciwon ya yi tsanani yana kama hanyoyin numfashi musamman huhu, inda yakan hana numfashi. Ta haka ne wad’anda ke mutuwa suka mutu.

Hanyoyin Kariya

To da yake annobar yad’uwa take kamar wutar daji dole ne muma mu d’auki matakan k’aiyade shige da fice zuwa k’asar Sin da ma duk k’asar da aka samu wannan ciwon, na d’an wani lokaci har sai abubuwa sun lafa, kamar yadda sauran k’asashen duniya suka fara aiwatarwa.

Duk da dai ba mu isa mu hana mutanen wata k’asa d’abi’u da al’adunsu ba, muna sa ran hukumomin lafiya na duniya za su tsaya kai-da-fata wajen ganin an bar shan farfesun jemagu a k’asar Sin, da ma ciye-ciyen namun daji iri-iri da suke yi, domin cutukan da ke jikinsu Allah-kad’ai ya san iyakacinsu.

A rage fita, a irin wannan lokaci na annoba, a lazimci zaman gida ko na wurin aiki kad’ai. Idan ta kama dole a fita kada a kuskura a tab’a komai sai an sa safar hannu. Sai yawan tsabtar hannaye wato wanke hannaye da ruwa da sabulu ko da man spirit na tsawon rabin minti duk lokacin da aka fita aka dawo, sai nesa-nesa da jama’a da gujewa shiga taro. Yawan shan ruwa na sa mak’oshi ya jik’e ya hana k’wayoyin cutar lik’ewa a mak’oshi. Sai tsabtar muhalli, da bibiyar labarai da shawarwarin ma’aikatan lafiya, su ne manyan hanyoyin da a d’aid’aikunmu za mu iya yi mu kiyaye kanmu daga kowace irin annoba.

ZAKI DA MAIKO

ZakiZaki da maiko suna da amfani a jiki. Sai zaki da maiko sun yi yawa a jiki ne yake zama illa. Wato abin ne yana da ‘yar sarkakiya; idan baka ci ba, akwai matsala, idan ka ci da yawa ma akwai matsala,kenan sai an daidaita su. A kimiyyance komai ana sonsa saisa-saisa ne, kuma har zaki da maiko; idan suka yi kadan jiki yakan bukacesu, idan kuma suka yi yawa nan ma har ila yau jiki zai yaki wannan yawan. Dole sai mutum ya gano yadda zai saisaitasu don lafiyar jikinsa. Dalilan da kan sa dole a ci ko yaya ne, su ne cewa wasu sinadarai da jiki ke bukata a kowace rana domin aikin yau da kullum, kamar bitaman na rukunin A, akan samesu a kayan zaki ne, wasu kuma sinadaran kamar irinsu bitaman ajin A, da D, da E, da K ana samunsu a abinci ne masu maiko.

Yawanci dabarar da likitanci ya kawo mai sauki ta saisaita cin zaki da maiko ita ce – a ci daidai misali, amma a biyo bayan cin da konasu ta hanyar motsa jiki, gami da cin kayan ganye da na itatuwa. A wasu lokuta idan wadannan biyun suka gagara, kuma zaki da maikon suka zo suka yi yawa a jiki, to fa sai an ba da magungunan konasu. Za a iya ganin wannan a mai ciwon suga (inda ake ba su magungunan kona zaki) da mai ciwon mummunar kiba (inda akan ba su magungunan kona moiko da kitse)

Wato idan aka ci zaki da maiko, jiki zai tsotsi abinda yake bukata to amma sauran ajiyesu zai yi. Idan ana so kada jiki ya ajiyesu sai dai kenan a ci kadan, sa’annan a kona ragowar ta hanyoyin da aka fada a sama. Domin wannan ajiyar ce sanadiyar cutukan zamani irinsu mumunar kiba da hawan jini da ciwon suga da na sanyin kashi na gabobin jiki da sauransu. Idan da za a lura lafiyar

 1. Mutum mai cin zaki da maiko wanda ba ya konasu ba daya take da
 2. Mutum mai ci mai kona ragowar ba. Haka nan lafiyar wannan na biyun ba daya take da
 3. Mutumin da ba ya cin zaki da maiko kwata-kwata ba.

Kun ga kenan an kasa mutane kashi uku ta bangaren cin zaki da maiko. Idan da zan zabi wanda zai fi lafiya a cikinsu, mutum na biyun zan zaba.

Idan dai mutum ya kasance a aji na biyu to ba sai ya nemi wani maganin zaki da maiko na asibiti ba, ballantana wanda akan ji ana yawan talla a titi.

Wadanne al’adun jego ne ke illa ga lafiya?

A likitance akwai wasu al’adu na jego masu amfani ga lafiyar mai jego, akwai kuma wadanda ba su da wani amfani. Kai akwai ma wadanda kan yi illa ga lafiya. Abubuwan ma ai yanzu da sauki domin zamani ya zo ya kawo wa masu jegon sauki sosai.

A al’adance da zarar mace ta haihu akan ba ta tafasasshen ruwa da ganyen darbejiya ta je ta yi wanka – wankan jego. A kimiyyance zuba ruwan zafi mai zafi haka kan iya buda hanyoyin jini, karfin bugun jini ya sauka, wanda kan sa matan jin jiri a yayin wankan, wasu ma su fadi su suma. Don haka kenan maimakon ruwa tafasasshe, a likitance sai dai a sa wanda ba tafasasshe ba kamar mai dimi sosai.

Bayan an yi wanka akan hada wa mai jego dauri ta sha, wanda akan ce ruwan maganin kan karawa mai jego da jariri kwari. Wasu ma sukan hana mai jego ma shan kowane ruwa sai dauri. To mu dai a likitance ba mu san shan ruwa na da matukar muhimmanci. Ta bangaren dauri kuma ba mu da masaniyar wadanne irin hadi akan yi wa ruwan maganin ba ballantana mu san illa ko alfanun hadin. Bayan nan wasu kan hada kunun kanwa a ba mace ta rika sha a kullum. Kanwa a kimiyyance gishiri ce domin tana da sinadarin sodium mai yawa, wanda zai iya sa hawan jini ko ya ta’azzara shi. Ba za a hana shan kunun kanwa ba tunda ko muma ma’aikatan lafiya mukan taba. Wato kenan a likitance za a iya sha jefi-jefi amma ba kullum ba ko kuma a sha na tsamiya.

Akan kuma yi yaji a rika ba mai jego tana sa wa a abinci domin karin dandano. A wancan lokacin da aka kirkiro da al’adar babu abubuwan da za su karawa abinci dandano shi ya sa akan yi wannan. Shi yaji ba shi da wata illa idan ba ga masu ciwon olsa ba, yana ma da sinadarin vitamin C don haka shi ma a iya ci jefi-jefi. A yanzu kam saboda zamani akwai kayan dandano da dama don haka an rage.

Sai al’adar hadawa mai jego farfesu da naman suna. Wannan al’ada ko a likitance ita ce muke ganin ta fi kowanensu alfanu, domin kuwa yawan shan farfesun karin lafiya ne ga mai jego da jaririnta.

Wasu ma sukan ma hana mai jego fitowa waje bayan haihuwa na tsawon mako guda idan banda fita bayan-gida. Wannan al’ada kwata-kwata babu alfanu in dai mace za ta iya yawonta. A barta ta rika fitowa da hantsi tana samun sinadarin vitamin D na hasken rana.

 

 

KWARI MASU MANA ILLA GA LAFIYA

KwariWasu kwari na gida da na daji na daga cikin manya-manyan halittu masu yada mana cutuka. Suna yin haka ne ta hanyoyi daban-daban yayin da suka yi cizo ko kuma suka hau abinda mukan ci ko mukan sha. A masu cizon wasu sukan sa mana kwayoyin cuta a lokacin da suka yi cizon, wasu su sa dafi (kamar kudan zuma), wasu kuma ba sa saka wata kwayar cuta illa dai su yi ta zukar jini har ma su iya sa ciwon karancin jini idan ba farga da wuri ba. Ya kamata mu san wadanne kwari ne wadannan domin mu gujesu.

Bari mu fara duba masu yada cutuka yayin cizo, kafin mu zo kan masu yada cutuka ba tare da cizo ba, sai kuma mu karkare da masu cizo don kawai shan jini.

Sauro: Wato lange-lange mai ramar keta, shi ne babban mugun a cikin kwarin gida masu saka mana cututtuka. Kusan kowa ya san sauro shi yake kawo mana ciwon zazzabin maleriya, wanda ke kashe miliyoyin mutane duk shekara, yawancinsu yara kanana. Abinda wadansu basu sani ba dai game da sauro shi ne cewa banda ciwon zazzabin maleriya, zai iya sa ciwon zazzabin shawara na yellow fever da ciwon zazzabin zika, da ciwon zazzabin Dengue da ciwon tundirmi na filariasis da ma wasu da dama. Don haka a kiyayi sauro.

Kudan Tsando: Wanda ake kira tsetsefly shi ma yana sa wa mutane da dabbobi musamman shanu a irin kasashenmu na Afirka, shi ya sa aka fi samun ciwon tsakanin makiyaya. Yana sa ciwon kwakwalwa na sammore da fulatanci wato sleeping sickness da Inglishi, mutum ya ji ba ya tabuka komai sai yawan barci.

Kwaron Filfilwa: Wanda ake cewa blackfly ko bakin kwaro shi an fi samunsa a garuruwan kudu a kusa da koguna masu gudu. Shi kuma shi ne ke sa ciwon dundumi (makanta) da tundurmi na onchocerciasis (kumburin kafa). Don haka duk wanda ya je kurmi cikin qungurmin dazukansu sai ya kiyaye cizon kwari don kada su sa masa irin wadannan cutuka.

Kaska: Kaska ba dabbobi kadai suke wa barna ba. Kwari ne da kan sha jinin mutane tare da sa musu kwayoyin cuta daban-daban tun daga na bacteria har na virus irinsu zazzabin typhoid da na ciwon Lyme disease wanda ke sa wasu irin kuraje.

Quma: Kwari ne masu kama da kwarkwata, kuma su ma suna shan jini sosai. Su ake kira flea da Inglishi. Kwari ne da ke yada cutuka na bacteria masu sa annoba. Su aka alakanta da wata babbar annoba a tarihi (wadda aka kira bubonic plague) da ta yi sanadiyar salwantar rayukan miliyoyin mutane a tarihi a yankin Nahiyar Turai shekaru dubu da suka wuce saboda suna bin beraye suna kwaso cutukansu suna bazawa jama’a.

 

Sai kuma masu yada cutuka idan suka tava kayan abincinmu. Wadannan sune:

Quda: Shi ne na biyu mai yada cutuka da dama bayan sauro a irin kasashenmu masu zafi. Shi ne ummul-haba’isin cutuka irinsu zazzabin typhoid da ciwon amai da gudawa na kwalara da na atini.

Kyankyaso: Da dama ba a san cewa duka cutukan da kuda kan iya yadawa kyankyasai ma za su iya yadawa. Don haka a yi hankali sosai da kyankyasai.

 

Bari kuma a duba kwari masu shan jini. Wadannan sun hada da:

Kwarkwata: Ba kamar kudin cizo da kwaron kazwa ba, kwarin kwarkwata za su iya kama kowa, mai tsabta da maras tsabta. Su ne qwarin da suka fi sa kaikayin kai ga yara ‘yan mata, musamman ‘yan makaranta, fiye ma da amosanin ka, a wasu lokutan ma har da manya mata. Maza da yake a yanzu zamani ya zo muna yawan aske kawunansu, an bar tara suma Afro, abin yayi sauqi sosai a tsakaninmu. Kwarin sukan shiga kan yarinya ne daga wata zuwa maras ita, kamar a wurin wasa, kamar misali a zaman aji na makaranta ko ta musayar kallabi. Kwarin idan suka shiga kai jini suke zuka. Kusan a kididdiga, a duk yara mata goma sai an samu a kalla daya mai kwarkawata, wato a aji mai ‘yan mata hamsin akan samu a kalla biyar masu matsalar, kuma ba wuya su sa wa na kusa da su.

Kudin Cizo: Su ne wadanda aka fi gani a kayan shimfida. Ana iya samunsu a kasashe da dama a duniya, tun daga kasashen nahiyar Amurka da nahiyoyin Turai da Asiya. Yawanci mutane ke yadasu daga wannan wuri zuwa wancan a cikin jakunkuna da kayansu. Don haka ba abin mamaki bane a samesu a gadon manya-manyan otal-otal, da na fitatttun wuraren shakatawa, kuma a iya kwasarsu a kai gida ba a sani ba. Abinda ya sa ake iya daukarsu da yadasu shine cewa sun iya buya, domin da wuya a gan su da rana, don sukan iya shigewa cikin yadin katifa ko kalmasar zanin gado, ta yadda sai duhu yayi kafin su lallaba su fito, su fara cizo suna shan jini. Wannan cizo zai iya sa wurin ya fara kaikayi ya canza kala, sai dai bai kai cizon kuma saka kaikayi ba. A kasashen Kudancin Amurka irinsu Mexico, kudin cizo za su iya yada kwayoyin cuta masu sa ciwon sammore da muka yi magana da fari

Kwarin Kazwa: Kwari ne masu kama da kwarkwata ko kudin cizo, sai dai saboda kankantarsu, su ba a iya ganinsu da kwayar ido. Matsalar itace idan kwarin da ke kawo kazwa suka shiga gidan mutum, sai an yi da gaske kafin su fita, don haka za a ga ba mutum daya kawai sukan kama ba, kusan duk mutan gidan. Sun fi nunawa a yara saboda rashin karfin garkuwar jiki. Manya masu kwarin garkuwar jiki ba su cika nuna kuraje da kaikayi ba idan kwarin suka shiga karkashin fatarsu. Don haka su ma manya za su iya zama sila wajen yadawa yaransu wadannan kwari. Wato a wasu lokuta ba yara ne ke kwaso ciwon ba, manya ne ke yadawa yara. Kwarin kazwa kan iya kama kowane jinsi, fari ko baki, mai kudi da maras shi duka, sai dai ta fi kama maras shi inda akan samu cinkoson wurin kwanciya.

Masu sa dafi su kuma sune irinsu kudan zuma da zanzaro da kunama da cinnaka da wasu nau’i na gizo-gizo, duk da cewa dai kunama da gizo-gizo a kimiyyance ba kwari bane, kuma sune idan suka sa wa mutum dafi zai iya masa illa sosai idan ba a je asibiti da gaggawa ba.

 

KYAMIS BA ZAI MAYE GURBIN ASIBITI BA

Kyamis ba zai maye gurbin asibiti ba, domin shi wuri ne na sayar da magunguna kawai. Su ma’aikatan kyamis iri biyu ne, akwai masu ilmin magani na digiri masu lasisi, wadanda za su iya rubutawa da sayar da kowane irin magani ne a duniya, akwai kuma wadanda aka ba horo na musamman kawai akan sayar da kananan magunguna kamar na ciwon kai da mura da tari. Su wadannan ba su da lasisi, kuma ba sa rubuta magani sai dai idan an kawo musu takardar likita su duba maganin su bayar idan suna da shi. Yawanci ma a ido mutum zai iya bambance kyamis din da yake da kwararre wato Pharmacist da wanda ba na kwararre ba, wadanda ake kira ‘Patent Medicine Store’ domin na kwararre ya fi na wanda ba kwararre ba tsari da shiryuwa.

shop0036

Kyamis

To a shi inda ake da kwararren ma’aikaci mutum zai iya zuwa ya fadi matsalolinsa shi kwararren ya ba shi shawarwari har ma da wasu magunguna idan ta kama, amma ba zai yi jinya ba, wato ba zai yi allura ko karin ruwa ko tiyata ko kwantarwa ba, tunda ba huruminsa ba ne. Idan aka ga ana yin jinya a kyamis to a san kuskure ne babba wanda idan aka kama wurin za a iya kulle mai shi a kuma ci tararsa. Ka ga kenan ba za a iya zuwa kyamis a mayar da shi kamar asibiti ba. Domin sam ba a tsarinsu daya ba.

Hukumomin Lafiya na Kasa kamar na PHCDA sun zayyana abinda wurin jinya ya kamata a ce yana da shi, komai qanqantarsa wanda ya hada da wurin sayar da magani (kuma ya kasance akwai magungunan, ba wai hoto ba), da kwararren mai-magani zai zauna a ciki, da likita ko makamancinsa kamar Mallamin Lafiya na CHEW da ma’aikacin jinya wato nurse, sai ungozoma wato midwife, sai dakunan duba maras lafiya, da dakunan jinya (ba dole sai na kwanciya ba) da isasshen ruwa da wuta da bayan gida da dakunan gasa kayan aiki da tsabtacesu da wurin kona shara da katon allon mai sunan wurin da alama da sauransu. Wato kenan duk wurin da ka ga mutum daya ya hada wadannan aiyuka duka shi kadai yana aiki (shine masanin magani, shine likita, shine mai jinya, a wasu lokuta ma don ganganci har tiyata suke) to a gujeshi domin barna da nakasa mutane kawai za a yi, ba sama musu lafiya ba. A inda ma aka samar da wadannan ma’aikata dole sai an yi taka-tsantsan an tantance wane ne kwararre wane ne mabarnaci.

BAMBANCI TSAKANIN NAU’IKAN SUGA

Suga a kimiyyance ya kasu kala shida; akwai glucose, fructose, galactose, sucrose, maltose, da lactose. Duk wani nau’in suga da ka taba ci dayan wadannan ne, har wadanda ake sarrafawa a kamfani. Shi suga da aka sani na shan kunu ko shayi shine sucrose, wanda ake tatsa a rake. Shi asalinsa ruwan kasa ne saboda bezar raken. Idan aka wanke shi yakan dawo fari. Sauran ‘ya’yan itatuwa suma suna da nasu irin sugan wanda dole daya ne ko biyu daga cikin wadannan da aka lissafa. Akwai iri biyu a zuma ma, wadanda sune glucose da fructose. Haka ma hatsi da sauran kayan abinci, duk suna da sukari. Kai har irinsu madara da yagot da ake gani ake ji kamar ba zaqi, suna da sukari, wanda shine lactose, wanda ka ga shima daya ne daga cikin wadancan da aka lissafa.

Wani abinda watakila sai an la’akari da shi game da wadansu abinci kalilan da basu da suga wato nama, kifi da maiko shine, idan fa suka shiga jiki su ma fa za a iya mayar da su suga ne kafin jiki ya yi amfani da su. Wannan nau’in suga da ake mayar da su shine glucose, wanda shima ka ga daya ne daga cikin wadannan nau’ikan suga da aka lissafa.

Jiki ba zai iya rayuwa ba suga ba domin suga shine ginshikin sinadaran ba da kuzari  ga jiki. Sai dai a ce jiki na buqatarsa daidai misali, saboda ko ka ci da yawa ajiyeshi za a yi, idan ma ka ci kadan jiki zai nemo a kitse. Idan yayi yawa a jini, tara shi ake a sarrafa shi har ila yau zuwa kitse, inda za a tara shi a teba ko a damtse ko a cinya da sauran wuraren da jiki ke ajiyarsa, sai bukatarsa ta tashi. Bukatar tana tashi ne kuwa yayin jin yunwa, kamar lokacin azumi, ko yayin motsa jiki inda har-ila-yau za a sake narka kitsen su koma suga.

SHAYARWA GA UWA MA’AIKACIYA

Makon da ya wuce ne hukumomin lafiya a ko’ina a duniya suka ware domin fadakarwa akan muhimmancin shayarwa. Abin takaici shine duk da ci gaba da aka samu a duniya ta bangaren aikin mata ta hanyar basu hutun haihuwa da na shayarwa, da ware wurare na musamman domin kula da jariransu, a wannan kasa har yanzu ba wa mata ma’aikata irin wadannan hakkoki da saura musamman a kananan ma’aikatu.

To idan ana muhawara a kan yadda uwa ma’aikaciya za ta shayar da jaririnta ta kuma hada da zuwa aiki, wasu sa ce e uwa ma’aikaciya za ta iya barin jaririnta a gida masu raino su rika dama musu madara ko ta shanu ko ta waken soya ko wadda aka kirkira. Wannan shawara ce amma gurguwa. Wasu kuma Sudan dauki tsattsauran ra’ayin hana matar aiki ma gaba daya saboda a maida hankali kacokan kan lura da shayar da jariri. To amma dai a wannan zamani da ya kamata mace ma ta samu nata abin hannu ko don taimakawa a gida, wannan ma gurguwar shawara ce.

Mafita da masana lafiyar jarirai suka fitar itace ta ci-gaba da shayarwar kuma a je aiki. To a irin wuraren da ba sa bari a je musu da jarirai ya uwa za ta yi? Mafita wadda ba ita dai aka so ba, ita ce ta matse ruwan nono a kwalbar feeder a bari a gida don ba wa jariri duk lokacin da ya bukata. Wannan wasu za su ji kamar da sauki abin, a’a akwai ‘yar wahala. To amma dai ita ce mafita mafificiya. Abinda ya sa aka ce akwai ‘yar wahala shine da dama mata iyaye sai an koya musu yadda ake matso ruwan mama, a asibiti, wasu ma saboda zafi da gajiyarwa da sun fara za su bari. To domin haka ne akan ba su shawara idan ba za su iya matsa da hannu ba to dole sai sun sayi wani dan famfon tatsa mai kama da feeder jaririn, wanda akan samu a manyan kyamis-kyamis, mai suna breast pump.

Bayan an tatso ruwan nonon a wannan famfo sai a juyeshi a cikin feeder jaririn. Idan ‘yan awoyi ne da basu wuce uku zuwa biyar ba ake a wurin aikin, kuma gari ba zafi, a kwano cooler kawai za a sa feeder har sai jariri ya buqata, idan ma ya rage, a mayar cooler. Idan kuma tsawon yini ne aikin to kusan dole sai an cika feeder biyu ko uku, kuma ba a cooler za a sa su ba, sai dai na’urar fridge. Sa’annan kullum idan aka wanke feeder jaririn sai an tsoma su a tafasasshen ruwa domin tsabtacesu da kiyaye jariri daga kwayoyin cuta saboda damuke-damuke da masu shayarwa suka yi.

Matsalolin yanayin damina

Kowane yanayi yana da nasa alfanun da kuma rashin alfanu ga lafiyarmu. Wani yanayin alfanunsa ya fi na wani, amma a mafi yawan lokaci ba yanayin ne ke da matsala ba, halayyarmu ce ke kawo matsala. Misali, barin ciyawa ta taru a kofar gidajenmu saboda danshin damina, wanda shi kuma kan jawo sauro; ko kuma ta yin ba-haya ko jibge shi a gefen magudanan ruwa (ka bi duk hanyoyin manyan garuruwanmu masu rafi ko tabki ko kogi, ka bi gefen inda mutane suke wanka ka ga yadda ake ba-haya!)
Ga cututtukan da aka fi samu da damina a takaice:

1-Cututtukan kwalara da atini da taifot: Duk wadannan cututtuka jirgi daya ne ya kwaso su, domin duk kusan a gurbataccen ruwa ake samunsu. Lokacin damina, lokaci ne da ruwa kan wanko bayan-gidan jama’a daga ko’ina zuwa ruwa ta hanyar kwatoci, tabki, kuddufai, koramu da sauransu, daga nan su shiga koramu da sauran manyan dam-dam na garuruwa, inda ruwan sha da ruwan da ake ban ruwa na noma ke taruwa.
Ciwon kwalara ko amai da gudawa, kwayoyin cutar bacteria da ake kira bibrio cholerae, su ke kawo shi. Atini ma ciwo ne da ke zuwa da gudawa mai jini ko majina, ko duk biyun, wanda kwayoyin cuta iri biyu ke kawowa. Wadannan kwayoyi su ne na bacteria da ake kira Shigella da na parasite da ake kira Entamoeba. Zazzabin taifot, kwayoyin cuta na bacteria da ake kira Salmonella typhi ke kawo su.
Duk wadannan kwayoyi a ba-haya da ruwan da ya gurbata da ba-haya suke rayuwa yawanci kuma dalilin kashi da muke yi barkatai a gefen magudanun ruwa. kwayoyin na yaduwa ne ta hanyoyi hudu: In aka sha gurbataccen ruwa, ko aka ci abincin da aka dafa da wannan ruwa, ko aka ci abincin mai dauke da wadannan kwayar cutar (wadda ba ta wanke hannu da sabulu bayan ta yi bayan-gida), ko kuma kuda ko kyankyaso masu shiga bayan-gida su kwaso cutar su zo su yada kan abinci suka kwaso kwayoyin suka sa a abinci. kwayoyin sukan shiga ciki su makale a ’ya’yan hanji, su kawo ciwon ciki (taifot) ko atini, ko amai da gudawa.
Alamomin Cututtukan:
Da kwayoyin sun shiga hanjinmu, nan da nan cikin ’yan awoyi sai zawo ko ciwon ciki. Wasu sukan yi amai. Amma atini ba ya zuwa da amai – abin da ya bambanta shi da ciwon amai da gudawa. Kafin gari ya waye mutum ya fada, ba kuzari, ruwan jikinsa ya kare. Idan ba a dauki mataki ba rai zai iya yin halinsa; Idan babba ne akan dau lokaci kafin ya galabaita. Yara ’yan shekara 1 zuwa 5 da haihuwa da tsofaffi su suka fi mutuwa. Manya sukan iya kamuwa da kwayar cutar ba tare da sun yi amai ko zawo ba ma.
Cututtukan na yaduwa ne kamar wutar daji ta hanyoyi uku: kuda ko kyankyaso yakan dauko kwayoyin cutar a amai ko zawon da mai cutar ya yi, ya taba abinci ko ruwa. Hanya ta biyu kuma ita ce mutum ya taba amai ko zawon mai cutar ya ci abinci bai wanke hannu ba. Hanya ta uku kuma idan mai dauke da kwayar cutar ya yi ba-haya ko zawo kusa da ruwan da jama’a ke amfani da su ko da rijiya ce kuwa.
Hanyoyin Kariya Daga Wadannan Cututtuka:
Ruwan famfo wanda hukumar gidan ruwa ta tace ta sa magani da kuma irin na kwalba da kan bulbulo daga karkashin dutse da ruwan sama da aka tara kai tsaye da ruwan rijiya mai zurfin gaske, kamar ta burtsate ko tuka-tuka, su ne za a iya cewa da wuya a samu wadannan kwayoyin cuta a ciki. Duk wani ruwa da bai shiga cikin wannan lissafi ba to ka kiyaye shi.
Sauran hanyoyin su ne:
1-A guji bayan-gida barkatai a hanya da gefen magudanan ruwa ko rijiya ko kogi kamar dabbobi. A koyi hali irin na kyanwa wadda takan tabbatar ta bizne ba-hayanta.
2-Kada a gina rijiya dab da bayan-gida, a ba da tazarar akalla kafa 50.
3-Gina gidajen ba-haya na zamani a wuraren zaman jama’a kamar kasuwanni zai rage yawan ba haya barkatai, da kusa da magudanan ruwa.
4-Saka dokar-ta-baci ga duk wanda aka samu yana bayan-gida a bainar jama’a ko yana zub da ba-haya irin na gidaje a magudanan ruwa.
5-A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha. Ruwan famfo yana da sinadarin chlorine da kan kashe kwayoyin cutar. Amma wasu lokuta bututun ruwa sukan fashe su sake gurbata da ruwan kwatami ta yadda sinadarin ma ba zai yi tasiri ba.
6-Hukumomin gidan ruwa su tabbata an tace kuma an saka sinadarin chlorine yadda ya kamata kafin a sako ruwa.
7-A guji shan kankara da ba a tabbatar daga ruwan da aka hada ta ba. Idan ya zama dole, a ribanya ledar jikin kankarar kafin a sa a ruwa mai tsabta don ya yi sanyi.
8-A tabbata an wanke hannaye da sabulu bayan an yi bayan-gida ko kuma an yi wa yara tsarki da kuma kafin cin abinci. Yawan wanke hannu da sabulu yana hana kamuwa da wadannan cututtuka kwarai da gaske. Kuma a tabbata an fara yin amfani da wani mayani kamar kara ko toilet paper bayan an yi bayan-gida, daga bisani kuma a sa ruwa.
9-Masu sayar da abinci su guji taba abin sayarwar da hannu, sai da babban cokali ko marar zuba abinci.
10-Duk matar da ba a yarda da tsabtarta ba a kiyayi abincinta.
11-A kiyaye tsabtar muhalli da ta bayan gida don kada kuda da kyankyaso su samu wurin zama.
12-A rufe duk wani abinci da abin sha da aka ci, don kada kuda ko kyankyaso ya hau.
13-Kada a ci kayan lambu irin su latas da karas da ba dafa su ake yi ba, har sai an wanke su a ruwa mai gishiri, an kuma dauraye. Ruwan gishiri yana aiki a nan kamar sabulu.
14-Da zarar an ga alamun gudawa, a samo ruwan gishiri da sukari na sachet wato ORS a hada a fara ba mara lafiya kafin a garzaya asibiti mafi kusa. Idan ba a samu ORS ba a samu gishiri rabin karamin cokali da sukari cikin karamin cokali biyar a hada a ruwa mai tsafta kwatankwacin babban kofi, a bayar a hankali har a kai asibiti.
15-Dole a tafi asibiti domin a duba maras lafiya sosai a ba shi magani ko karin ruwa saboda mara lafiya zai iya amai ya dawo da ruwan gishirin da aka ba shi. Sinadarin ORS ba shi zai tsayar da gudawa ba.

2- Zazzabin cizon sauro:
Bayan cututtukan da kan sa gudawa, an yi amanna cewa zazzabin cizon sauro shin e na biyu wajen halaka yara kanana kuma ya fi yawa a lokacin damina saboda yawan ciyayi inda sauro ke kyankyasa. Wannan ciwo kuma har ila yau bai bar manya ba. Ta macen sauro ce ke daukar wannan kwayar cuta ta saka wa mutane yayin da ta zo shan jini da dare.
Alamomin Wannan Ciwo:
1-Akwai zazzabi mai zafi. 2-Ciwon kai. 3-Wani lokaci akwai amai ko kumallo. 4-Sai ciwon gabobi. 5-A yara zai iya kawo suma idan jiki ya yi zafi sosai.
Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo:
1-Yawan sare ciyayin da ke kewaye da gidajenmu na rage kwanciyar sauro.
2-A rika tabbatarwa magudanan ruwa suna gudana sosai, ta hanyar daina zuba shara a cikinsu ko kuma rufe su ma baki daya.
3-A rika kwashe shara a kai-a kai.
4-Saka kaya masu rufe ko’ina a jiki idan dare ya yi, kamar riga mai dogon hannu da safa a kafa.
5-Yin amfani da gidan sauro irin na taga da kofa don rage shigar sauro dakunan kwanciya.
6-Yin amfani da gidan sauro yayin kwanciya.
7-Za a iya sa maganin feshi a daki amma a tabbatar ba kowa a ciki tukun, in ya sarara a bude tagogi.

3-Mura:
Sai ciwon mura. Akan samu wasu kwayoyin cuta musamman na birus masu son danshi su kawo matsala a irin wannan yanayi na damuna. An yada ta ta iska, ta hanyar atishawa, sai dai ba kamar lokacin bazara ba lokacin da gari ba danshi sai busasshiyar iska.
Hanyoyin Kariya:
1-Yawan cin kayan marmari na itatuwa masu cike da sinadaran bitaman na rukunin C, yana kiyaye wannan ciwo, ta yadda ko mutum ya sami matsalar ba zai nuna alamu ba ma a mafi yawan lokuta, tunda sindarin bitaman C yana sa garkuwar jini kaifi, wanda su kuma sukan kashe kwayar cutar.

4-Borin jini:
Bayan mura sai borin jini. Akwai mutane da yawa da kan samu kurajen borin jini a farkon damina kawai, ta yadda da zarar damina ta kankama, sai su bace. Wannan ba wata matsala ba ce tun da ba ta da wani hadari ga rayuwa, sai dai dan kaikayi. Ko a kyamis za a iya ba mutum maganin borin jini da kaikayin jiki (irinsu piriton). Mun rubuta a makon da ya shude cewa wani mai karatu ma Aduwa kawai yake ci sai su bace.