Magungunan Da Ke Karya Azumi

medical ampoules and syringe
Allura ta Jijiyar Jini 

Mallamai na addini da na kimiyya kamar likitoci da masu hada magunguna, sun sha zama akan wannan batu a kasashen musulmai irinsu Saudiya da Masar da sauransu, domin samun mafita a game da amfani da magunguna lokacin azumi, musamman ma magungunan da ba sha ta baki ake ba. A kasar nan dai ban san ko ana irin wannan zama ba.

Magungunan da ake hadiya kai tsaye wannan kowa ya san sai dai a ajiye azumi a sha su, musamman idan ciwo na cin mutum, ko kuma su a ajiyesu a ci gaba da azumi, musamman idan dole a sha fiye da sau biyu a rana. Idan ciwon mai sauki ne, kuma shan maganin bai wuce sau biyu a rana ba, ka ga a kaikaice za a iya sha lokacin shan ruwa da lokacin sahur kenan.

Ga abinda na binciko game da wannan batu: Wadanda suka hadu suka fitar da hukunci akan wannan batu suka ce magunguna a lokacin azumi idan ya zama dole a yi amfani da su, hukuncinsu yana kasuwa kashi biyu ne, da masu shiga ciki kai tsaye da masu tsayawa a wajen jiki:

 1. Magungunan da ake shaka masu bin iska: Suka ce mutum zai iya amfani da maganin shaka kamar na asma ko na wani ciwo, wadanda ke bin iska, tunda huhu suke shiga kamar yadda iska ke shigarsa, ba ciki suke tafiya ba, kuma yawancinsu a nan huhun suke zamansu ba sa bin jini.
 2. Magungunan da ake digawa a ido: Suka ce wannan ma ba laifi idan aka diga magani a ido idan ana azumi. Wato hakan ba zai karya azumi ba tunda ido ba kafa ce ta cin abinci ko abin sha ba.
 3. Magungunan da ake digawa a kunne: Wannan ma ba zai kai ga karya azumi tunda a cewarsu, da wuya maganin kunne ya gangara ya shiga ciki
 4. Magungunan da ake digawa a hanci: Suka ce wadannan in dai a sigar ruwa maganin ya zo, to kuwa idan aka digashi zai iya kwaranya makoshi daga nan hanci ya tafi makogaro ko ciki, ko an ji shigarsa ko ba a ji ba, don haka zai iya karya azumi
 5. Magungunan da ake shafawa: Su kuma suka ce ba za su iya karya azumi ba tunda akan shafa sabulu da man shafawa ko na goge baki lokacin azumi, kuma duk yawanci iyakacinsu wajen jiki.
 6. Magungunan yin dauke: Irin masu rage zogi da rage zazzabi ko rage kumburin basur, suma sun ce ba za su karya azumi ba
 7. Allurai: Wadanda ba sa iya qara kuzari, kuma ba da wani abin qarin kuzari aka yi su ba, irinsu alluran karkashin fata kamar ta masu ciwon suga, (duk da dai masana ciwon suga suna ganin mai amfani da allura ba magunguna ba, ya fi kyau ya ajiye azumi)  ko na cikin tsoka kamar na mai zazzabi, ba sa karya azumi. Wadanda ake yi a cikin jijiyar jini kai tsaye irinsu karin ruwa komi kankantarsa yawanci an fi so a hakura da azumi, domin za su iya karya shi.

Domin karin bayani za a iya tuntuvar malamai na addini ko kuma binciken littattafan musulunci kamar na Ibn Uthaimin wanda yayi dogon bayani akan azumi da magunguna, domin a daidaita wadannan ka’idoji.

 

Advertisements

MAKARANTUN FIRAMARE: TUBALIN GINA LAFIYAR YARA

SHPA da akan dauki lafiyar yara a kananan makarantunmu, musamman ma na gwamanatoci da muhimmanci sosai. Amma a yanzu saboda tabarbarewar al’amura ’yan makarantun hukuma idan aka gan su ko sha’awarsu ba a yi, ta wajen tsabtar jiki da ta kayan sa wa, balle a zo ga maganar makarantun allo. Wannan na nuni da irin yadda shi kansa ilmin ya tabarbare, domin a ka’ida an gina kananan makarantun firamare ba don ilmi kawai ba har da kulawa da mu’amala da tsabtar dalibai.

A yau mun lalubo manyan tubalai na kiwon lafiyar ’yan makarantar firamare domin tunatar da mu da malamai da hukumomin da abin ya shafa. A cikin tubalan abu daya ne ko biyu kawai muke jin labarin ana samarwa yara ’yan makaranta, shi ma don dawowar siyasa. Wannan kuwa shi ne ciyarwa lokacin ‘tara.’ Makarantu da dama a yanzu a wasu manya birane na Arewacin kasar nan an dawo da ciyar da dalibai abinci. Abin da dai kawai ba mu sani ba shi ne ko masu tsabta da gina jiki sosai ake bayarwa.

Tubalin gini na biyu shi ne samar da ilmi a kan kiwon lafiya, wanda wannan ma akwai shi. Sai kuma samar da wuraren motsa jikin. Wauraren motsa jiki a makarantunmu filaye ne kawai ba kayan wasa. Wato fili ne kawai aka ware kato guda, ba a raba an zana taswirar bangaren kowane irin wasa ba. Sai tubalin bin diddingin tsabtar kowane dan makaranta ta jiki da ta kayan sa wa, wanda da ake yi duk sati akalla sau daya a makarantun firamare. Wannan ya hada da duba tsaftar farce ko kumba, duba baki, duba tsabtar tufafi da takalma. A da duk yaron da bai cika tsabtar jikinsa ba kora shi gida ake kada ya yada wa yara cututtuka. Har yanzu a wasu kasashe sai an nuna shaidar allurar riga-kafi ma kafin ba a yara gurbin karatu, don gudun irin haka, amma a kasar nan an daina.
Wani tubali da za a ce kusan yanzu babu shi kwata-kwata a makarantun firamare shi ne dakin shan magani na sha-ka-tafi, wanda ake ajiye wa ma’aikacin lafiya sukutum. Ba makarantun firamare ba, kai har sakandare a yanzu da wuya a samu wannan.
Mun san akan samu bandakunan zagayawa, amma sam mun sani a yanzu da su gara babu su. Tun a hanyar shigar su mutane suke kicibis da kazanta.

Duk binciken da masana ke gudanarwa a kan harkar lafiyar ’yan makaranta a ’yan shekarun nan a kasar nan ba su yi nuni da ci gaba mai kyau ba a harkar kiwon lafiyar makarantu. Binciken ya hada kuma har da makarantu na kudi, inda sai dai a ce gara su da na gwamnati, amma duk tafiyar daya ce. Da fatan masu ruwa-da-tsaki za su gyara lamarin.

Hanyoyin Kariya Daga Illolin Yanayin Sanyi

A bana sai ga shi sanyi ya zo da karfin gaske a garuruwan arewacin kasar nan, ta yadda idan ba a yi tanadi ba, na barguna da kayan sanyi da kayan jin dimi, to zai iya illa. A cikinmu ‘yan Adam akwai mutane da suka fi son yanayi na sanyi, akwai kuma wadanda suka fi son yanayi na zafi, dangane da yadda jiki ke karvar canjin yanayin.  Haka ma a cikin halittu na kwayoyin cuta, akwai wadanda suka fi rayuwa a yanayi na sanyi, akwai kuma wadanda suka fi rayuwa a yanayi na zafi, akwai kuma wadanda suka fi son danshi. Misali, kwayoyin cuta na virus sun fi son yanayi na sanyi, amma na fungus sun fi son yanayin ruwa da danshi. Na bacteria kuma da dama sun fi yawa lokacin zafi.

 1. Ga wasu daga cikin matsalolin da kwayoyin cuta kan kawo lokutan sanyi:

Mura: Kwayoyin cutar da kan sa mura duka na virus ne, wadanda suka fi yawa a wannan yanayi. Suna bin iska ne mu shakesu ta hanyar kafofin numfashi. Wasu masanan kuma sun ce a’a wadannan kwayoyin suna nan a kowane lokaci amma sun fi samun karfi a lokacin sanyi. Saboda kusancin da muke da juna, da kukkule tagogi da muke, hakan kan sa mu rika yadawa juna.

Alamomin murar sun hada da zazzabi da ciwon kai, amma ba sa tsanani irin na maleriya.  Abinda ya fi bambanta su shine yoyon hanci ko cushewar hanci.

Hanyoyin da za’a bi a kare kai daga kamuwa da mura sun hada da yin nesa-nesa da mai mura. Idan kuma ta kama mutum, zai fi kyau ya bar shiga mutane na tsawon kwanaki biyu ko uku. In ya zama dole ya fita, ya rika yawan amfani da hankici ko hannun riga ya rufe fuska yayin atishawa don kada ya yadawa wasu. Sai kuma yawan wanke hannaye da ruwa da sabulu don rage kwayoyin cutar da sukan hau hannayen yayin share hancin. Mai mura ya rika yawan shan ruwa da shan abu mai yaji kamar farfesu, ko shayi mai citta ko shakar robb don kwayoyin cutar kamar basa son yaji, kuma ruwan romon da shayin kan dumama jiki.

A qasashen da suka fi mu sanyi kuma akwai allurar riga-kafin kamuwa da murar kwayar cutar virus nau’in influenza ko flu a takaice, wadda take kashe musu mutane da dama a duk shekara, musamman kananan yara da tsofaffi. Ga wadanda za su je irin wadannan kasashe a cikin irin wannan yanayi yana da kyau komin shekarunsu su karbi wannan allurar riga-kafin kafin su tafi, ko kuma da zarar sun sauka can.

Tari: Kamar mura, lokacin sanyi akan yi tari, musamman na ciwon hakarkari, wato numoniya, idan kwayoyin cuta sun fara gangarawa daga hanci zuwa makoshi da huhu kenan. Wani tari da ya fi kamari a irin wannan lokaci shine na yara ‘yan kasa da shekara biyar, da ake kira croup a likitance, saboda numfashin mai murar kan yi ta ‘kurup-kurup’ kamar na mai asma ko tarin shika,  wasu kuma kana ana hura usur, saboda maqogwaron ya kumbura. Sukan kasa cin abinci sosai. Wani lokaci hakarkari na shigewa ciki idan suna jan numfashin. Idan aka ga irin wannan, dole a kai yaro asibiti domin karbar magani da iskar oxygen, domin a wasu lokuta sai an kai ga saka musu wannan iska da magungunan shaka ta bututun iskar. Yana xaya daga cikin cutukan da ke galabaitar da yara, yayi sanadin rasuwar wasu.

Hanyoyin kariya basu wuce irin na mura ba, a rika sawa yara kayan sanyi masu aminci a kuma rika ajiyesu daki mai dumi, da kuma daina yawo da su tsakar gida lokacin sanyi.

Mura

A. Dangane da yadda jiki ke karbar canjin yanayi kuma, jikin wasu kan samu kansa a yanayi na:

Sabar fata/Bushewar Fata/Kaushi/Faso: Wasu fatarsu ta sama ke fita wata ta fito, kamar dai yadda wasu halittu suke yin saba. Wannan ba ciwo bane, yanayi ne da fata kan bi domin ta gyara kanta. Wasu kuma fatar tasu takan bushe sosai. Wasu kan samu bushewar a fuska wanda ake kira waskane. Bushewar fata ta fi kamari a kafafuwa inda akan samu kaushi da faso, a wasu lokutan ma fason ya zama ciwo. Yawan sa safar qafa mai qwari da takalma sau ciki idan za a fita, da yawan dumama kafafu a ruwan dimi da shafa man basilin sukan taimakawa mai busasshiyar fata wuce sanyi lafiya kalau

Yawan fitsari/Taurin Bayan Gida:  Shima yawan fitsari a irin wannan yanayi hanya ce da jiki ke samu domin fitar da ruwan da baya bukata a wannan lokaci. Wato in dai ba dama can mutum yana da yawan fitsari ba a lokacin zafi, to kusan yawan fitsari lokacin sanyi alama ce ta lafiyar koda. Amma kuma duk da haka ana so mutum ya ci gaba da shan ruwansa daidai wa daida, domin hakan kan taimakawa ciki da hanji narkar da abinci. Domin ba abin mamaki bane mutum ya ji ya fara samun taurin bayan gida a lokacin sanyi, idan baya shan ruwa sosai.

B. A wasu lokutan kuma wasu cutukan sun fi tashi a wannan yanayi, misali:

Asma: A irin wannan yanayi na sanyi aka fi samun mutane masu matsalar asma, kuma a irin wannan yanayi ciwon ya fi tashi ga masu ita, saboda kurar hazo. Mai asma dole ya rika sa kyalle ko takunkumi mai rufe fuska kenan a ranakun da ake hazo, kuma ya rika yawo da maganinsa na rage illar asma kamar inhaler.

Ciwon hakori: A mafi yawan lokaci mataccen hakori baya tashi ciwo sai a lokacin sanyi, ko kuma idan an sha ruwa mai sanyi. Ba sanyin ne ke jawo ciwon hakorin ba, a’a dama can kwayar cutar musaman na bacteria ta ci, ta cinye, har jijiyar karkashin hakorin ta fito. To da sanyi ya tavo wannan jijiya sai fa haqorin ya fara zogi.  A nan zuwa asibitin hakori domin cike ramin, ko ma a cire shi gaba-daya idan an ga bashi da mamora shine kawai mafita.

Bugun zuciya: Masu ciwon zuciya iri dabam-daban sun fi samun matsaloli a irin wannan yanayi domin ciwon kirji na masu ciwon zuciya da kuma bugawar zuciyar ya fi aukuwa. Wannan na faruwa ne musamman a tsofaffi wadanda jikinsu baya samar da dumi sosai, don haka jininsu kan fara daskarewa har zuciya ta tavu. Wato dai dole ne tsofaffi da masu ciwon zuciya su kasance a wuri mai dumi a irin wannan yanayi. Idan ta kama dole a fita kuma dole a yiwa sanyin shiri ta hanyar rufe ko’ina a jiki da kaya masu kauri.

Sai kiyaye irin abubuwan da ake kunnawa na jin dimi a dakuna. Hayakin itace da na makamashin kwal suna dauke da gubar carbon monoxide mai iya kisa cikin dare musamman idan tagogi a rufe suke. Wutar gawayi bata fiya hayaki ba sosai, za a iya amfani da ita. Idan aka hura gawayi a waje ya kama, sai hayakin ya lafa kafin a shigo da shi daki. A kuma kiyaye kada a sa wurin da zai iya kama wuta. Ga masu wutar lantarki, heater itace tafi.

Mu tuna da ‘yan uwa ‘yan gudun hijira wajen taimakawa da tantuna masu kwari da kayan sanyi da barguna da magunguna, a kungiyance don kaiwa sansanoninsu.

HANYOYIN KARIYA DAGA ILLOLIN CIWON SUGA GA MASU MATSALAR

Diabetic FootA wannan shafi tuni mun riga mun ga hanyoyin da ake bi wajen kare kai daga kamuwa da ciwon suga, wanda muka ce kiba ce ta fi kawo shi fiye da gado. Ga wadanda kuma aka jarrabesu da wannan matsala, bayan addu’o’i neman sauki da shan magunguna, ba haka kawai kuma za a zauna ba, akwai ‘yan dabaru a likitance da ake yi wajen rage illar da ciwon ke sawa a jiki.

Da yake mu a likitance ciwon suga in dai ya kama mutum sai an yi da gaske kafin ya bar shi, (in dai ba irin na mace mai juna biyu ba) dole ne sai ana hadawa da wadannan dabaru idan ba a so matsalar ta yi wa jiki lahani. Mun san cewa ciwon suga na iya yi wa kananan magudanan jini na wasu sassan jiki kamar na idanu, na zuciya, na qoda, na kwakwalwa, na fata da na kafafu illa saboda taruwar suga a cikinsu. Haka nan yakan iya yi wa wasu jijiyoyi na laka ma illa kamar na hanji, na dubura da na kafa.

Mun kuma san cewa shi dai ciwon suga yana faruwa ne yayin da jiki ya kasa samar da sinadarin insulin wanda kan sa jiki ya tsotse sikari ko kuma kiba ta sa wuraren da ake tsotse suga a jiki su ki aiki. Don haka idan babu wannan sinadari ko wurin tsotsewar na da matsala, suga kan taru a jini har ya kawo illa ga wadancan sassa na jiki da aka ambata. Idan suga yayi yawa a jini har buge mutum yake ya suma, haka ma idan yayi kadan, musamman a masu wannan matsala. Wato dole ne kenan sai an saisaita suga tsaka-tsaki. Duk wanda yake da iyaye ko kakanni masu ciwon suga, shima yana da kyau a riqa gwada nasa yawan sugan a kalla sau daya a shekara.

Ga masu ciwon kuma wadanda aka xora kan shawarwari ko magunguna, dole ne su bi waannan ka’idoji, kuma su riqa shan magani kamar yadda aka zayyana, domin ba makawa idan aka bi waxannan ka’idojin, za a iya rayuwa kusan kamar kowane mai lafiya.

 

Hanyoyin Kariya Daga Wadannan Illoli Sune:

 1. Bin Ka’idar Cin Abinci: Kowane mai ciwon suga dai ya riga ya san dole ya kiyayi abincin da aka sa suga na kasuwa, wato suga na gari, amma zai iya cin abincin wadanda da sugansu aka halicce su kamar kayan marmari. Wasu akan hana su cin wasu abubuwa masu sitaci irinsu doya, amma wasu ba a hana su, wannan ya danganta ne da irin yanayin jikin mutum da irin yadda magani ya karve shi. Akan bukaci su yawaita cin wake da acca da kayan ganye, da burodin alkama da sauransu, saboda su ba su da yawan suga. Duk dai abincin da aka dora mutum akai dole ya kiyaye. Hasali ma masu ciwon da yawa akan fara basu wannan ka’ida a karon farko kafin a je maganar magani. Idan suka kiyaye wannan yawanci ba sai an je ga shan magani ba.
 2. Yana da kyau mai ciwon suga ya sayi na’urar gwada sukari ta ‘glucometer’ wadda za a iya samu a manyan kyamis, sa’annan ya je a koya masa yadda ake amfani da ita, ya rika auna sugan da kansa a gida a kalla sau daya a sati idan mai amfani da magani ne. Idan kuma shi mai amfani da allurar insuli ne kusan yana wajaba a riqa aunawa a kalla sau daya a rana. Amfanin wannan shine bibiyar sugan jini domin kare duk sassan jiki daga illa, da kuma kiyaye aukuwar irin yawan suman da wasu masu ciwon suga kan yi a gida, walau idan suga yayi yawa a jini, ko kuma idan yayi qasa sosai
 1. Ga lafiyar koda, akwai wata na’ura ma har ila yau ta auna sugan da ke cikin fitsari urine dipstick wadda ita tsinke ne kawai ake dangwalawa a cikin fitsari a ga yadda zai canza kala. Suma akwai ire-irensu masu sauqi a manyan kyamis hade da robar fitsarin (tunda sai dole a roba mai tsabta ake zuba fitsarin, kuma sai zubar fitsari ta tsakiya ake tara a robar, ba na farko ba, ba na karshe ba). Amfanin wannan itace kare koda daga illar suga. Da yake mun ce koda na daya daga cikin manyan sassan jiki da ba sa son suga, da mutum ya ga alamun suga a fitsari ta hanyar wannan tsinke, sai ya garzaya asibiti a saisaita masa maganinsa, domin kuwa alama ce ta cewa suga ya fara zama a qoda. Banda wannan na gida a asibiti ma akan auna sinadarai da kan iya nuna lafiyar koda duk lokacin da mutum ya je sabunta magani
 2. Ga kiyaye lafiyar ido kuma, kamata yayi a kalla duk shekara a auna lafiyar idanun mai ciwon suga a asibiti ko da sau daya ne. Shi wannan ba wata na’ura mutum zai saya ba, a’a ko yana jin alamun matsalar gani dusu-dusu ko bashi da ita, ya kamata a ce a asibitin da mutum ke zuwa akwai vangaren ido, domin likitan sugan ya aika shi a auna idon a kalla sau daya a shekara. Idan kuma babu to dole sai ya nemi asibitin ido. Wannan zai yi matuqar kare ido daga illar yanar ido ta sukari (cataract) da kuma illar da sugan kan yi a can bayan kwayar idon (retinopathy). Idan aka ga alamar matsala da wuri an fi iya maganceta fiye da idan aka gano a kurarren lokaci, wanda hakan kan iya jawo makanta.
 3. Game da lafiyar kafa kuma, dole ne mai ciwon suga ya riqa duba kafarsa kusan duk safiya lokacin wanka, ya duba kumburi, ko canjin kala, ko wani kwarzane ko faso, ya latsa ya ji ko akwai inda ba ya jin tavi, ko akwai wuri mai zogi, domin da yawan abubuwan da ke fara shafar lafiyar qafar mai ciwon ba zafi ne ko raxaxi ake ji ba. A wasu lokutan dai akan ji raxaxin kamar na qunar wuta a tafin qafa, ko na tafiyar kiyashi, waxannan alamu ne na farko-farko ga mai ciwon suga cewa suga fa yana tava jijiyoyin laka na qafa. Idan wannan ya daina suga bai sauka yadda ya kamata ba, to sauran duk abubuwan da zasu fari ga qafar da wuya mutum ya ji alamun ciwo. A qasashen da suka ci gaba a asibitoci akwai sashen duba lafiyar kafa na musamman (podiatry), wanda har yanzu bai zo qasashenmu ba tukuna. Duk dai wata alama da mai ciwon suga ya ji a qafarsa ya kamata ya sanar da likitansa cikin gaggawa kada a je lokacin da za a ce sai an yanke yatsu ko qafa
 4. Hanyoyin kare magudanan jini na zuciya da na qwaqwalwa daga illar suga duk xaya ne da hanyoyin kare su daga maiqo waxanda muka sha zayyanawa a wannan shafi.

 

KIRKIRE-KIRKIREN ZAMANI A FANNIN KIWON LAFIYA

Daga science photos library
Daga Taskar Science Photos

Mutane masu matsalolin rashin lafiya da dama irinsu ciwon suga da hawan jini da asma da sikila da sauran ire-irensu waxanda kusan a likitance mukan ce musu mutu-ka-raba, zuwa yanzu ya kamata su san cewa bibiyar matsalolinsu da da aka fi yi a asibitoci, za a zo lokacin da suma da kansu zasu rika bibiyar kansu-da-kansu a gida. A irin wannan zamani na yanzu wanda kayan kere-kere da sabbin kirkire-kirkire basu bar kowane bangare na rayuwa ba, tuni yanzu mai ciwon suga ya san a qalla na’urar auna sugan jini, ko ma yana da tasa a gida; mai ciwon asma a kalla ya san na’urar auna karfin numfashi, ko ma shima yana da ita a gida; shima mai ciwon hawan jini ya san na’urar auna hawan jini ta tafi-da-gidanka, ko ma a ce shima yana da ita, da sauran dai ire-iren masu wadannan matsaloli.

Dole ne kowane mai matsala ta rashin lafiya mai bukatar yawan bibiya a asibiti ya tambayi likitansa ko majinyaciyarsa irin na’urorin da ya kamata ya nema domin bibiyar lafiyarsa a gida kafin ranar komawa asibiti ta yi. Bayan an fada masa ya same su, dole ne kuma ya nemi a yi masa bayani yadda ake amfani da su. Wannan ba karamar ragewa maras lafiya matsalar zarya zuwa asibiti zata yi ba, da matsalar zulumin halin lafiya da mai matsalar lafiya ke shiga idan dan wani abu kadan ya faru ga lafiyarsa kafin ranar komawa ganin likita ta zagayo. Haka nan irin wadannan dabaru za su iya rage cinkoso sosai a asibitocinmu.

Haka nan a bangaren mu masu ba da kula da marasa lafiya tuni mun san sababbin kirkire-kirkire irin na zamani da zasu sawwaka mana aiki wadanda kasashe masu arziki tuni suka fara amfani da su. Wannan ba wai ana maganar ma kayan aiki irin na gwaje-gwaje ba, wanda har yanzu suke sa wasu cikinmu tura marasa lafiya kasashen waje, ana maganar na’urori waxanda za su ajiye bayanai akan duk wasu masu zuwa asibiti akai-akai ba tare da fargabar batan fayil ba. Banda matsalar batan fayil, irin wadannan na’urori kan taimakawa ma’aikatan lafiya sanin ranakun zuwan wane da wance domin su basu takamaiman lokacin ganin likita a wannan ranar, ba sai mutum ya zo da asubahin fari ya yini a asibiti ba, wasu ma don kawai a sabunta masa magani. Akan sa ire-iren waxannan manhajoji a na’urar kwafuta wadanda kan tattara bayanan mutanen da zasu ga likita a wannan rana ta hanyar saqonni akan shafin farko da an kunna na’urar.

To ire-iren waxannan abubuwan qirqire-qirqire alfanunsu kenan ba kawai ga maras lafiya bane, har ma da masu jinyarsu. Duk da tafiyar hawainiya da harkar lafiyar kasashenmu ke fama da su, za a zo nan gaba waxannan manhajoji na zamani su kasance sune kawai abin amfani ko an ki ko an so, kamar yadda wayoyin tafi-da-gidanka suka zama wajibi a aljihun kowane mutum a yanzu.

Wadannan misalai da muka yi bayaninsu a sama kusan tsoffin kirkire-kirkire ne ma a wasu qasashe domin suna amfani da su fiye da shekaru goma da suka wuce. Bari mu duba wasu sabbin kirkire-kirkire da wasunsu ma ba su ma shigo gari ba tukuna:

Ga daidaikun mutane yawanci manhajojin kiwon lafiya a yanzu a manyan wayoyin tafi-da-gidanka ake sa su. A yanzu akwai manhajoji da mutum zai iya lodawa wayarsa wadda zai iya amfani da ita wajen motsa jiki, ta gaya masa tsawon kilo nawa ya ci yana tafiya ko sassarfa ko gudu (irinsu manhajar runstactic pro); akwai manhajojin da za su iya auna bugun zuciya (irinsu manhajar instant heart rate), akwai waxanda za su iya auna hawan jini idan mutum ya sayo kuma ya daura robar da ake jonawa wayar salula; akwai masu auna nauyin jiki; akwai masu auna xumin jiki; akwai masu auna bugun zuciyar jarirai na ciki idan mai juna biyu ta kara su a ciki; akwai mai kintatar ranar haihuwar mai juna biyun, da dai sauran ire-irensu da dama wadanda idan mutum ya samu ya bincika wayarsa in dai mai manhajar android ko ios ko blackberry os ce, ba zai rasa na zaba ba na kyauta, sa’annan akwai kuma na kudi.

Akwai kuma wadansu na’urori wadanda ba a waya suke ba sai an saya, wadanda suka dade kamar irin biron da ake amfani da shi wajen allurar insulin, insulin pen a maimakon allura maimakon allura mai zafi a masu ciwon suga . Har ila yau a bangaren allura a sabbin kirkira ana nan ana kirkiro yadda magungunan riga-kafi ba dole sai ta allura za a iya shigar da su jiki ba, wasu da yawa za kera na digon baki kamar na shan inna. Sauran na’urorin da aka kirkiro sun hada da irin karafunan da suke aika saqonni zuwa qwaqwalwa domin bawa gurgu da maras hannu ikon motsa sabbin hannayen da aka sa musu. Kai a kwana-kwana nan ma har tubarau mai sa wasu nau’in makafi gani aka kaddamar.

Ga masu aikin lafiya kuma misalan sabbin kirkire-kirkire da aka yi dominmu na lodawa a waya sune na duba bayan ido irinsu iExaminer, da cikin kunne irinsu cellscope oto waxanda ba a samu a wasu asibitocin, ko kuma ga masu son duba maras lafiya a gida ko daji inda ba kayan aiki.

Ga asibitoci ana nan ana kirkiro wata na’ura kuma ga dakunan binciken jini wadanda za su iya gwada sinadarai da dama a jikin mutum da digon jini daya kawai, ba sai an ta zukar jini a kwalabe biyu ko uku ba, abinda wasu marasa lafiya basu cika so ba. Har ila yau a bangaren binciken cututtuka, a yanzu za a iya gane masu dauke da cutukan daji ta hanyar amfani da wasu karnuka da aka horas, ta hanyar sansana jikin mutum kawai, kamar yadda akan horas da karnuka su sansano miyagun kwayoyin magunguna a filayen jirgin sama.

CUTUKAN FARCE

Akwai cutuka da dan dama da suke kashe farce, wadansu farcen kawai sukan kama, wasu kuma duk jiki ciwon kan shafa har da faratan, kuma irin wadannan akan ganosu idan aka kalli farcen mutum. Da farko dai akwai cutukan farce su kansu kamar a irin wadanda su farcensu baya fitowa yayi tsawo waje, sai dai […]

TSABTAR HAKORA

Yawancinmu bamu fiya damuwa da tsabtar haqori ba, har da ma bakin gaba daya. Tsabtar haqora tana da muhimmancin gaske domin komai yawan tsabtar bakin mutum da ya ci abinci, ya dan bar bakin tsawon awa guda bai wanke ba, to fa qwayoyin cuta ne zasu taru a ciki, su ci karensu ba babbaka (wato […]