Matsalar ‘Dannau’ A Mahangar Likitanci

A kwanakin nan ana muhawara a shafukan sada zumunta kan shin mene ne Dannau? Shin matsalar kwakwalwa ce ko kuma ta iska ce? To, da ma an dade a duniya ana samun muhawarori iri-iri game da abubuwan da ke illata mu su sabbaba mana cutuka. Akwai su kuma da dama. Duk abubuwan da muke zama da su a duniyar nan wadanda muke gani da wadanda ba ma iya gani, wadanda muka sani da wadanda ma ba mu sani ba, za su iya illata mu. Masu ilmin zamani mukan guji hada ilmomi wajen fayyace zance. Shi ya sa wasu lokuta za a ji muna cewa a likitance, saboda fassara ce kawai ta ilmin likitanci ba a hada da wani ilmi ba. Amma idan za a shiga ilmin addinai a shiga na zamani, a shiga na al’adu a kan mas’ala guda misali, za a iya samo bayanai gamsassu da dama, ko kuma a kiaye yadda za a yadasu. Misali akwai abinda a likitance za a iya yadawa amma a al’adance yadashi batanci ne.

Za a ga cewa shi ilmin addinai ya riga ya dasu, shi kuma na kimiyya da fasaha yanzu yake girma. Na al’adu kuma baya ma yake ci. A wurinmu ma’aikatan lafiya, sanin wadannan ilmomin da aiki da kowane a inda ya dace zai iya taimaka mana wajen warware mana wasu mas’aloli da dama.

Shi ilmin addinai ya sanar da mu abubuwa da dama wadanda ko ilmin zamani bai sani ba, sai yanzu ne yake ‘gano’ wasu. Ilmin likitancin zamani ilmin kimiyya ne, ita kuma matsalar kimiyya ita ce aiki da zahiri da watsi da badini ko surkulle. Don haka abinda ilmin kimiyya bai gani ba, ba zai sa shi a ma’auni ba. Kai kwayoyin cuta fa, tun shekaru aru-aru, ai ilmin addinai ya sanar da mu akwai su, amma ilmin kimiyya bai sa su a lissafi ba sai da aka fara ganinsu a madubin hangen kananan halittu na microscope kuru-kuru. Kenan da za a kirkiro madubi mai ganin iskokai, likitancin zamani zai yi kokarin danganta wasu matsalolin lafiya da sukan jawo.

Bari mu zo kan matsalar Dannau. Ta fuskar ilmin addinai, mallaman addinai sun yarda akwai shedanu da kan danne mutane wadanda ba sa addu’o’i idan sun zo kwanciya barci, a danne mutum har ya kasa motsi. Wai kar ka dauka ma a addinin Musulunci ne kawai, a’a har a addinin Katolika haka ne. To wadannan bayanai na addini da alamun da akan ji idan hakan ta faru sai ya yi kama da bayanin likitanci akan sleep paralysis. Wannan matsala ta sleep paralysis dadaddiyar matsala ce wadda tun kafin zuwan likitancin zamani akwai ta, ballantana a ce ai yanzu aka ganota. To da yake likitancin zamani kamar yadda muka fada, yana so ne ya fayyace abinda yake zahiri kawai, sai ya gaza samun ainihin me za a alakanta wannan matsala da ita, sai aka alakantata da inda ake tunanin abin ke faruwa wato kwakwalwa. To dalilin kenan da muke ganin likitancin zamani bai alakanta matsalar Dannau da iska ba. Amma kuma wannan ba yana nufin ko me ya taba kwakwalwar mutum a ce iska bane.

Illolin Makaman Nukiliya

Su dai makaman nukiliya suna daga cikin makaman kare-dangi, kuma ana kiransu haka ne saboda irin barnar da suke yi su al’umma da dama suke illatawa ba a mutum adya ko biyu ba. A makonnin baya ne fada ya barke tsakanin kasashe da ake ganin suna da wadannan makamai.

Wani makamin Nukiliyar Kasar Rasha


Kasashen da ake ganin sun mallaki makaman nukiliya su ne Amurka da Rasha da Ukraniya. Akwai ma Birtaniya, Sin, da Koriya ta Arewa, sai Faransa da Israila. Akwai kuma Indiya da Pakistan, sai kasar Iran. Ukraniya da ake gani kamar karamar kasa bincike ya nuna tana makaman nukiliya, sai dai an ce ta ba hukumar da ke kula da makaman wato IAEA ‘ajiya’. Ana tsoron barkewar yaki tsakanin kasashe masu makaman nukiliya saboda kada su harba su.


Ba kamar sauran makaman yaki irinsu bindiga mai harshashi da nakiyoyi da bama-bamai ba, su wadannan makamai ko ba a saita mutum da su ba idan aka harba su a sararin sama to duk wanda yake yankin da abin ya faru yana iya mutuwa ko samun illa a lafiyarsa.

A wani faifan bidiyo da na gani a kwanakin baya, wanda a ciki aka yi hira da tsofaffin sojojin Ingila da na Amurka sukai aikin gwajin wadannan makamai a tsibirai daban-daban (domin a tsibirin da ba kowa ake gwadasu), dukkansu sun yi amanna dan Adam bai taba kera wani abu mai hadari fiye da makamin nukiliya ba. Suka ce a lokacin idan sun je harba makaman, duk da cewa suna nesa da wurin da aka harba, nisan da aka yarda babu illa idan aka tsaya, akan ce musu da sun harba su juya baya, su sa hannayensu su rufe fuskokinsu na tsawon mintuna. Amma suka ce ko sun rufe ido hasken da ke tashi a wurin yakan sa duk da idanunsu a rufe ne suna ganin kashin hannayen da suka rufe idanun nasu da su. Zafin tiririn da sukan ji kuwa, suka ce suna ji kamar wani mutum ne da wuta ta kama ya zo ya ratsa ta jikinsu ya wuce. Suka kara da cewa duk abokanan aikinsu da suka rigamu gidan gaskiya bayan sun yi ritaya, cutukan daji ne yawanci ke ajalinsu saboda wannan aiki da suka yi a baya.


Babu babban misalin makami mai guba da aka taba amfani da shi a wurin yaki wanda ya girgiza ita kanta wadda ta harba kamar makamin da Amurka ta harba a garuruwa biyu na kasar Japan a shekarar 1945 wato garuruwan Hiroshima da Nagasaki. Makaman a tsakiyar gari kawai aka jefa su, amma kan gari ya waye an ce mutane fiye da dubu dari ne suka mutum har lahira a garuruwan biyu, wasu dubu darin kuma cikin makonni da yin abin. Wannan ta faru ne saboda karfin girgizar garin da bam din ya sa, da karfin tiririn maganadiso mai kona jiki tun daga fata har cikin bargo da ake kira gamma radiation, wanda idan bai kashe mutum a lokaci guda ba, zai iya janyo rikidewar kwayoyin halitta na jiki ko su jawo ciwon daji. To abinda ya faru ga sauran mutan wadannan garuruwa kenan wadanda bam din bai halaka ba.

Allah Ya cigaba da karemu daga irin wadannan bala’o’i, Amin.

Shiga Tashin Hankali da Yada Labaran Tashin Hankali Na Iya Taba Lafiyar Kwakwalwa

A cikin ‘yan kwanakin nan da tashe-tashen hankula suka yawaita a kasar nan, ana samun yawan yada hotuna da bidiyo na abubuwan ta da hankali ta kafafen sada zumunta. Masu tura wadannan hotuna suna fakewa da cewa sai an yada ne abin zai fito fili mahukunta da jama’a su sani. A’a ba haka bane, idan aka fada ta kafafen yada labaru da aka saba, hakan zai isa ga jama’a, su kuma hukumomi sun ma fi mu sanin abubuwan da ke faruwa. Su kafafen yada labaru da aka saba da su, a ka’idarsu ba sa yada irin wadannan hotuna da bidiyo. Don haka ne muke so mu ja hankalin masu wannan dabi’a da su sani cewa ba kowa ne fa ake so ya ga irin wadannan hotuna ba. Su kansu masu yadawar basu sani ba abin ka iya shafar tunaninsu nan gaba.

Ba tun yau ba masana lafiyar kwakwalwa suka san cewa yawan gana azaba, da yawan shiga tashin hankali na iya samar da ciwon kwakwalwa kamar su ciwon damuwa na depression. Sa’annan akwai ciwon kwakwalwa na musamman wanda tashin hankali da yawan shiga tashin hankalin, da yawan ganin tashin hankalin ke haddasawa mai suna post-traumatic stress disorder, PTSD wanda ke nufin ciwon kwakwalwa wanda ya auku bayan an shiga tashin hankali na rayuwa kamar yunwa ko fari ko yaki, da sauran kayan hadin rashin kwanciyar hankali kamar yawaitar satar mutane. Yanzu a kasar nan ana samun tashe-tashen hankula, domin akwai yunwa da kashe-kashe, da sace-sacen mutane, amma muna godewa Allah ba a shiga fari ba, ba a shiga babban yaki ba, amma ko yunwa kadai aka bar al’uma cikinta ta ishesu tashin hankali ta jawo musu ciwon kwakwalwa balle a hada da kashe-kashe da yawan ganin kashe-kashen da sace-sacen jama’a.

An kiyasta cewa kashi 39% cikin dari na ‘yan gudun hijra a kasar nan, musamman ma wadanda suka fito daga Arewa maso Gabas, suna da alamu na ciwon damuwa, kashi 18% cikin dari kuma suna da tabbataccen ciwon damuwa. Shi kuma ciwon PTSD kusan rabin ‘yan gudun hijrar suna da shi, inda ya kai kashi 42% cikin dari. Wannan a ‘yan gudun hijrar da ke Arewa maso Gabas kenan da suka dade suna cikin tashin hankali wato fiye da shekaru 10. To idan ba a yi hankali ba, mutanen da ke cikin tashin hankali a yanzu a Arewa maso Yammacin kasar nan su ma za su iya shiga wannan kiyasi. A yanzu dai ba a yi wani bincike na ku zo mu gani ba a can tukuna, amma idan aka bari ta ci gaba, to sai dai inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.

Wadanda Allah Ya sa wannan abu bai shafesu ba, kada su ma a rika tayar musu da hankali ta hotuna da bidiyo, sanarwa da baki ko tura kanun labarin ya wadatar. Da wannan ne muke daukar wannan dama muke roqon masu yada wadannan hotuna da bidiyo da su yi hakuri daina, domin su kansu barin hotunan da bidiyon a wayoyinsu suna yawan kallo zai iya bata musu tunani. Mu ma da an turo mana kamata ya yi kada mu kalla, mu yi sauri mu goge kada mu kara turawa wasu. Ba a san wa abin zai taba wa kwakwalwa ba a cikinmu.

Ga sauran hanyoyin da za mu bi mu kiyaye kanmu:

 1. A dage da addu’o’i domin yawan addu’o’i wato meditation an tabbatar magani ne da kariya daga ciwon kwakwalwa, gami da kariya daga shiga tashin hankali
 2. Muna kira da al’uma musamman na Arewa maso Yammacin kasar nan cewa kafin ita ma ta zama kamar Arewa maso Gabas, mu hadu mu dauki mataki na gaske kuma cikin sauri a tsakaninmu mu al’uma, ba matakin surutu da kumfar baka ba, tunda abu ya gagari hukumomi.

Gwaje-Gwajen Lafiya Kafin Aure

Ana so a rika yin aune-aune da gwaje-gwajen lafiyar ma’aurata kafin a daura aure. Wannan gwaji a likitance shi muke kira da pre-marital screening, kuma a yanzu a kusan ko’ina a duniya, har qasashen musulmai na Larabawa ya zama doka ta wajibi wadda dole sai an cika kafin a daura aure.

Gwaje-gwajen lafiya kafin aure na daya daga cikin manyan hanyoyin da ake bi wajen kiyaye aukuwar cutuka, musamman a mata da kananan yara. Tunda an ce riga-kafi ya fi magani, idan aka rungumi wannan hanya ta riga-kafi za a iya shawo kan wasu manya-manyan cutuka da mata da yara kan samu wadanda za mu lissafosu a gaba.

Awon jini shi ne ginshiqin wannan gwaji. Ana auna cutuka da dama a ma’auratan, amma su cutukan sun kasu kashi biyu: Cutukan gado na tangardar kwayoyin halittu na gado na DNA wadanda uwa da uba za su iya sa wa dansu, da kuma cutukan da kwayoyin cuta za su iya sa wa, wadanda miji ko mata za su iya sa wa junansu, har ma idan ba a yi sa’a ba su sa wa ‘ya’yansu. A kashi na farko ana duba kwayoyin halittu na cutuka kamar na amosanin jini wato sikila da sauran tangardar kwayoyin halittun gado irinsu ciwon maloho da sauransu. Amma da yake ciwon sikila ya fi yawa, kuma ya fi yi wa yara illa da saurin kisa, an fi ba da karfi da muhimmanci a kansa. Wannan gwaji na sikila sunansa ‘Hb Genetype’, kuma a yanzu wajibi ne ma’aurata sai sun yi shi. A kashi na biyu kuma ana auna cutuka ne wadanda kwayoyin cuta sukan sa, cutuka irinsu kwayar kanjamau kamar yadda ka ce, gwajin da muke kira ‘HIV Screening’ sai awon ciwon

hanta na hepatitis B, wanda muke kira Hepatitis B Screening’ sai na ciwon tunjere ko syphilis, awon da ake kira VDRL. Akwai saura amma wadannan su ne manyan.

Wadannan aune-aune a yanzu sun zama tsari na dindindin a asibitocinmu wadanda ake yi lokutan awo, amma ba su zama tsari na dindindin ba a masallatai da majami’u inda ake daura aure ba. Wannan shi muke so a canza, domin ina amfani a zo awo a ga mace da wadannan cutuka? (Amfanin kawai shi ne, watakila a ceci danta, amma ba ita ba). Amma idan aka yi kafin aure an kiyayeta da ita da ‘ya’yanta. Tunda misali idan aka ga akwai mai ciwon hanta a tsakanin ma’aurata alluran riga-kafi kawai za a yi wa wanda bai da ciwon a cikinsu, shikenan an kare kowa.

ILLOLIN TABA SIGARI

Sigari   Tarihi ya tabbatar da cewa an dade ana zuka ko taunawa ko shakar taba a duniya, domin kusan shekaru dubu hudu kenan da fara amfani da taba. Sai a ‘yan shekarun baya ne, kamar shekaru dari daya da suka shude sa’annan aka fara alakantata da cututtuka irin na zuciya da na huhu da ciwon daji iri-iri.

Duk da cewa a kasarmu da sauran kasashen Afirka matsalar bata yi kamari sosai ba kamar sauran sassan duniya, an yi kiyasin a kalla rabin mazan duniya suna sha ko sun taba shan taba sigari. A mata matsalar bata kai haka ba domin kashi goma ne kawai cikin dari na mata ke sha. Yawanci mutane na fara sha ne tun a kuruciya daga shekaru sha biyar misali zuwa sama, kuma ana koya ne a wurin iyaye ko abokai ko dai na makaranta ko na majalisa. Da yake aikin babban sinadarin cikinta wato nicotine a kwakwalwa yake, nan da nan kwakwalwar takan ji dadi kuma ta nemi kari, ta haka har mutum ya saba. Wasu kalilan wadanda kwakwalwarsu bata jin dadin sinadarin a nan take suke barin shanta, wato ba kowa bane sigari ke wa dadi.

Da an zuki hayakin sinadarin nicotine ke tafiya huhu, a nan sai magudanan jini su tsotse shi su rabawa lakar jiki, da kwakwalwa, nan da sai mutum ya ji nishadi. Bayan sinadarin nicotine sauran guba da ke tattare a cikin hayakin, irinsu benzopyrene, da formaldehyde, da cadmiumda nickelda arsenicda nitrosamines,  su kuma manyan cututtuka irinsu ciwon daji suke kawowa. Amma an tabbatar da cewa taba ta taunawa tunda babu hayaki, ba ta kai mai hayaqi illa ba. Duk da haka ita ma takan iya sa ciwon kansa ko sankara.

Ga cututtukan da aka tabbatar taba sigari kan jawosu

 1. Sankarar baki da makoshi
 2. Sankarar Huhu
 3. Sankarar tantanin fitsari na mara
 4. Bugun zuciya
 5. Kumburin Huhu na COPD
 6. Bugun jini a kwakwalwa mai sa mutuwar barin jiki

Akwai wasu musabbabai ban da sigari da kan jawo wasu daga cikin cutukan da aka lissafa, kamar bugun zuciya da mutuwar barin jiki kiba da hawan jini suka fi kawosu, sa’annan shan sigari. An kiyasta duk shekaru mashaya sigari miliyan bakwai duk shekaru.

Hanyoyi da dabarun rabuwa da taba sigari suna da yawa kuma sukan taimaka wajen kiyaye wadannan cutuka da muka lissafa a sama. Hukumar Lafiya ta duniya ta tabbatar da cewa hukumomi da daidaikun mutane masu sha, duka akwai rawar da zasu iya takawa wajen ganin karshen wannan bala’i wadda kamfanonin sarrafata ne kawai suke moruwa da ita. Wadannan sun hada da:

Bangaren Hukumomi:

 1. Sakawa sigari Haraji mai tsauri: Wannan zai iya sa sigari ta yi tsada. Hakan kan sa mutum ya rika tunanin yawan kudin da yake kashewa a kanta, domin ya rage. Hasali ma wannan tsadar ce ta sa kasashe marasa arziki ba su kai masu arziki shan taba ba.

 

 1. Saka dokar hana shan taba a bainar jama’a: Kasashe da dama sun gwada wannan hanya kuma sun fara ganin moriyarta domin zama ma da madaukin kanwa yana kawo farin kai, wato masu zama inda ake shan sigari da yawa su ma suna cikin hadari kamar na masu sha.

 

 1. Kamfe ta kafofin watsa labarai kamar irin wadannan mujallu, da gidajen radiyo da talabijin, da manyan fastoci a garuruwa da kauyuka a wuraren taruwar jama’a kamar kasuwanni, asibitoci, da sauransu da yaren da mutanen garin ke fahimta, da hana tallanta ta wadannan kafafe

 

A bangaren daidaikun masu sha:

 1. Gudunmowar iyaye: Da yake a kuruciya yawanci mutum kan fara shan sigari, ya kamata iyaye maza da mata mu rika kula da abokan ‘ya’yanmu. Illar itace akwai alaka mai karfin gaske tsakanin shan taba sigari da shaye-shayen sauran muggan kwayoyi a tsakanin samari. Akwai alamu da ake gani a abokai kamar duhun lebba da tafin hannuwa da jan idanu da akan gane mashayanta.

 

 1. Gudunmowar mata: Sanin wasu ne cewa tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama a kwanaki ya sanar da rabuwa da sigari saboda nacin da matarsa ta rika masa a kan ya bari. Wato kenan in dai uwargida ta kafa kahon zuka a kan maigidanta zai iya barin sigari, ba don komai ba don har ita ma idan yana sha a gidanta tana cikin hadari da ita da yaranta

 

 

 1. Gudunmowar ma’aikatan lafiya: Dole mu ma ma’aikatan lafiya mu ci gaba da wayar da kan jama’a akan wannan matsala, kuma mu guji shan sigari idan muna sha, musamman a bainar jama’a domin mun san akwai masu sha kalilan a cikinmu. Illar ita ce ba mu san iya mutanen da suke iya koyi ko nuni da dabi’un ma’aikacin lafiya ba

 

 1. Canjin ra’ayi: Haka kawai mutum zai iya yin ra’ayi barin sigari kuma ya bari nan take ba tare da wata matsala ta faru ba. A lokutan azumi an fi samun damar yin hakan. Wasu idan suka yi irin wannan canjin ra’ayi tashi guda sukan sha wahala saboda sabo da sinadarin nicotine da kwakwalwarsu ta yi.

Wasu kuma ba sa samun wata matsala.

 

 1. Musayar sinadarinNicotine: Ga wadanda suka samu matsala saboda tsaida sinadarin nicotine tashi guda kamar wasu alamu a jiki na rashin lafiya da sa wa kwakwalwa alamun dan tabin hankali na wani lokaci, akan taimaka musu da musayar sinadarin ta hanyar cingam ko alewa ko lika sinadarin a kan fata. Wadannan sinadarai an rage karfinsu ta yadda ba za su cutar ba sosai. Mutum na sa wa yana ragewa a hankali har a zo a tsayar gaba daya. Idan ana amfani da dayan wadannan mutum ba zai ji kwadayin sigari ba sosai. Ana iya samu a manyan kyamis-kyamis

 

 1. Magunguna: Idan wadannan hanyoyi sun gagara kuma mutum yana da ra’ayin daina sha, to akan iya taimaka masa da wasu magunguna masu aiki a kwakwalwa amma sai an je wurin likita ya rubuta.

 

BAYANI AKAN CIWON NUMFASHI NA CORONA

Kwayar Corona

K’wayar Cutar Corona

A ‘yan makonnin nan ne muke ji a labarai cewa wata irin mura sabuwa fil mai zafin gaske kuma mai saurin yad’uwa ta b’ulla a k’asar Sin. K’wayar cutar da kan sa wannan mura sunanta Novel Corona wato sabuwar k’wayar corona wadda a karon farko ne take kama mutane, kuma tana kama da ta SARS domin kuwa dukansu k’wayoyin virus ne wad’anda akan d’auka daga jemagu. Kun san a k’asar Sin ana shan dabgen jemagu. Wato ita wannan k’wayar cuta ta samo asali ne daga jemagu. Daga wad’annan dabbobi ne cutar kan shiga jikin d’an Adam. Ana yad’ata ta iska sai ta shiga hanyar numfashi idan mai ita ya yi tari ko atishawa.

To had’arin da ma shi ne, ita sabuwar k’wayar cuta wadda ta taso daga dabbobi kuma take yad’uwa a cikin mutane tana zuwa ne a matsayin annoba, wato idan ta b’ullo ba mutum d’aya take kamawa ba. To sai aka yi rashin sa’a ita wannan ba ma gari d’aya kawai take kamawa ba, duka duniya ta shiga domin tana yad’uwa ne kamar wutar daji ta hanyar mutane masu shige da fice a k’asashen duniya. Ga shi ba mu da riga-kafinta (ba a ma santa ba ballantana a k’irk’iri allurar riga-kafinta) don haka jama’a da dama yake kwantarwa, wasunsu kuma ba sa kai labari saboda ciwon ba shi da magani.

A wannan kafa mun sha fad’in cewa duk wani ciwo wanda wannan k’waya ta virus kan kawo wuyar magani gareta, irinsu ne ke kawo k’anjamau da bak’on dauro wad’anda har yau ba a gano maganinsu ba.

A yanzu haka dai maganar da ake ta kama mutane kusan sam da 500,000 kuma ta halaka 26,000. Kuma a halin da ake ciki an ce ta shiga kasashe kusan 200 har da k’asashenmu na Afirka.

Abinda mutumin da ya kamu da wannan ciwo zai fara lura da shi shine ciwon mak’ogaro sai ciwon jiki da kasala da zazzab’i mai zafi, sa’annan sai tari, a fara jin hanyoyin numfashi sun rirrik’e. A wasu lokuta ana samun gudawa. Don haka duk wanda ya ga wani da irin wad’annan alamu dole ya taimaka ya sanar da hukumomin lafiya mafi kusa domin a tantance irin ciwon, amma kada ya kusanci mai matsalar. Idan ciwon ya yi tsanani yana kama hanyoyin numfashi musamman huhu, inda yakan hana numfashi. Ta haka ne wad’anda ke mutuwa suka mutu.

Hanyoyin Kariya

To da yake annobar yad’uwa take kamar wutar daji dole ne muma mu d’auki matakan k’aiyade shige da fice zuwa k’asar Sin da ma duk k’asar da aka samu wannan ciwon, na d’an wani lokaci har sai abubuwa sun lafa, kamar yadda sauran k’asashen duniya suka fara aiwatarwa.

Duk da dai ba mu isa mu hana mutanen wata k’asa d’abi’u da al’adunsu ba, muna sa ran hukumomin lafiya na duniya za su tsaya kai-da-fata wajen ganin an bar shan farfesun jemagu a k’asar Sin, da ma ciye-ciyen namun daji iri-iri da suke yi, domin cutukan da ke jikinsu Allah-kad’ai ya san iyakacinsu.

A rage fita, a irin wannan lokaci na annoba, a lazimci zaman gida ko na wurin aiki kad’ai. Idan ta kama dole a fita kada a kuskura a tab’a komai sai an sa safar hannu. Sai yawan tsabtar hannaye wato wanke hannaye da ruwa da sabulu ko da man spirit na tsawon rabin minti duk lokacin da aka fita aka dawo, sai nesa-nesa da jama’a da gujewa shiga taro. Yawan shan ruwa na sa mak’oshi ya jik’e ya hana k’wayoyin cutar lik’ewa a mak’oshi. Sai tsabtar muhalli, da bibiyar labarai da shawarwarin ma’aikatan lafiya, su ne manyan hanyoyin da a d’aid’aikunmu za mu iya yi mu kiyaye kanmu daga kowace irin annoba.

ZAKI DA MAIKO

ZakiZaki da maiko suna da amfani a jiki. Sai zaki da maiko sun yi yawa a jiki ne yake zama illa. Wato abin ne yana da ‘yar sarkakiya; idan baka ci ba, akwai matsala, idan ka ci da yawa ma akwai matsala,kenan sai an daidaita su. A kimiyyance komai ana sonsa saisa-saisa ne, kuma har zaki da maiko; idan suka yi kadan jiki yakan bukacesu, idan kuma suka yi yawa nan ma har ila yau jiki zai yaki wannan yawan. Dole sai mutum ya gano yadda zai saisaitasu don lafiyar jikinsa. Dalilan da kan sa dole a ci ko yaya ne, su ne cewa wasu sinadarai da jiki ke bukata a kowace rana domin aikin yau da kullum, kamar bitaman na rukunin A, akan samesu a kayan zaki ne, wasu kuma sinadaran kamar irinsu bitaman ajin A, da D, da E, da K ana samunsu a abinci ne masu maiko.

Yawanci dabarar da likitanci ya kawo mai sauki ta saisaita cin zaki da maiko ita ce – a ci daidai misali, amma a biyo bayan cin da konasu ta hanyar motsa jiki, gami da cin kayan ganye da na itatuwa. A wasu lokuta idan wadannan biyun suka gagara, kuma zaki da maikon suka zo suka yi yawa a jiki, to fa sai an ba da magungunan konasu. Za a iya ganin wannan a mai ciwon suga (inda ake ba su magungunan kona zaki) da mai ciwon mummunar kiba (inda akan ba su magungunan kona moiko da kitse)

Wato idan aka ci zaki da maiko, jiki zai tsotsi abinda yake bukata to amma sauran ajiyesu zai yi. Idan ana so kada jiki ya ajiyesu sai dai kenan a ci kadan, sa’annan a kona ragowar ta hanyoyin da aka fada a sama. Domin wannan ajiyar ce sanadiyar cutukan zamani irinsu mumunar kiba da hawan jini da ciwon suga da na sanyin kashi na gabobin jiki da sauransu. Idan da za a lura lafiyar

 1. Mutum mai cin zaki da maiko wanda ba ya konasu ba daya take da
 2. Mutum mai ci mai kona ragowar ba. Haka nan lafiyar wannan na biyun ba daya take da
 3. Mutumin da ba ya cin zaki da maiko kwata-kwata ba.

Kun ga kenan an kasa mutane kashi uku ta bangaren cin zaki da maiko. Idan da zan zabi wanda zai fi lafiya a cikinsu, mutum na biyun zan zaba.

Idan dai mutum ya kasance a aji na biyu to ba sai ya nemi wani maganin zaki da maiko na asibiti ba, ballantana wanda akan ji ana yawan talla a titi.

Wadanne al’adun jego ne ke illa ga lafiya?

A likitance akwai wasu al’adu na jego masu amfani ga lafiyar mai jego, akwai kuma wadanda ba su da wani amfani. Kai akwai ma wadanda kan yi illa ga lafiya. Abubuwan ma ai yanzu da sauki domin zamani ya zo ya kawo wa masu jegon sauki sosai.

A al’adance da zarar mace ta haihu akan ba ta tafasasshen ruwa da ganyen darbejiya ta je ta yi wanka – wankan jego. A kimiyyance zuba ruwan zafi mai zafi haka kan iya buda hanyoyin jini, karfin bugun jini ya sauka, wanda kan sa matan jin jiri a yayin wankan, wasu ma su fadi su suma. Don haka kenan maimakon ruwa tafasasshe, a likitance sai dai a sa wanda ba tafasasshe ba kamar mai dimi sosai.

Bayan an yi wanka akan hada wa mai jego dauri ta sha, wanda akan ce ruwan maganin kan karawa mai jego da jariri kwari. Wasu ma sukan hana mai jego ma shan kowane ruwa sai dauri. To mu dai a likitance ba mu san shan ruwa na da matukar muhimmanci. Ta bangaren dauri kuma ba mu da masaniyar wadanne irin hadi akan yi wa ruwan maganin ba ballantana mu san illa ko alfanun hadin. Bayan nan wasu kan hada kunun kanwa a ba mace ta rika sha a kullum. Kanwa a kimiyyance gishiri ce domin tana da sinadarin sodium mai yawa, wanda zai iya sa hawan jini ko ya ta’azzara shi. Ba za a hana shan kunun kanwa ba tunda ko muma ma’aikatan lafiya mukan taba. Wato kenan a likitance za a iya sha jefi-jefi amma ba kullum ba ko kuma a sha na tsamiya.

Akan kuma yi yaji a rika ba mai jego tana sa wa a abinci domin karin dandano. A wancan lokacin da aka kirkiro da al’adar babu abubuwan da za su karawa abinci dandano shi ya sa akan yi wannan. Shi yaji ba shi da wata illa idan ba ga masu ciwon olsa ba, yana ma da sinadarin vitamin C don haka shi ma a iya ci jefi-jefi. A yanzu kam saboda zamani akwai kayan dandano da dama don haka an rage.

Sai al’adar hadawa mai jego farfesu da naman suna. Wannan al’ada ko a likitance ita ce muke ganin ta fi kowanensu alfanu, domin kuwa yawan shan farfesun karin lafiya ne ga mai jego da jaririnta.

Wasu ma sukan ma hana mai jego fitowa waje bayan haihuwa na tsawon mako guda idan banda fita bayan-gida. Wannan al’ada kwata-kwata babu alfanu in dai mace za ta iya yawonta. A barta ta rika fitowa da hantsi tana samun sinadarin vitamin D na hasken rana.

 

 

KWARI MASU MANA ILLA GA LAFIYA

KwariWasu kwari na gida da na daji na daga cikin manya-manyan halittu masu yada mana cutuka. Suna yin haka ne ta hanyoyi daban-daban yayin da suka yi cizo ko kuma suka hau abinda mukan ci ko mukan sha. A masu cizon wasu sukan sa mana kwayoyin cuta a lokacin da suka yi cizon, wasu su sa dafi (kamar kudan zuma), wasu kuma ba sa saka wata kwayar cuta illa dai su yi ta zukar jini har ma su iya sa ciwon karancin jini idan ba farga da wuri ba. Ya kamata mu san wadanne kwari ne wadannan domin mu gujesu.

Bari mu fara duba masu yada cutuka yayin cizo, kafin mu zo kan masu yada cutuka ba tare da cizo ba, sai kuma mu karkare da masu cizo don kawai shan jini.

Sauro: Wato lange-lange mai ramar keta, shi ne babban mugun a cikin kwarin gida masu saka mana cututtuka. Kusan kowa ya san sauro shi yake kawo mana ciwon zazzabin maleriya, wanda ke kashe miliyoyin mutane duk shekara, yawancinsu yara kanana. Abinda wadansu basu sani ba dai game da sauro shi ne cewa banda ciwon zazzabin maleriya, zai iya sa ciwon zazzabin shawara na yellow fever da ciwon zazzabin zika, da ciwon zazzabin Dengue da ciwon tundirmi na filariasis da ma wasu da dama. Don haka a kiyayi sauro.

Kudan Tsando: Wanda ake kira tsetsefly shi ma yana sa wa mutane da dabbobi musamman shanu a irin kasashenmu na Afirka, shi ya sa aka fi samun ciwon tsakanin makiyaya. Yana sa ciwon kwakwalwa na sammore da fulatanci wato sleeping sickness da Inglishi, mutum ya ji ba ya tabuka komai sai yawan barci.

Kwaron Filfilwa: Wanda ake cewa blackfly ko bakin kwaro shi an fi samunsa a garuruwan kudu a kusa da koguna masu gudu. Shi kuma shi ne ke sa ciwon dundumi (makanta) da tundurmi na onchocerciasis (kumburin kafa). Don haka duk wanda ya je kurmi cikin qungurmin dazukansu sai ya kiyaye cizon kwari don kada su sa masa irin wadannan cutuka.

Kaska: Kaska ba dabbobi kadai suke wa barna ba. Kwari ne da kan sha jinin mutane tare da sa musu kwayoyin cuta daban-daban tun daga na bacteria har na virus irinsu zazzabin typhoid da na ciwon Lyme disease wanda ke sa wasu irin kuraje.

Quma: Kwari ne masu kama da kwarkwata, kuma su ma suna shan jini sosai. Su ake kira flea da Inglishi. Kwari ne da ke yada cutuka na bacteria masu sa annoba. Su aka alakanta da wata babbar annoba a tarihi (wadda aka kira bubonic plague) da ta yi sanadiyar salwantar rayukan miliyoyin mutane a tarihi a yankin Nahiyar Turai shekaru dubu da suka wuce saboda suna bin beraye suna kwaso cutukansu suna bazawa jama’a.

 

Sai kuma masu yada cutuka idan suka tava kayan abincinmu. Wadannan sune:

Quda: Shi ne na biyu mai yada cutuka da dama bayan sauro a irin kasashenmu masu zafi. Shi ne ummul-haba’isin cutuka irinsu zazzabin typhoid da ciwon amai da gudawa na kwalara da na atini.

Kyankyaso: Da dama ba a san cewa duka cutukan da kuda kan iya yadawa kyankyasai ma za su iya yadawa. Don haka a yi hankali sosai da kyankyasai.

 

Bari kuma a duba kwari masu shan jini. Wadannan sun hada da:

Kwarkwata: Ba kamar kudin cizo da kwaron kazwa ba, kwarin kwarkwata za su iya kama kowa, mai tsabta da maras tsabta. Su ne qwarin da suka fi sa kaikayin kai ga yara ‘yan mata, musamman ‘yan makaranta, fiye ma da amosanin ka, a wasu lokutan ma har da manya mata. Maza da yake a yanzu zamani ya zo muna yawan aske kawunansu, an bar tara suma Afro, abin yayi sauqi sosai a tsakaninmu. Kwarin sukan shiga kan yarinya ne daga wata zuwa maras ita, kamar a wurin wasa, kamar misali a zaman aji na makaranta ko ta musayar kallabi. Kwarin idan suka shiga kai jini suke zuka. Kusan a kididdiga, a duk yara mata goma sai an samu a kalla daya mai kwarkawata, wato a aji mai ‘yan mata hamsin akan samu a kalla biyar masu matsalar, kuma ba wuya su sa wa na kusa da su.

Kudin Cizo: Su ne wadanda aka fi gani a kayan shimfida. Ana iya samunsu a kasashe da dama a duniya, tun daga kasashen nahiyar Amurka da nahiyoyin Turai da Asiya. Yawanci mutane ke yadasu daga wannan wuri zuwa wancan a cikin jakunkuna da kayansu. Don haka ba abin mamaki bane a samesu a gadon manya-manyan otal-otal, da na fitatttun wuraren shakatawa, kuma a iya kwasarsu a kai gida ba a sani ba. Abinda ya sa ake iya daukarsu da yadasu shine cewa sun iya buya, domin da wuya a gan su da rana, don sukan iya shigewa cikin yadin katifa ko kalmasar zanin gado, ta yadda sai duhu yayi kafin su lallaba su fito, su fara cizo suna shan jini. Wannan cizo zai iya sa wurin ya fara kaikayi ya canza kala, sai dai bai kai cizon kuma saka kaikayi ba. A kasashen Kudancin Amurka irinsu Mexico, kudin cizo za su iya yada kwayoyin cuta masu sa ciwon sammore da muka yi magana da fari

Kwarin Kazwa: Kwari ne masu kama da kwarkwata ko kudin cizo, sai dai saboda kankantarsu, su ba a iya ganinsu da kwayar ido. Matsalar itace idan kwarin da ke kawo kazwa suka shiga gidan mutum, sai an yi da gaske kafin su fita, don haka za a ga ba mutum daya kawai sukan kama ba, kusan duk mutan gidan. Sun fi nunawa a yara saboda rashin karfin garkuwar jiki. Manya masu kwarin garkuwar jiki ba su cika nuna kuraje da kaikayi ba idan kwarin suka shiga karkashin fatarsu. Don haka su ma manya za su iya zama sila wajen yadawa yaransu wadannan kwari. Wato a wasu lokuta ba yara ne ke kwaso ciwon ba, manya ne ke yadawa yara. Kwarin kazwa kan iya kama kowane jinsi, fari ko baki, mai kudi da maras shi duka, sai dai ta fi kama maras shi inda akan samu cinkoson wurin kwanciya.

Masu sa dafi su kuma sune irinsu kudan zuma da zanzaro da kunama da cinnaka da wasu nau’i na gizo-gizo, duk da cewa dai kunama da gizo-gizo a kimiyyance ba kwari bane, kuma sune idan suka sa wa mutum dafi zai iya masa illa sosai idan ba a je asibiti da gaggawa ba.

 

KYAMIS BA ZAI MAYE GURBIN ASIBITI BA

Kyamis ba zai maye gurbin asibiti ba, domin shi wuri ne na sayar da magunguna kawai. Su ma’aikatan kyamis iri biyu ne, akwai masu ilmin magani na digiri masu lasisi, wadanda za su iya rubutawa da sayar da kowane irin magani ne a duniya, akwai kuma wadanda aka ba horo na musamman kawai akan sayar da kananan magunguna kamar na ciwon kai da mura da tari. Su wadannan ba su da lasisi, kuma ba sa rubuta magani sai dai idan an kawo musu takardar likita su duba maganin su bayar idan suna da shi. Yawanci ma a ido mutum zai iya bambance kyamis din da yake da kwararre wato Pharmacist da wanda ba na kwararre ba, wadanda ake kira ‘Patent Medicine Store’ domin na kwararre ya fi na wanda ba kwararre ba tsari da shiryuwa.

shop0036

Kyamis

To a shi inda ake da kwararren ma’aikaci mutum zai iya zuwa ya fadi matsalolinsa shi kwararren ya ba shi shawarwari har ma da wasu magunguna idan ta kama, amma ba zai yi jinya ba, wato ba zai yi allura ko karin ruwa ko tiyata ko kwantarwa ba, tunda ba huruminsa ba ne. Idan aka ga ana yin jinya a kyamis to a san kuskure ne babba wanda idan aka kama wurin za a iya kulle mai shi a kuma ci tararsa. Ka ga kenan ba za a iya zuwa kyamis a mayar da shi kamar asibiti ba. Domin sam ba a tsarinsu daya ba.

Hukumomin Lafiya na Kasa kamar na PHCDA sun zayyana abinda wurin jinya ya kamata a ce yana da shi, komai qanqantarsa wanda ya hada da wurin sayar da magani (kuma ya kasance akwai magungunan, ba wai hoto ba), da kwararren mai-magani zai zauna a ciki, da likita ko makamancinsa kamar Mallamin Lafiya na CHEW da ma’aikacin jinya wato nurse, sai ungozoma wato midwife, sai dakunan duba maras lafiya, da dakunan jinya (ba dole sai na kwanciya ba) da isasshen ruwa da wuta da bayan gida da dakunan gasa kayan aiki da tsabtacesu da wurin kona shara da katon allon mai sunan wurin da alama da sauransu. Wato kenan duk wurin da ka ga mutum daya ya hada wadannan aiyuka duka shi kadai yana aiki (shine masanin magani, shine likita, shine mai jinya, a wasu lokuta ma don ganganci har tiyata suke) to a gujeshi domin barna da nakasa mutane kawai za a yi, ba sama musu lafiya ba. A inda ma aka samar da wadannan ma’aikata dole sai an yi taka-tsantsan an tantance wane ne kwararre wane ne mabarnaci.